Saturday, 27 January 2018

BANA KAUNAR KA Page 10 to 14

==BANA KAUNAR KA 10==
.
Ranar litinin al,amin ya dawo bayan ya huta sai kiran mahida yace mahida ina wahida? wallahi ai tun ran daka tafi ta bar gidan....saboda me? dan ya furuq yai mata duka shine ta tafi abba yace inje in taho da ita amma tace in munga ta dawo gidannan to dan uwanta ya dawo al,amin ya mike dakin faruq ya shiga ya finciko shi wai kai wanne irin mugune azzalumi me wahida taimaka faruq yaja shaka yace yi hakuri big brother ba zan kuma ba so nake ka fada min abin da tai maka da har ka raba tada gida faruq ya fada masa duk yadda akayi tsaki yayi ya juya ya fita bai zame ko ina ba sai gidan atu ina sharar tsakar gida yai sallama nai ciki datsin tsiyar na rungume shi ya dago ni ya dunguran goshi me ya rabo ki da gida nai raurau yaya in baka nan ab tsaneni kullum cikin duk ni kuma na baro musu gidan yace min fa rashin kunya kike masa ni ba rashin kunya nai masa ba wai dan nace ba zan cewa mahida anti ba to shikenan ki shirya mu tafi ya wuce dakin atu.muna zuwa gida da gudu na fada jikin mom ina murna mom ta ture ni ni daga ni kai mom baki gane ni ba autar ki ce fa wahida me nai miki mom?
.
  kin fi kowa sani to yi hakuri mom na daina mahida ta fito tana hararata kai anti mahida me nai miki ta dungure ni ni ce ai zan ce miki anty ta kamo hannuna taso muje dakinmu na bita gaba daya dakin ta zagaye shi da manyan hotunan haidar da bom boy wani muduka sai wanda tasa aka hada mu nida bomboy ina sanye da wani material me tsananin kyau domin hoton ya dauku domin nayi kyau ainun mun dauki hotanne lokacin da mukai partin candy dinmu shima yayi kyau dama tare muka dauka amma lokacin bai nuna manufarsa a kaima ba yadda mu kai hoton in kin gani sai ki rantse muna son juna don gannin yadda na shisshige masa munyi kyau sosai ni kaina ina son hoton na kalle ta sai naga tana faman dariya na karaso yana da manyan idanu masu tsananin kyau da idanunsa ban tsoro domin in ya zare min ido sai nayi fitsari amma a yanxu suna birge ni inason kalar idanunsa masu zubin ruwan gol sam bana iya hada ido dashi domin wani shokin yake sakar min idanunsana hargitsa min lissafi sannan suna tsuma min zuciya toko shine so?
.
kai ni na so ba son sa nake yi ba kauna ce ta yan uwantaka sannan yadda wannan dogon sajan dake kara fito da samartaka dogo ne shi domin bashi da kiba sai dai yana da faffafan kirji sannan yana da kirar karfafa jaruman maza fuskar nan kulum dauke da annuri kamala,kwarjini duk fa yadda naso fasalta muku bom boy ya wuce haka sai dai ince duk inda namiji ya kai da kyau iya diresin bom boy ya kai har ya wuce.
mahida kin san abin da yake hada ni dake kuwa? a,a kin gan ki wallahi za,ayi muguwar kazama saboda me kika ce haka? a farko kin ga dakin nan ina tunanin tunda na bar gidannan baki taba daukar tsinstiya da sunan zaki share dakin nan ba ko kin share? to ai bai yi dauda ba da kyau kinga kan kayan kallonnan kalli yadda sukai mugun kura mahida kalli zanin gado kalli tunin kayan dauda ke dai sai dai ki fidda goma ki tsoma biyar Allah kar ki ce na rana ki kece me son auro muddin kika ce kazanta zakiyi wallahi kinyi asara soyayyar kanta bata yiwuwa sai da tsafta ko ba komai da tsafta tafi inganci tsafta cikon addini ke kenan daga kallo sai karatun soyayya Allah ya kyauta nai shigewata (toilet) ina shiga na fito saboda wani zarni (toilet) keyi nace mahida kin banu toilet din ma ba kya wanke wa??.zagewa nai na wanke toilet din nasa turare sannan na hada kayan wanki na bayar na cire zanin gadon na sa wani na share na goggoge ko ina nasa wa dakin turaran wuta ina sallah haidar yai sallama ita kuma tana kwalliya bayan na idar na gaishe shi na fice a zuciyata nace da haka zai zo ya samu dakin kamar bola? ina kwance a falo bom boy ya fito daga dakin yaya al'amin ya karaso ya tsugunna gabana wani kallo nai masa tare da nace lafiya dai ko?
