Saturday, 27 January 2018

BANA KAUNARKA Page 15 to 18

==BANA KAUNAR KA 15
.
oho ni na manta ya shahid ina kwance jin shiru nace au good morning domin in ance masa ina kwana ya kan ce mene kuma ina kwana? ikon Allah ganin yadda ya shagalta da sauri na kalli kaina wa iyazubillahi gaba yai mumunan faduwa shi kenan ya gama kalloba inalillahi nai waurin janyo hijabina na rufe jikina nakalle shi cikin bacin rai nace wallahi ka kalli haram ban yafe maka.
.
yasa hannu ya doke min baki uban wa yace ki zauna a haka to wa ya ce ka shigo min dakina na fada cikin kuka ya mike ya fice nasa kafa nai boll da tea din na shiga birgima shi kenan ya gama kallon abin da zai kalla ni ya cuce ni ya cuci masoyina mahida ta fado dakin ke kuma me kike wa kuka na shiga bata labari na ciro hijabina kin ga fa rigar toke me yasa ba kya son sa bireziyya.Allah ya kiyaye ni bana son biriziyya to ai gashi nan ya kalli bati ai kuwa har Allah ya isa nai masa oho ke zata bi. bom boy ya shigo shi da small boy na mike na bar musu falon domin ni haushinsa nake ji sai bayan la'asar mahida ta tafi na zauna ina kallo dakin anty yai sallama yayi shiri na kalli agogo lokacin fitarsa yaya sai kuma gobe da safe na mike na fice ya kalli anty,anty zan tafi sai da safe anty ta janyo wani galan ta dauko glass cup ta cika masa shi da rubutu ya amsa yai bismillah ya shanye tace ka shirya kaje katsina malam baba yana son ganinka to anty yaushe zani kin san fa bani da lokaci ka daure dai kaje ko wuni kayi to anti kaci abinci ya shafa cikinsa rabonsa da abinci tun karin safe ya kalli anti yaga tana kallonsa yace yanzu nasa wahida ta kawo min okey miko min zam zam din can ya mike ya dauko ta juyo a cup tai masa tofi a ciki ta bashi ya sha tai masa nasiha irin tasu ta manya daga nan yai mata sallma har ya fita ya dawo anty ina small, small ya tafi katsin can zai kwana me yasa bai fada min ba kayi hakuri ya fada min in sanar maka mantawa nayi okey Allah ya dawo dashi lafiya amin dakin wahida ya shiga tana zaune tana zuba abinci ya zauna ta mike ta bar masa abincin yai murmushi tare da riko hannunta dan girman Allah ki zauna billahillazi rabona da abinci tun karin safe please help me ta koma tare da cigaba da zuba mana tare muka ci yana min hirar irin nasarar da suka samu a tafiyar da suka yi,muna gamawa ya min sallama ya tafi na mike nai alwala nai sallah sannan na kwanta.bakin dare misalin karfe biyu na shiga toilet na fito ne ina shirin kwanciya sai naji kamar ana dirowa dif!! dif!! dif!! tuni kafafuna suka soma karkarwa jikina ya dauki rawa karar bindiga ita ta dawo dani hayyacina tuni na shiga laluban wayata na shiga danne danne har n nemo ya shahid layinsa na celtel a kulle tumi na tafi glo cikin sa,a ya shiga,hello yaya kana ina? gida a rude nake sosai nutsu ki fada min me ya faru?
.
yaya ka fito barayi sun shigo mana gida barayi wahida to gani nan zuwa har ya kashe y bigo,wahida ki kulle dakinki ki zare key din kar ki fito har sai na dawo cikin kuka na ce to kayo sauri yaya daina kuka yanzu zan dawo shiru ba yaya haba tuni na fita da gudu nai dakin ya shahid na dinga dukan kofar ina kiran sunansa na koma dakin small nan ma a kulle wayyo nai dakin anty anan na gansu dukkaninsu sun wani nannade kansu da fuskarsu nan da nan nayo kansu ina dukansu ina ihu wani daga ciki ya daka min tsawa ke ina zaki? ban sani ba shegu tsinannu,la"anannu ogansu ya haska ni da toch light sanye nake da rigar bacci iya gwiwa wata mahaukaciyar dariya ya saka yace cool down beb ya kalle su ku karasa bari mu daidaita da baby yes sir,cak ya dauke ni na shiga dukansa har da cizonsa ina zaginsa amma bai dire ni ko ina ba sai bedroom dina runi ya raba ni da rigar jikina da gani sai pant ya shiga murzata san ransa,inallilahi wa inna ilaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibatin wa aklifi khairin minha,la haula wala kuwata illa billahi aliyul azim,wala haula wala kuwata illah billah aliyul azim,wala haula wala kuwwata illah billahi...sai kawai ya....to me kake /kike tunani iyeh!! iyayen gulma toh baza kuji ba.bom boy sadaf! sadaf! ya shigo saboda haka bbu wanda ya ganshi kai tsaye dakin wahida ya shiga ganin dakin a bude ya razana shi yana danna kai ya soma jin ihun wahidar ogan yana rike da ita gaba daya ya gama fita a hayyacinsa bbu abin da yafi buri irin ya cimma burinsa,ta baya bom boy ya anyo ransa ya gama baci hankalinsa a tashe gaba daya ya birkice shi kuwa oga tuni ya mance da abin da ya kawo shi wuka bom boy ya soka masa a kirji ina kuka na mike da gudu na kankame shi ya daga aina muka gama ido ban taba ganin shahid cikin irin wannan yanayin ba cikin kakkausar murya yace bai taba kiba ko?