.
yace lafiyar ce ta kawo haka please ki taimaka min in taimaka maka da me? so? ya furta nace so menene kuma so? kina son sanin menene so? look at me na mike domin na san ba zan iya abin daya sani ba caraf ya kamo hannuna a fusace na juyo tare da tofa masa yau ina daga idona muuka hada ido daya al,amin gabana yai wani mumunan faduwa shi kenan ta faru ta kare an yiwa me zani daya sata wata irin harara ya wullo min ai da gudu nai dakin mom na fada jikinta mom ki yiwa bom boy magana nace bana sonsa bana kaunarsa! meye zai dinga takura min?,yakike so in yi masa wahida? so kike in tare shi ince kar ya kara kula ki?
.
  in kin yi tunani koba komai shahid ai dan uwankine da mahaifiyarsa da ubanki cikin su daya haba auta kiyi hakuri ki sassauta wannan bawan Allah ni wallahi nafi miki sha'awar shahid ko kina da wanda ya fishi,
.
==BANA KAUNAR KA 11==
.
Gaskiya mom ku hana shi zuwa gidannan in ba haka ba sai in bar masa gidan in koma katsina mom inaji ana cewa soja akwai zuciya shi kuwa wannan ba shi da zuciya mom tace ai so daban zuciya daban kuma wallahi na amince da son da shahid ke miki na mike na fita don bana son zancan daki na koma dakin bbu kowa da alama sun tafi yi musu rakiya na kwanta sai ka na mike na shiga toilet nai wanka gidansu wata yar class dinmu tun muna primary ina kallo yaya alamin ya shigo fuskarsa bbu walwala yace wahida duk irin rashin kunya da cin mutuncin da ake cewa kina wa bom boy ban taba yadda zaki aikata ba sai yau ashe baki da kunya a gabana kika tofa shahid yau na zumburo baki nace to yaya ai shi ne bashi da gaskiya dan me zai dinga rike min hannu ni kuma na dau alwashin muddin zai taba ni sai na tofa masa yau amma komai ya mike keki kaja tunda kin san yana sonki wahida ya kamata ki sassauta wa shahid ki dinga fada masa kalamai masu kwantar da hankali ko ba kya sonsa bai kamata ki dinga yi masa abin da kike masa ba yaunzu ki taso muje ki bashi hakuri tabdijan gaskiya ba san iya ba ni dai na fada miki kai don Allah yaya kana gani na ci kwalliyata gidansu da yar ajinmu zani yai tsaki ni dai nace ki jira ni in shirya ya fice nai zaune ina mamakin yaya al'amin naga alama so yake inji kunya yanzu ba kunya sai inje in bawa ya shahid hakuri hum'um ai ba zata zabu ba ina nan zaune ya shigo yayi kyau sosai ya rankwafo ta mudubi na kalle shi yaya kana kama fa da bomboy ainun wahida bom boy bai fini kyau ba no haske kawai ya fika amma kamarku har ta baci na dauko hijabina muka shiga dakin mom,
.
ina gyara dakin anti antin tai sallama nace sannu da zuwa anty yauwa wahida sannu da aiki small ya shigo anti tace lafiya na ganka kamar mara lafiya? ya shafa cikinsa yunwa muke ji tun daxun muke jiranki bafa abin da muka ci sai take away ao sorry my son bari inyi sallah in shiga kicin bayan kowa yayi sallah anty na zaune dukkanin su sun hallara a falo sai na shiga jera abinci kowa na kallona sai dana zauna anti na soma zubawa sannan mu kuma na shimfida dadduma domin nafi son cin abinci a kasa gaba dayanmu na hada mana bomboy yai tsuru domin yasan wahida ta san baya son tuwo shine kuma tai tuwo amma kuma zai bata mamaki,
.