.
cikin kuka nace eh maza ki sa kayanki ki kulle dakinki tuni na rike shi ina kuka to saka kayanki in kai ki dakina ki kulle nasa hijabina ya kaini dakinsa na kulle yace kar ki fito kin ji nace to dakin anty ya nufa gaba daya y tasar musu kasancewar yana da wani sirri wanda shi kadai ya sanyar wa kansa sani don haka cikin kankanin lokaci ya dama dasy ya shiga dakin kwance ya ganta cikin jini inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
,
BANA KAUNAR KA 16
.
Dagowar da yayi ido hudu da wasu suna shirin guduwa yai amfani da piston ya harharbe su ta bude idonta da kyar take magana kaje dakin wahida da mahaifinka da sauri ya mike ya nufi dakin mahaifinsa a kulle ya ganshi cikin jini harbi biyu daya a kai daya a kirji kadan ya hana shahid zautuwa sai dai albarkacin kalmar da yake ta maimaitawa yasa nutsuwa tazo masa ga abinda yake cewa,
.
innalillahi wa inna ilaihi rahiun Allahumma a jirni fi musibatin wa aklifli khairan minha Allahumma la sahla illah maja alhu sahla wa anta taj alul hazna iza shi ita sahla.koda naji shiru bbu alamar motsi sai na fito da gudu nai dakin anty na dinga tsallake su ina wucewa caraf wani ya damko min kafa tuni na shiga ihu wayyo shahid kaxo zai balla min kafa wayyo da hanzari ya fito ya duba dakinsa bai ganni ba a dakin anty ya ganni tsawaya doke min ke wacce irin yarinya ce waya ce ki fito ba yi magana ba na ci gaba da kukana ina nan ina kuka naga sojaji sunata shigowa bayan sun gama shigo wa daya daga cikinsu ya kalli shahid cikin harshen turan ci yace ma akai min ina ji yaya na masa bayani kafa yasa ya doki hannun da gudu nai dakin anty bbu wanda suka taba ko?
.
shahid ya daga rinanim idanunsa aya ce sun harbi dady har guri biyu dad dina Allah ya amahi abinsa sannan sun harbi anty a kirji gaba daya suka sa salati amma musulman cikinsu daga nan yai musu jagora dakin mahaifinsa sun kwace shi sun shimfidar dashi a gadonsa tuni likita ya shiga aiki..ina shiga na kankame ta ina kuka hannu ta daga da kyar ta shafa kaina wahida ba dai abin sa sukai miki ko? a daran yaya shahid dani muka kai anty wani babban asibiti kudi basu yi wata-wata ba suka shiga da ita emergency likitoci sunyi nasarar cire mata bulet din ina zaune na hada kaina da gwiwa ya shigo taso mu tafi yace min na mike na bishi muna isa muka tarar su abba mom atu baba rabiu duk sun zo har anyiwa daddyn wanka kukan da nake yine yasa abba yayi min magana tashi ki koma daki ina kallo shahid na kwararawa mahaifinsa addu'a waya naiwa haidar cewa maza ya taho gida bbu lafiya kan kice meye wannan gidan ya cika da mutane tashin hankali, haidar ya iso ya tadda ana shirin fita da mahaifinsa daga dakinsa lokaci daya ya birkice da kyar aka shawo kansa yaiwa mahifin nasu addua,amma sumansa uku koda za,a dauke shi kukan kura yai ya rike makarar ya dinga duka masu rike da ita,
.
shahid shi ya dauki haidar yasa shi a daki ya kulle sannan aka samu damar fita da mahaifin nasa a asibiti kuwa sunce basa bukatar dan jinya sai dai anti da kanta ta roki a bata wahida saboda haka wahida ce a gurinta.bayan sati daya ba laifin jikin antin yana sauki ranar shahid da haidar abba da baba rabiu anty ta soma yi musu magiya hadda kukanta su fada mata gaskiya ina mijinta yana raye ko kuma ya rasu kukanta ya daga hankalinmu ainun,haidar yace anty sai dai hakuri amma maganar gaskiya daddy ya rasu yaune kwanansa bakwai gaskiya ta girgiza domin bbu wanda ya ankara sai ganinta akai wanwar a kasa ta fadi tuni jini ya balle haidar ne ya kira likita,likitoci sukai hanzarin dauke ta wani likita ne ya dinga fada kun gani kun wargaza mana aiki shi yasa muka fada muku bamu....