Allah sarki bai gama tunani ba yaga ta janyo kula da filet ta soma hada masa nasa na musamman tuni su al'amin suka ce ba,a isa ba sai dai suci tare kasancewar da yawa sai na hada yadda zai isa ai kuwa suna ci suna santi gaba daya sai da suka share abincin nan suka koma kan tuwo nan suka dinga santin tuwan bom boy na gefe small yace Allah bom boy cikaji tuwan yafi dadi loma daya yayi ya kada kunne gaskiya yai dadi amma na koshi sosai,bayan sun gama an sha lemu ba kwashe kayan sannan na gyara gurin,ya amin yace ki zo mu tafi dare nayi anty tace ka barta tai min kwana biyu yace shi kenan,har gun mota na kara shi ya kalle ni yace yanzu sister sai yaushe kenan? sai randa anti tace in dawo zan dawo to duk randa zaki dawo ki yo min waya,Allah wahida nafi sonki kusa dani sam bana son ki min nisa nai murmushi yayana kenan,ni kaina nafi son zama cikin yan uwana to amma yaya zan yi? ya tada motar na daga masa hannu har ya fice ina tsaye tabbas ina bana son rabuwa da yaya dan dai ba yadda zanyi ne.
.
Da safe da wuri na shiga kicin na hada breakfast anty ta shigo oh wahida break fast din ma bazaki kwanta ki huta ba anti ina kwana lafiya lau wahida ya gajiyar jiya ba gajiya , daki na koma nai wanka sannan na fito cikin doguwar riga gaba daya suna falo na tsunguna na gaida dad dinsu ya shafa kaina yace ina mahida nace tana gida dad dinsu bomboy yana da kirji ga wasa da dariya mutum ne mai kirki sam bashi da wulakanci.bom boy ne zaune yasa hoton wahida gaba yana ta faman sambatu yace wahida me nai miki me yasa ba kya sona? me nake dashi wanda ba kya so ko sana'a tace ba kya so? billahillazi in ba kya so na ni kuma zan iya bari,me yasa ba kya sona wahida me nai miki ki tuna fa ni dan uwanki ne ya kamata ki sassauta min ki tausaya min ya daga hoton wahida kin yadda kina sona? za ki kasance me farantamin? zaki zamo uwar yayana daure ki ban amsa haba yar uwata abar alfaharina haidar ganin dan uwansa na shirin zautuwa akan mace yace haba my big brother ne yasa kake wahalar da kanka akan mace?
.
kai rufe min baki ko dan kaga ka samu taka shine kake min bakin ciki akan tawa? haba bom boy in ban da zarewa sai kasa hoto gaba kai ta sambatu ni wallahi dana dauka kai da wahidar ne sai dana shigo naga ashe hoto ne kai small tashi bani guri don na gane so kake ka raba mu to kayi kadan domin kaunarta nake small ya kwashe da dariya sannu mai sahiba,
.
==== BANA KAUNAR KA 12====
.
wahida in ce dai ta san kana yi? bari kaji in da ake soyayyar gaskiya ya dauko waya hadda sa handfree hello my dear kina lafiya? lafiya amma ba lau ba what? me ke damunki? ciwon rashin ganinka ina sister ta saku? wani zancan sister ki tana nan lafiya to ka gaisar min da ita kafin nazo okey zata ji yanzu me kike yi? tunaninka da son ganinka okey zan zo anjima me kake so in tanadar maka? nafi so ki akan komai na gode Allah ya kara mana son juna amin my sweety i love you so much gaba daya suka sumbaci wayar small ya kalli shahid ka gani kuma kaji da kunnanka shahid yace tsaya kaji nima ai tana sona tsabar ajine amma bari kaji ya kira wahida cikin sassanyar muryarta tace salamu alaikum amin wa'alaikaikumus-salam kana lafiya?
.
yai murmushi farin ciki ni kaina saida naji sautin murmushin me kike yine? ina kwance ko wani abu zan maka? a,a kawai dai ina son jin ya kike ne? to na gode my brother a,a ban yadda ba to my shahed tabbas yaji dadin yadda ta furta a tunaninsa tunda aka rada masa sunan bai taba jin wanda ya fadu sunan yai masa dadi ba sai wahida yai murmushi yace ban yadda ba to my bom ke! ke! ke! please i am sorry my lovely tank u very much tsalle ya dinga yi yana adungure small ya rike baki anya ba allurar shahid bace ta motsa?