.
kan ya karasar bom boy ne cikin fushi ya dakatar dashi ya dinga yiwa likitan bala'i da kyar abba ya ja shi suka tafi.tsakad dare ina zaune kan abin sallah tace wahida ban ruwa insha na mike na dauko robar swan na tsiyayo a cup na dago kanta na bata tasha sosai har tace ya ishe ta na maida ita ba kwantar tace sannu wahida nace yauwa wahida Allah yai miki albarka ubangiji Allah ya raba ki da sharrin makiyanki amin,wahida ki taimaka ki bawa dan uwanki ishassun hadin kai shahid yana tsananin sonki anty ba wai bana sonsa bane ina son karatu ne to wahida Allah ya taimaka ameen,ta koma ta kwata ina jin ta tana ta jero kalmar shahada koda inda saboda yace na saba jin irin wannan saboda koda yaushe sannan duk irin baccin da anty take yi muddin akayi kiran sallah ta kan ce in taimaka mata tayi alwala tai sallah yau ma ina zaune har akayi sallar asuba sai dai nayi mamakin yadda har aka idar anti na bacci komawa nai na kishingida bacci ne ya soma daukata sallamae abbana naji shi da ya shahid.
.
BANA KAUNAR KA 17
.
  ina tunanin daga masallaci suka fito shida shahid ne yai gun anti nai saurin cewa ya shahid kar ka tashe ta ta samu bacci cak ya tsaya ya zuba min kwala kwalan idanunsa masu tsananin kyau na lumshe idanuna ina jin wani sanyi na ratsa min duk ilahirin jikina toko shine so? no! ni nasan ko kadan bana som bom boy kome yasa oho ma muryar shahid din ita ta dawo dani hayyacina yace anty tayi sallah ne? a,a gani nai ta samu bacci shi yasa na kyale ta da sauri ya karasa ya kama hannunta jin sa yai kamar kankara yai saurin yaye bargon da wahida ta rufa mata tare da taba jikinta inalillahi wa inna ilaihi raji'un ya dago a firgice yana karkada hannu yana fadin abba anty bbu,anty bbu ya sulale tare da dafa kai da sauri abba ya karasa mikewa da gudu na karasa ina girgiza anty,anty ki tashi don Allah kar ki tafi ki bar mu anty kuka nake sosai a daidai lokacin likitoci suka shigo tun daga lokacin ban kara sanin meke faruwa ba sakamakon suman da nai.shahid bai taba shiga tashin hankali irin na wannan rana ba,don ma karfin addu'a da taimakon ubangiji ya samu nutsuwa. Bayan sati biyu wahida zaune ta hada uban tagumi wasu irin hawaye ke shatata akan kumatunta ya faruq ya shigo ya zauna wahida ya kira sunan cikin sanyin murya na dago na kalle shi sai dai sam na kaaa tsayar da hawayen,wahida ya kamata kiyi hakuri addu'a zakiyi wa anty,tashi kiyi wanka kinji Allah ya ji kanta "amin" na mike na nufi bedroom dinmu nai wanka na fito cikin atamfa gold star ba wata kwalliya nai ba nasa hijabina dakin mom na shiga nace mom zani gidansu bom boy mom ta kalle ni wahida kin ga kuwa yadda kika rame na rausayar da kai ta ci gaba,din Allah wahida ki kwantar da hankalinki ko kina so kema mu rasa ki? na girgiza kai tace to kar ki dade wai ma me zaki yi a gidansu bom boy din? mom kayana zan kwaso sannan ina son ganin bom boy domin na san..... shigowar ya faruq ce ta katse min maganar na mike kawai na fice, na zauna a motar ina shirin tayar da motar hassan me bawa filawa ruwa ya rugo da gudu yana daga min hannu, hassan dattijo ne domin a kalla zai yi shekera hamsin muna mutunci sosai domin akwai shi da ban dariya yana zuwa ya tsungunna,an gaishe ki sarauniyar kyau na tabbata duk nigeria bbu mai kyanki wahida ta mahida hajiya wahida ta alhaji al'amin family dinku na kaunarku muma muna kaunarku,domin kuna fita hakkinmu ya dan sassauta yana washe baki na harare shi ta kasan mutuwa akai min ba sorry ya hakuri? nace mun gode Allah to Allah ya jikan musulmi Allah yai musu rahama, amin nace sannan na dauko dubu biyar na bashi ya zube yana kwara godiya ya bani tausayi ainun a sallibe naja motar.
.