.
small yace anya brother ko dai allurar ce ta motsa dariya kawai yayi,da rana bayan an gama girki ina kwance dakin da aka ware min ina wasa da waya wato game wayar tai kara hello sister ya kike? yadda kike mon,abba sahibina suna nan lafiya? nace baki tambaye naki shahibin bane? ai yanzu muka gama gaisawa sannunku uwayen soyayya,kefe ke ni soyayya bata gabana karatu nasa a gaba to anry wahida daga karatu sai me-ke ki daina ce min anty to me zan ce miki?
.
usaina wayyo kin cuce ni ki ce min autar mom da abba da ya al'amin kin san ko yanxu mom ta haihu kin tashi daga auta? me zai sa mom ta haihu ai daga kaina aka rufe fayil din'..to autar bom boy ai kuwa bom boy na gaishe ki ince dai yanzu kuna son juna haba dai mahida kina wasa dani wato kin mantani kenan kin sanni in nace in so to fa ina so in kuma bana so bana so na fada miki yanzu bani da lokacin soyayya karatu ne a gabana.....to uwar biro da takarda ya ishe ni ke kuma uwar soyayya fadi ki kara wallahi sai Aliyu haidar, da ya yamma ina kwance ya amin yayo waya salamu alaikum ya Al'amin ka tashi lafiya? lafiya my sister yaushe zaki dawo?
.
kai yaushe zaka zo in ganka? in kinga shahid ai kamar kin ganni tunda kin ce muna kama koya kika ce?a'ah kai daban shi daban wai yaya su small sun girme ku? ke kin yadda? na dan yadda kadan amma to shi kenan ki tambaye shi kwana nawa ya bamu to ya ka gaisarmin da mom me zai hana ki buga ki gaishe ta? wayar tawa ce bbu kudi a ciki okey ki jira zan turo miki,godiya mara iyaka.minti ashirin ba'a yi ba naji karar text message ina budewa kuwa na shigar da lambobin #3000 ya sako min naji dadi sosai hello "na"am auta ya kike? "normal mom" auta ya gida yasu small? "suna lafiya mom ina nan zan zo "to sai kin zo mu kai sallama.
.
SHAHID tsungune gaban anti,tace wai ina za a tura ku shahid?"anti addu'a kawai zakiyi min domin tafiyar tanada........kai k sanar da su baka da lafiya ba zaka ba shahid bana son rasa ka bana son aikin sojannan anti ni dai addu'ar nake muradi shi kenan ki sanar da Dad dinku dadditunkan lokacin na sanar dashi okey Allah ya taimaka, amin mom ta dauko wani littafin addu'o'i ta dauko ta mika masa ya amsa yasa aljihu sannan ya mika mata hannunsa ta sumbace shi,yaso ganin wahida sai dai bata nan domin ta tafi gidansu lokacin haka ya tafi amma ba don yaso ba yaso ganinta suyi sallama! bayan sati biyu muna zaune a falo "hello mom wahida kin wuni lafiya?
.
lafiya lau mom kice mahida ta kawo min kayan ke me zai hana ki fada mata mom kin santa raina ni ina fada mata cewa zatayi ba zata kawo min ba leda ita waye ya raina wani? mom ita ta fara raini nike da ita wacece babba? mom ita ta girme ni da kadan amma ashe dai ta girme ki zan sa ta kawo miki insha Allah to mom na gode sai anjima.
.
yaya faruq hello yayana ina jinki yace ince dai lafiya oh yaya kaga abin da yake hadani da kai ba ko ka tambayi lafiyata kace ya nake bana son jin yadda kai ken mun kai dai wallahi baka da sakin fuska kai dai me ganin fara'arka daga mahida sai sahibarka anty mamy,to ya ranki?.fari sol tunda ina da wanda zai min inji sanyi da ace bani da shi sai inyi kuka da samunka a matsayin yayana ke wahida Allah in na fito sai na zane ki Allah sarki duka don Allah in zaka fito ka taho da tabarya ko bindiga,na kashe wayar ina dariya a can gida kuwa,a fusace faruq ya fito hannunsa rike da belt kai tsaya yai dakinsu wahida mahida kwance ta takarkare tana waya yana shiga ya soma laftarta wayyo me nai maka ina wahida me za kai mata billahillazi in baki nuna min ita ba sai na zane ki mahida ta dinga dariya tace, wallahi wahida bata nan domin tana gidan anty yanzy fa ta yo min waya ta kare min rashin kunya dakin mom ya shiga mom ina wahida?