nai sallama falon kakarmu da haidar suna zaune suka amsa sallamar na zauna ina gaishe su,kakarmu tace yanzu nake cewa zanje duba ki ashe kina tafe na sunkuyar da kai nace shahid na nan kuwa tace eh dakinsa na shiga nai sallama,nai sallama sama da goma da sauri na shiga yana zaune ya hada kai da gwiwa a salube na karasa na tsyngunna nasa hannu na dago fuskarsa wadda ta jike sharaf da hawaye idanun nan sun kada sunyi jajir ya shahid menene ba ka da lafiya ko anti ce?wayyo shahid ka bar yiwa anty kuka cikin kuka na furta kuka nake sosai na rike hannunsa gam yayi shiru wahida bbi abinda yake damuna da sauri muka zubawa juna ido har sai da muka gamsu dan kanmu na hango tsantsar kauna ta cikin kwayar idonsa ganin kallonsa na haifar min da kasala na sunkuyar da kai nace don Allah ka tashi kai wanka nan ma ba musu ya mike ya shiga toilet da hanzari na gyara masa dakin na feshe shi da airfresner sannan na fita. Shahid na fitowa sanyin ac da kamshin airfresner ya sanyaya masa zuciya hannu ya daga Allah ka bani wahida don hasken annabi da alkur'ani ya zauna gaban mirror yana kallon kansa tabbas ya rame rama ba yar kadan ba yai make up shadda yasa marun ya fesa turarensa me tsananin kamshi ya fito cikin kwalliya bakin takalmi yai amfani dashi yana fitowa wahida na mikewa inna ni zan tafi wahida ki kwana mana ayya inna ban ce zan kwana ba sai dai inna sake zuwa to ki gaida mom din.na shiga mota ina shirin tayar da motar ya bude ya shigo na kalle shi yai min kallo muje kawai na tada motar kai tsaye gidan baba rabiu ba nufa dake sabon titi ya kalle ni ina kuma zamu? na kalleshi nace yaya ina son bawa mamy sako ne bana so fa kina ce min yayan nan na kalleshi to me zan ce maka? kice min nawa ko kice min my darling uhum sai dai ince my brother ya harareni kasan sunan da nake tsananin jin dadinsa? ya girgiza kai ina son sa kai kuma baka so muce maka shine bom boy,daidai lokacin nai fakin da gudu mamy ta fito ta rungume ni ta kalli shahid dan uwa ku shigo daga ciki mana bayan mun gaisa da umminta muka wuce dakinta ta shiga hidima damu sai data cika sannan ta zauna shahid ina wuni kun wuni lafiya? ya muka ji da hakuri hakuri mun gode wa Allah Allah yai musu rahama "amin don albarkar annabi(S.A.W) n gaishe ta tace ina kika baro min mahida? tana gida.waya ta ta shiga kuka na dauka hello,naji ance daga can bangaran,salamu alaikum,aim....  wa alaikasalam,wahida "na'am wanene kai? wahida ba ki gane ni ba? amir ne ya hakuri?
.
Alhamdullilahi to Allah ya jikan musulmi amin na gode,amir sai anjima na kashe tare da cilla wayar jaka don ganin yadda bom boy kole watsomin harara da wa kike magana oh yaya kenan na fuskanci tunda na soma magana hankalinka na kaina,to amir ne abokin yaya al'amin ya bugo yai min gaisuwa waya ba shi number ki ina tunanin ko gun ya amin ya amsa okey zamu haduda al'amin din taso mu tafi mamy ta ce oh bom boy ba dai kishi ba tun yanxu daku bari kuyi sallar magariba da sauri ya fice yace ba kya cewa mu kwana naiwa ummi sallama muka fita ya cemin bani key,din motar dan na san da magariba ba kya gani saboda bacci naifar tare da kanne ido nace kamar ka sani domin har na soma jin bacci na bude motar na shiga domin na lura na haifar masa da kasala mamy ta leko gaskiya kun yi min kyau gashi kamarku daya Allah ya barku tare for ever amin yace tare da mika mata bandir din naira dari dari nace keh mamy kin taba ganin yayan da ya yakeso ya auri kanwarsa? bom boy yace za a fara akanmu mun soma tafiya ya kira sunana "wahida" na'am kar in kara jin bomboy a bakin ki na dago muka hada ido na rausayar da kwayar idona nace toh yaya muna zuwa gida na fito muka jera mom muka tarar a falo bom boy ya gaisheta sannan ya wuce dakin ya faruq mom tace auta maza tashi kiyi sallah wash mom na fa gaji ta kalle ni a kafa kuka taho na girgiza kai to maza tashi kiyi sallah na mike da hanzari. mun hadu muna cin dinner da mom ta tanadar mana waya tace ta cika falon da kara na dauka amir ne nai tsaki kai wannan amir da naci yake na kashe wayar na cilla kan kujera ta ganni kowani yake kallo ba kamar bom boy sai na mike ina gunaguni na bar falon,mom ce tai kira nazo auta na jawo na zana waya bata miki idona ya karo ruwa cikin shagwaba kamar zan kuka nace ba wannan amir din bane abokin yaya al'amin ya takura min ni kuma wallahi bana sonsa na shige dakinmu ina shigewa ya shahid ya shigo wahida ta waya bata miki rai,b wannan nataccen amir din bane ya takura min ke me yasa ba kya sonsa na dago na zuba masa ido tare da turo baki na kara shagwabewa kamar zanyi kuka nace na fada muku ni karatu zanyi ba kya sonsa kenan? na daga kai to shikenan dakko min wayar na mike na dauko na bashi a daidai lokacin wayar ta shiga ringing,abba ne yace wahida maza kizo,to abba nai saurin mika wa bom boy wayar na fita.abba gani yace wahida waye yayo miki waya na zauna na kwashe duk yadda akayi na fada masa to ke meyasa ba kya sonsa? nai narai-narai idona ya kawo ruwa nace abba karatu na fada masa ba yanzu zanyi aure ba,abba kinga abinda yake hada ni dake to meye abin kuka to abba bana so yana bugo mi waya to shi kenan kiyi hakuri zan yiwa ya amin din magana ya faruq yace gaskiya abba ku kuke shagwaba wahida shi kenan ita kowa bata so,abba hannu kawai ya daga masa ya mike yana jin haushina ya bar gun abba yai ta lallashina tare dayi min nasiha. bom boy ya latsa lombobin amir wayar ta shiga ringing amir cikin zumudi ya dauka hello,hello my sweety heart don Allah kin amince,Allah ina tsananin sonki wahida taimaka ki bani amsa tun kan gubar sonki ta halakani,wahida ina sonki...............bom boy ya cije lebe yana jin tsananin takaici ransa ya baci hankalinsa ya tashi ya mike kamar wanda aka cakawa allura yai saurin katse amin din stop it!! har ni zaka fadawa maganar banza,wanne kai? in ji amir.cikin tsawa zaka san ko ni waye,amir yanzun nan zan maka bayanin ko ni waye,nine shahid bomboy jikin amir ya dauki karkarwa ya san bom boy kamar yunwar cikinsa bom boy yana da sauki yan da zafi muddin aka taba shi ba wasa tunda sun taba yin sa insa wadda basu jima da shiryawa ba gashi yanxu ya bullowa kansa ya salam tabbas ya san yana son wahida amma fa ba irin son nan ba me zafi domin karfin son sha'awa ce yarinyar komai nata burgeshi yace sannan bbu abin da yafi daukar hankalinsa irin kirjinta me dauke da albarkatu sannan mazaunanta masu birkita masa kwanya abin da yake jan hankalinsa kenan har yake tunanin ko sonta yake to yanzun ma so yake ya lallabata taso shi sannan cikin dabara ya samu ta biya masa bukatarsa in yaso sai ya samfe abinda yake so kenan.amir ya shiga bawa bomboy hakuri ya kwantar da kai amma a zuciyarsa ya dau alwashin sai ya lalata rayuwar wahida.....
...
kana jina amir ka fita daga sabgar janwata,amir na sonka fiye da yadda ka san kanka wallahi har in ji in gani ka san Allah ko magana kar ka kuma shiga tsakaninku in kunneh yaji jiki ya tsira,ya kashe wayar .bom boy yaiwa abba sallama abba yace haba shahid ka kwana mana ai duk gida ne shahid yai murmushi tare da duba agogon hannunsa 1:30pm ya ce Abba ina da wani aiki ne a gabana to shahid Allah ya taimaka,amin abba na gode.washegari da wayar boy na karya hello,nace cikin muryar bacci kin tashi lafiya? . lafiya lau bomboy bana ce miki bana so ba ni kuma nace ina son bom boy yai dariya haba tawa kina so ki dinga cemin yayanmu su tasu suma suce min dariya ta kwace min domin ina tunanin wasa yake min nace ai sai mu hana su yace na yadda amma da shahid in munyi aure zaki dainace min,nai dariya cikin dariyar nace na yadda.ina kwance cinyar mom sai faman shagwaba nake mata mahida na kicin yaya faruq sai hararata yake yi ni kuma na kara shagwabewa mom tace auta kin manta goma daidak al'amin zai iso? da sauri na mike na fada dakin yaya tunanina gyara masa dakin ko ina kamshi ke tashi gaskiya ina son yayana al'amin. ina kwance a dakinmu naji yana my sister da gudu na fito na fada jikinsa yaya nayi missing dinka ainun yaya don Allah karka kara tafiya ka dade ba zan kara dadewa ba in ce sai kin gyara min dakina na girgiza kai yace kin soma nai dariya yace kin girma da yawa la,ni din don bakaga mahida bane.na hada breakfast na kai masa lokacin yana wanka don haka na ajiye masa na koma dakinmu ina me farin cikin ganin ya amin mai sona dawowar ya amin ba dan karamin dadi tai min ba domin yana dawowa ya soma yi min kiciniyar makaranta ba,ayi wani bata lokaci bana soma zuwa makaranta na tsaida hankalina akan karatu bbu wasa,wayata kanta cire sim card dinnan na ajiye saboda bom boy kam ya takura min.sun rushe gidansu gaba daya an gyara shi an canza masa fasali yayi kyau ainun raba shi biyu sukai ya kasance kofa daya ce amma kowa barinsa daban bbu mai iya ganin wani koda kuwa za,a shekara daya gidajan sun tsaru iya tsaruwa in ba wanda ya sani ba sai yayi tsammanin gidan mutum daya ne,sannan da dan tazara tsakanin gidan wannan da wancan a wannan lokaci aka sa ranar bikinsu mahida da haidar,mamy da ya faruq.
.