.
==BANA KAUNAR KA 13==
.
wahida kwananka biyu da tafiya itama ta tafi gidan sister khadija ya juya yana gunguni dakinsa ya koma ya dauko waya bugu daya ta dauka hello kin san Allah in nazo gidannan sai na lahira ya fiki jin dadi banzamara kunya,Allah ya faruq kasan fa masoyina soja ne ni nasan in kazo gidannan ka taba ni sai ya harbe ka in kuma ka musa to kazo ni kuma zan masa waya ince ga wani yazo zai taba lafiyata kasan yana sona zai iya komai a kaina oho dai dadin abin ba sonsa kike ba la! da ka sani yanxu muna tsananin son juna na kashe wayar ina dariya.faruq ya cika da mamaki dama wahida na son shahid in kuwa haka ne gaskiya bom boy yayi dacan big girl kuma beautiful gentel girl dakin Al'amin ya shiga yake fada masa Al'amin yace kana mamakine? haba dole in yi mamaki ko dan ganin irin tsantsar kiyayyar da wahida ke nunawa shahid wallahi ka bar mamaki domin ka san bom boy dan soyayga ne tabbas zai iya lankwasa wahida san ransa.
.
ina zaune ina karanta wani littafi da ya shahid ya siyo min mahida day amin da ya faruq wayyo dadi ihu na sak na kankame mahida cike da tsatsan farin ciki kicin na shiga na hado musu abin motsa baki sannan na zauna ya Al'amin ina wuni sister ya gida? lafiya lau na lalli ya faruq koda ba gaishe shi kallon arziki bai min ba,anty ta fito tace a'ah lalle yau ina da manyan baki wahida me kika bawa ya"yan nawa? nai murmushi su ya amin suka gaishe ta na kalli mahida mahida ince ko kin taho min da kayana? ai zuwa muka yi mu tafi dake lalle ma keni ba yanzu ba Allah ko sai yaushe? na mike na koma kusa da ya faruq nace ke ni bar ni mu gaisa da yayana,na dafa cinyoyinsa ina tsungune kan gwiyoyiwa nace yaya faruq don Allah kayi hakuri wai ma me nai maka? na kwantar da kaina kan cinyarsa please ya faruq im sorry baki fada kunya Allah in baki bani guri ba zan yo boll dake,stupid girl,mahida ta taso kai don Aah yaya kar kasa ta kuka,ina laifi data baka hakuri,to ban hakura ba wato ke me yar uwa to kamo ni taso kinji anty wahida dadin ta ma ba Abba bane nice ke ma ba zan wani bashi hakuri ba muka koma kusa da yaya Al'amin muka ci gaba da hirar mu
.Muna nan zaune bom boy yai sallama a,a kace muna da manyan baki hadda mahida a gidan? mahida tace Allah yata muna zuwa kaine dai ba a samu ka ga yanxu ma tun dazu muka zo ba don Allah yayi zamu gana ba har sai mu tafi ba ka nan,ni sister ma ce min tayi kwata kwata baka kasar tabbas jiya cikin dare muka iso ku bani ten minuti in yi wanka sai daya soma duba anty sannan ya shiga dakinsa nace yauwa ya amin ga bom boy muna so ju fada mana cikinku waye babba? mahida tai caraf la! baki sani ba ai tsiransu kwana biyu shi yasa ma aka hada sunansu akayi rana daya ke ni dai ban yadda ba duk.