A school ina zaune ina shan lemo rani,direba nake jira can na hango bom boy yai fakin bai fito ba na mike na karasa na bude motar na shiga tare da sallama ya zuba min kwala-kwalan idanunsa bai ce min komai ba ya tada motar har muka bar makarantar har muka isa gidansu dake GRA tun daga net nake kallon gidan,gaskiya gidan ya tsaru a kayataccen falon muka zauna ya kawo lemo da keck na dan tsakura domin hankalina na gida kan carpet ya zauna yace min sauko na sauko muka zauna muna fuskantar juna,ya matso daf dani har muna jin sautin numfashin junanmu kamar mai shirin maidani ciki. wahida na dago muka zuba wa juna ido wani irin yarr naji haka nan gabana ya shiga faduwa jikina ya dau rawa amma sai na dake na basar na sunkuyar da kai look wahida ina son ki bani ten minutes,na dago ba tare da shakka ba amma sai me sam na kasa jure kallon kwayar idonsa da kyar na iya minti biyar na sunkuyar da kai wahida ya furta cikin wata kasalalliyar murya na"am wani taimako nake so ki min dan girman Allah wahida ina son fitowa maganar auranmu wahida don girman Allah ki taimaka min wata tafiya ce ta kamani ta tsawon shekara daya in mun samu nasara kan shekara ma zamu dawo ina so ki yadda a hada auranmu da na su haidar a daura inna dawo sai ayi biki a tare,wahida ki taimaka min na mike tsaye tare da kare masa kallo na yamutsa fuska wallahi ka bani mamaki ka bani kunya wai shahid kai wanne irin dakiki ne sau nawa zan fada maka i don't like you na fada yafi a kirga shahid amma zan maimaita maka so ko bana sonka BANA KAUNARKA,wato shi yasa kaje har makarantarmu ka dauko ni kin san abin da kika fada ya fada cikin karaji nine dakikin? i don't know idanunsa sun kada sun yi jajir ya janyo dirowa ya dauko wata kwalba ya daga me zan gani ni wahida barasa dole ne ki sa min mafita cikin biyu daya ko ki amince da bukatata ko kuma yanzunnan insha abin da ba kya so,ka sha man me ya dame ni ya kara rungumo ni idanunsa na fidda hawaye sai dai ko a jikina nace mallam sake ni anki a sake ki nace dama haka ka iya wa ya san abin da kake yi in ka tafi dama irin ku ne masu kama yayan mutane kuna.........saukar mari naji tas,tas, gaba daya na gigice cikin tsananin bacin rai yace tunda nake ban taba zina ba ina mayi ne wahida akanki zan fara ya fizgeni kamar kayan wanki yai dakinsa dani wata irin matsa yai min wadda na tabbata da ciki ne dani da bbu abin da zai hana dan cikin bullutsowa.bbu shiri ban san sanda ya raba ni da kayan jikina ba gaba daya ya gama kidimewa ganin irin baiwar da Allah yai min gaba daya ya gama hautsinani ya gama fita daga hayyacinsa kuka nake tuburan bom boy na gaf da cimma mugun burinsa sai naga yaja da baya tare da sakin oh na manta ina fashin sallah kwalbar nan ya jawo hakori yasa ya balle murfin ya kafa ban ankara ba sai kwalbal na gani ya dire,innalillahi wa inna ilaihi rajiun,tuni na zube gun ina gunjin kuka oh my god,nai sairin saka kayana don kar ya soma haukan yayo kaina gashi kallona kawai yake ina kuka ina karawa ganin ya kwalalo min ido na kara tsurewa ko hijabi ban sa ba nai saurin ina shirin barin dakin yai kirana wahida zo wahida kar ki gujeni zo wahida ba halina bane ya mike yana tangadi ganin ya biyo ni na zura a guje. l  zubewa yai a gurin ya saki wani marayan kuka wanda tunda ya mallaki hankalinsa bai taba tin makamancinsa ba,wahida me yasa ba kya sona?
.