.
bom boy ne yai sallama idona har cikin nasa yai min kyau yana sanye da fakistan ruwan madara karasowa yayi kusa dani cikin rada yace gimbiya me zan samu rabona da abinci har na manta na mike na shiga kicin dama tuni nai masa tanadi na musamman gaba daya na hado musu dasu ya amin can lambu na koma i na zaune ya amin ya shigo ya zauna ya kalleni yace ince dai yanzu soyayar tayi karfi murmushi nai kawai domin nasan babu wata soyayya.bayan isha'i suka tafi mahida taso kwana nina hana ta domin inta kwana bbu mai taimakawa mom wajen shirya abinci duk illahirin yan aikin gidanmu sam mom bata bari suyi mata girki ita take yi duk da kullum sai an fita da abinci masallaci komin yawansa ni zan taya ta ko kuma niyi ni daya sam koka dan mahida bata son aiki aikinta kwanciya game,kallo,karatun littafi,Allah ya sani sam bana son halin mahida domin ya mace ko ba komai aure za ai mata san a rayuwTa bbu abin dana tsana irin kazanta muddin ina gida in kin ganni zaune da dalili shi yasa duk irin fadan da muke da ya faruq ko kadan baya so ya budi ido yaga bana gidan domin in ina nan dakunansu kullum ne saina gyara musu nice wanke musu toilet gyaran gado hatta yan aikinmu su kanyi missing dina.
ina zaune dakina small ya shigo wahida bom boy na kira na kalle shi nace yana in ne? yana dakinsa na mike nasa hijabina na fita nai sallama yana kwance ya kalle ni cikin lumshe ido wahida nai masa shiru donni tsoro ya bani ma tunani ko wani abin yasha domin idanunsa sunyi jajir WAHEEDAH ya kara furtawa na'am na ce cikin sauri wahida bani da lafiya me yake damunka kece wahida kece ya kamo hannuna,hannunsa zafi kamar garwashi ba tausaya masa ainun amma don kar in kyale ya samu damar sai na fisge hannuna na ce bana son iskan.kafin na karasa ya fizgo ni ya rungume ni waye dan iskan? gabana ya shiga faduwa, ma don kar in nuna naji tsoro ya samu wata sabuwar damar sai na dake nace kaine dan.
.
yasa hannu ya doke bakina ya murde min lips ina wayyoahna! kafa yasa yayo ball dani sai gani a kofar daki da gudu na fita nayi sa'a falon ba kowa daki na shiga na kulle nai kuka mai isata.
maheedah zaune tana game Al'amin ya siga dakin mahida ya kira sunanta ba tare data bar abin da take ba tace na"am kanna dawo ki shiga dakina ki gyara min kin ga yayi kura sosai to sai ka dawo nai taci gaba da harkar gabana.
==BANA KAUNAR KA 14==
.
sai kusan magariba ta tuna tai saurin shiga dakin ta burbura sharar minti biyar tana fitowa ya amin ya shigo kai tsaye yai dakinsa ai bai karasa shiga ba ya kwala mata kira mahida da sauri tazo me na saki?.Yaya ai na share maka ya kalli dakin cike da takaici ko tsarar da tai bata kwashe va a kofar dakin ta barta sannan dakin buzu buzu faruq yace ayya kadan daga cikin aikin mahida,Al'amin ai tayi maka mai kyau ni dana sata gaba daya karkashi gado ta tura min sharar ka ganta nan bbu abin da ta iya sai kallo sai soyayya Al'amin ya hau salati da kin san baki iya ba kice min to kanwar kanwarki ta fiki iya abin duniya,mahida kuka ta saka ai kun san tuni ya ba kuka sani al'amin dan haushin bai karasa magana ba lallai ya shiga tattare sharar.
.
kwalliya nayi sosai na shirya cikkin wani ratsatten less,leshin ya amshe ni nayi kyau ainun na rataya jakata na sa karamin hijabi dakin dubai anty na tafi to wahida ki gaida mom amma fa kar ki kwana to anty a wacce mota zanje? ta mike ta dauko min mullin nace la! anty motar yaya shahid umh ni dai tsoro nake kin san motarsa da sunansa kar inje aka mani,antu tai ta dariya bbu me kama ki kallo daya za,ai miki a san ke kanwarsa ce,bbu me kamaki na juya na salube kai gaskiya notar akwai kyau, mota ce wadda ta amsa sunanta rantsattsiya kirar zamani gaban motar kawai zaki kalla kinsan waye me motar da manyan baki aka rubuta BOM BOY sai dana gama karewa motar kallo sannan na bude na shiga wayyo sanyi da kanshin me motar yaso rudata na shiga lumshe ido kwance nai cikin luntsumemiyar kujerar motar jina soma gyangyadi nai kirgil hoton me motar dake jiyawa gaban motar na zubawa ido yana murmushi yayi kyau ainun hannu nasa na shafi a fuskarsa tare da fadin i love you so much yayana,wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu,ashe duk abinnan da nakeyi bom boy na bayan motar yana kallona,ohi sam ban sani ba koda na hau titi nayi mamakin irin yadda mutane da dama suka dinga daga min hannu kasancewar glass din motar mai duhu ne bbu wanda ya ganni gaskiya kan naje gida na kara tabbatarwa shahid mutumin kirki ne mai jama'a.
.
ina fitowa mai gadi yace sannu da zuwa yauwa baba tsoho ya gida? lafiya lau ina shiga sister ta fito da gudu muka rungume juna dakin Abba muka karasa abba sannu,yauwa sister wahida abba ina kwana? lafiya lau wahida,ya kika baro yar uwar tawa tana nan lafita ta mace in gaishe ku muna amsawa da sauri na mike da gudu nai dakin yaya faruq hello yayana na fada jikinsa ya dago fuskata sister amma kin dawo kenan? la! anty wata in dawo anya anty ba zata bar man keba,umh ai nafi son can saboda me? can sunfi sona basa dukuna da sauri na fita hello ya amin hello ya amin dina na dawo na rungume yayana yace yaushe kika zo sister yanzu nazo amma kin zo kenan munyi kewarki,Gaskiyaba zaki koma ba yaya naga dakin ka duk ya canza shima ai yayi missing dinki bebinmu maza huta ki gyara mana dakinmu dakin abban kuma mun sha hira da abba sai da abba ya fiti na shiga dakin yaya faruq na wanko masa toilet sannan na ciro zanin gadon na shimfida masa wani lallausan bargo na goggoge na share na kunna turaran wuta dakin yaya amin shima ba gyara fes na janyo dakin na kulle dakinmu na koma ba zan iya fasalta muku irin yadda dakin ya koma bana dai gyara shina hada kayan wanki na bayar saida na kammala girki dare na gyara kicin din sannan na koma dakin nai wanka har lokacin su yaya basu dawo ba nai wasu mom sallama na tafi.
.
faruq na dawowa dakinsa ya tura haba sanyin a.c da kamshin turaran wuta dan maiduguri ya buga shi kujera ya zaina tare da fadin thank you sister ya zare kayan jikinsa ya shigo toilet shima sai kamshi yake gaskita faruq yaji dadi sosai haka zalika al'amin ya gode wa wahida.
iba zuwa gida ya shahid zaune a falo nai salama ya amsa min ciki ciji dakin anty na wuce nai sallama tana zaune ta amsa da fara'arta zama nai kusa da ita tace sannu da zuwa nace anty ya gida lafiya lau ya kika baro su mahida suna nan lafiya lafiyansu klau dakina na shiga wayata ta shiga ringing ya faruq sunansa ya bayyana akan screen din wayar cikin sanyin murya na amsa "hello wai a tunanina laifi nai masa me yasa kika ki bari mu dawo mu kawo ki gida? umh gani nai yamma tayi,okey naga dakina yai fes na gode fa dariya kawao nai.
.
Wahegari na tashi da matsanaicin ciwon kai da kyar na iya fitowa dakin anty naje na gaishe ta sannan dakin daddy sannan dakin small kamar in shiga dakin shahid wata zuciyar tace kawai in share shi daki na koma na cire hijabina sanye nake da wata yar bingilar shimi shara-shara domin kawai na kirjina a bayyane yake kasancewar bbu mai shigo min daki kwanciya nai anty ta shigo min da break fast din da magani ina zaune ina shan tea sun hadu gurin breakfast bom boy yace anty ina yar takine bata jin dadi ya mike me ke damunta bai maji amsar da antin ta bashi ba domin sam hankalinsa baya jikinsa ina zaune ina shan tea yai sallama zama ya yi a gabana ya zuba min ido.

0 comments:

Post a Comment