me nake dashi wanda bai miki ba to ke aikina ne ba kya so an sa min billahillazi la'ila ha illa huwa in har ba kya so a yau sai na cire kaki wahida sonki sai ya dafe kirjinsa haka nan ya dinga kwara wani irin amai a cikin zuciyar ya dinga kiran sunan Allah ya yaye ma son wahida in har ba alkairi bane ubangiji Alllah ya yaye masa in kuma alkairi ne Allah ya kwantar da son wahida ya karkato da hankalinta gare shi ta so shi fiye da yadda zata so kanta amai ya dinga yi har ta hanci cikin ikon Allah sai ya samu nutsuwa yana jin matsanancin sonta amma da sauki. wanka yai ya shirya kayansa aka ra min kil ya fito cikin kananan kaya ya kare falon kallo shi kenan na koma legas gida sai na dawo amma na dau alwashin ba zan taba dawowa ba sai da mata,zan ba wa wahida mamaki,waya sa tashin ga ringin gani nan kawai ya ce ya kuma kashe waya manyan hotunan wahidar ya diba ya fita yana rungume fa su bomboy kenan son wahida kaunarta sun hadu sun gama yi masa illa Allah yayi mana tsari damu ya dauka ya matsa kusa da dakinsa ya rubuta da manyan haruffa DAKIN WAHIDA,sannan cikin hanzari na fita.wahida na fitowa taci karo da haidar kanin shahid bai tambaye ta dalilin kukanta ba ya bude mota kawai ta shiga yaja gida ya kaita yana dawowa daga kaita sukai kacibis da bomboy shi yana shirin shigowa bomboy na shirin fita gaba daya suka fita suka rungume juna haidar na dariya ya dago yace bomboy yai tsaki yace ka kula da gida small boy duba dana sonka ba na san wasa ban da tara shashan abokai zaka dinga jina anytime ka dinga bude gidana kana gyara min insha Allahu ba zan dawo ba sai da mata small boy ya zaro ido dariya da tausayin dan uwansa ya rungume bom boy yana hawaye bomboy dago dan uwana please big brother na san irn son da kake yi jaruntaka in kana kuka mahida zata raina ka please na san kan na dawo amarya ta tare zan aiko ma komai na lefe da sadaki tukuncina in dawo in tadda beby me sunan antinmu sukai dariya tare da yin musabaha,haidar ya tabbatar masa zai dinga ziyartatsa akai akai lokaci daya suka shige mota ni dama daga nan nima na tari mai adaidaita sahu domin ga kaini gidansu wahida,domin ba zan iya bin bom boy ba saboda ina tsoron sojoji ainun.ina zaune ina tunanin abin da ya hada mu da bom boy tabbas ina son munafintar kaina maganar gaskiya ina son bomboy sai dai yanzu haishinsa nafi son nasa rinjaye bomboy mashayi ne inalillahi bom boy.........ya amin ne yai sallama ya zauna kusa dani yace yar uwata me yake damunki na ga duk kin canza na lumshe ido nace nothing,ya kuka yi da mutumin? wafa? amir mana na taba baki ni ban ce masa komai ba asali ma ko wayarsa bana dagawa ya kalle ni cike da mamaki kin tabbata bbu wata magata ta batanci da kika fada masa? wacce irin magana sai dai in bom boy don shi na bawa wayar.........
..
haba shi yasa ni na san da walakin,ina zaune amir yayo min waya wai ya fasa auranki ya janye maganar neman auranki nina rasa dalili duk yadda akayi wani abun bom boy ya fadawa amir amma bari inje gidan bomboy din ya mike na bishi da kallo har ya fice.mahida tace"Allah ya haidar ina tunanin sabani suka samu tsakanin bom boy da wahida,wallahi duk tunaninta na gidannan ta kwashe tasa su kasan filo.haidar yace ni ai nasan sunyi fada domin har nina daukota daga get din gidanmu na kawo ta gida kuma daga alama ta batawa bomboy rai domin cewa yayi ba zai dawo ba sai fa mata mahida tai murmushi tace lalle ran maza ya baci ni kaina duk na cina ta fada min abin da ya hada su taki gashi koda yaushe tana cikin damuwa wani lokacin kuma sai tai ta kuka gaskiya abin yana damuna dan ba yadda zanyi domin wahida tana da zurfin ciki dani ce dai da tuni na fada mata ko dan ta bani shawara.ina kwance jikin mom tace wahida wai me ya hada ku da shahid? mom bbu komai illa na fito face to face na fada masa i don't like you in da sabo wannan kalma bomboy ya saba jinta amma tsabar naci ya mannen sannan nace in har ya cika shahid alitu muhd kar ya dawo daga legas sai da mace ma'ana yayi aure ba abin daya shafen,ke auta haka kikace masa so what a kan me zai takura min in ban da naci nace bana sonsa bana kaunarsa dan me zai takura min?mahida tace nina san ruwa baya tsami banza don ubanki maga wanda zaki samu me sonki da gaskiya shima shahid dinne ya manne miki amma kamar shahid wanda yanmata suke rububinsa har zaki wulakanta Allah yasa in zai dawo ya taho da matar muga karyar wulakanci,wahida kin mare shi akan yace yana kaunarki kin zage shi akan yana sonki kin tofa masa yawu......
.
to wai ina ruwanki banza uwar shishigi yar ficika sunan data tsana da gudu ta biyo ni nai dakin yaya ina mata gwalo.abin kunya abokansa sun cika dakin na riga na shiga don haka nai bed dinsa bayan sif dinsa ina boye ta shigo tana wallahi sai na dokeki,
.
BANA KAUNAR KA 18
.
ya amin yace mata meya hada ku ta ce zagi wahida fito na fito nace ya zanyi ta dinga raina min hankali wai acikinku waccece babba? da sauri wani abokin yaya saifu yaya amin yace ke wahida bata hakuri yaya itace fa ta fara tsokanata ni dai nace ki bata hakuri kiyi hakuri mun juya zamu tafi yace kuzo nan baku iya gaisuwa ba ko ba kuga baki nai ba na kalleshi kunya ta kama ni da gudu na fita dakin mom na shiga na kwanta jikinta mahida ta shigo nace mahida don Allah kama min kaina ai kuwa sai dai ki mutu....
.
please anty wahida, ina kwance ina yiwa mom hira har bacci ya soma daukata,mahida ce tace daga ganin yadda wahida take lumshe ido bacci zatayi mom tace ai gwanda tai bacci muma mu huta da rigima,mahida tace mom in tambaye ki ina jin ki kar fa kiji haushi mom tai dariya wanne irin haushi wai mom ina iyayenki? ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina ne garinku sannan ina yan uwanki? hawaye mom suka digo min a kumatu,zumbur na mike ke mahida dan me zakiyi wa mom irin wanan tambayar me daga hankali,wai ma ina ruwanki gashi nan ai gashi kin sata kuka ya amin ne ya shigo ganin mom tana hawaye duk sai ya rude ya tsunguna gabanta yana fadin lafiya nace ba mahida bace ta saka ta kuka meye tayi mata?
.
  wai cewa tayi mom ina iyayanki ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina yan uwanki,ina ne garinku kuma kina da yan uwa koke kadai ce? ya amin yace kiyi hakuri kin ji mominmu ke kuma mahida kar ki kara yi mata irin wannan tambayar mai tada hankali mom tace ba komai ku kira faruq sai in baku labarina ya amin ya kira faruq suka nutsu kamar masu cin dan wake don jin labarin mom.
.
Da farko dai ni sunana maryam mahaifina mallam abdulkadir haifaffen gyambu ne auran zumunci akai musu shi da mahaifiyata fulani ne sosai mahaifiyata ta kasance tana tallan nono kasancewar mahaifina ba shi da hali koda ta haife ni sai ya kasance muna tallan nonon tare ko dana girma sai nace inna ta zauna ni zan ci gaba da yin tallan,mahida tace Allah ya kiyaye in yi tallan nono yaya yasa kafa ya doke ta mikewa tayi ni bazan ji labarin mom din ba nina dauka iyayen mom masu kudine kamar abbanmu,ya faruq yace in baki zauna ba sai na duke ki da sauri tace na zauna yi hakuri yaya nace sannu yar masu kudi waya sani ma koda abban dako yake yi sai lokacin ya amin yai magana yace ku tashi ku fita yaya yi hakuri ni dai ba zan kuma magana ba mom cigaba.
.
a wanan lokacin na hadu da wani saurayi wai shi jauro ya nuna yana sona domin kullum naje kasuwa sai ya goyo ni a mashin dinsa ya kawo ni gida abu kamar wasa har aka sa ranar bikinmu da jauro,amma har lokacin ina tallan nono mahida tai tsaki domin bbu abinda ta tsana irin tallah bbu wanda ya kulata koda lokacin biki ya zagayo akayi biki irin na al'adarmu an daura aure anzo an min jere iya bakin kokarin iyayena sunyi kokari.amarya ta tare iyayan jauro masu kirki sai dai suma basu da hali domin duk rashinmu mun fi su hali domin su tun safe za a dama kunun nono shine abincinsu sai kuma wata safiyar sam ba a ruwo sai ranar sallah sai dai madarar shanu in kana so ka tatso shi kuwa jauro tun safe inya fita sai can dare a waje yake siyan abincinsa mai rai da motsi a haka na soma laulayin ciki kasancewar cikin na bani wuya ga yunwa duk sai nabi ba tsotse gashi mahaifiyar jauro sam bata tausaya min tunda ta fuskanci ina da ciki sai ta shiga muzanta min komai ni zanyi gashi yanzu jauro in ya fita ya kan yi sati,
.
sati biyu baya gida wata dawowa da jauro yayi tun kan ya huta inna tai kiransa bi ban san abin da ta sanar masa ba ya dai kama ni da duka sannan yace inje gida tun kan naje ya hau mashin yaje ya shirya min karya gun babana ban san abin da ya fada ba a kofar gida na tadda bbana na tsunguna ina gaidashi yace haba yarinya ai mijinki ya fada min komai ashe in baya nan yawon banza kike kinje kin samo ciki kin zo kin manna masa ko to kin wa kanki amshi takarddarki yace ya sake ki anshi nace,hannu nasa na amsa ina kuka ki kama hanya ki san inda dare yayi miki don ba za ki haife min shege a gida ba,
.
na tsunguna ina kuka ina bashi hakuri amma faruq yace sai na bar masa gidansa ganin dare yayi nace don Allah ya barni in kwana gobe na nemi hanya nan yayi ta zagina yana tsine min ganin yana tara min jama a sai na tafi ina kuka ga duhu ban san sanda naje titi ba wani mai mota ya faka kusa dani yace baiwar Allah shigo in rage miki hanya nace to ko da na shiga ban kuma sanin inda nake ba sai farkawa nai na ganni a wani katon gida girman gidan ya wuce hankali.
.
na kalli wasu mata dake ta kuka nace bayin Allah me ya kawo ni gidannan matan suka ce suma basu sani ba domin wani mutum ne ya kawo su gabana ya fadi nan nai ta addu a cikin zuciyata wani katon mutum shirgege yazo inda muke ya ce zan shiga dakinnan daya bayan daya ku dinga shigowa yana shiga aka dinga shigar da mu ashirin ne ni ce ta karshe ina shiga sai naga dukanninsu an musu aski.
.
Topah mezai faru?..
.
Kuna tare dani kuwa?

0 comments:

Post a Comment