Friday, 19 January 2018

'Yar Mafiya Part 1 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI



Doguwar Yarinya na hango matashiyan mai ji da jini a jika shekarun ta bazai wuce ishirin da uku zuwa da hud'u ba kallo d'aya zaka mata ka gane tana matuk'ar ji da kanta tamkar 'Yar gidan sarauta, fara ce kuma tana d'an tsayi sannan bata cika kyan d'aga hankali ba amma tana da gizo wanda duk ya kalleta zata na yi masa gizo, tana da idanu manya-manya wanda in ka zuba musu ido na wani d'an lokaci zakaga suna canza kala, ko da mukayi duba zuwa fuskan ta daga gani tana cikin matsanaci b'acin rai take yanayin hallitarta tasoma canza wa, da gudu ta fito daga falo ta nufi d'akin ta da ke can k'arshen d'ankunan k'ofar ta rufe take ta fara wani irin gurnani tamkar namiji zaki wanda yunwa ya dame shi ya fito farauta, cikin tsoro na kalli Sanah na ce"ke kalli yanda takeyi nikam zan gudu don na tsota da ita na fasa kwasan labarin". Wani harara Sanah ta aika min da shi ta ce"dad'i na dake kin fiye tsoro kamar farar kura ba gani a kusa da ke ba? To miye na tsoron?". Hannuna taja mukaje tagar d'akin da ta shiga muka leka, cikin tsoro nake shirin sakin k'ara Sanah ta toshe min baki ko da na k'ara duba wannan Yarinyan ne ke hawaye amma na jini kanta ke firda wuta tamkar an kunan itace da gass, tafin hannuta ma haka yake fitar da wuta kayan jikinta suka canza kala zuwa ja-jazur, cikin murya mai ban tsoro ta ce"Baba mai yasa zakayi haka? Shin kasan had'arin da ke cikin wannan al'amarin kuwa? Kasan halin da Yasar zai shiga kuwa? Ina tsoron Samar in yaji wanan al'amarin shikenan zaku rasa Yasar". Cikin tsoro Sanah ta kalleni"Rash wai mike faruwa ne?", ba tare da na bata amsa ba na kamo hannuta muka nufi falo. Muna daga k'ofa mukaji wani dattijo ya na ce ma Yasar "Allah ya maka albarka tabbas nasan bazaka watsa mana k'asa a ido ba". Wanda aka kira da Yasar kansa na duke a k'asa ya amsa da "Ameen Abba" ya sake rusunawa ya ce"ni zan koma gida naga dare ya soma yi", Tsohon nan ya amsa da"to Yasar ka sauka lafiya ka kula". Cikin girmamawa ya fito yashiga motar sa ya nufi gidan sa ko da ya shiga gida muna biye da shi gate(gareji) ya rufe tare da komawa mota ya ja ya kai gun ajiye motoci ya ajiye motar, ya fito ya fara tafiya irin na gaye wanda ke ji da kansa da kuma boko ya shiga cikin falo tare da mai da k'ofar ya rufe ya nufi hanyar matakala, tass! Tass!!  Tass!!! Kake ji k'arar d'aukewar wuta tare da wani irin walk'iya mai had'e da k'ara tare da tsawa aciki wanda ya samu komawa baya da gudu,  cikin jarumta irin na maza ya soma lalub'en hanya dai-dai k'ofar d'akin ya hango haske wanda ya hango takun sawun k'afa zalla da jini ajiki yana bin hanyar da zai bi, cikin hanzari ya juya zai koma sai ganin yarinya k'arama tana tunk'aroshi ta ware hannuta alamar oyoyo, ga idanun ta yana fitar da hawayen jini bakin ta ma na zubar da jini cikinta yana juyawa da ida mutun yake zai na iya hango zalla jinin da ke juyawa a cikinta, cikin kid'ima yarasa baya zaiyi ko gaba yana juyawa ya ga yarinyar na dariya ta b'ace da gudu yayi hanyar sauk'owa daga matakalar benin, sam ya kasa yin addu'a bare daman shi ba gwanin yin addu'a bane(kira ga 'Yan uwa yana da kyau mu kasance cikin addu'a akullum kar muna mantawa fa Annabi ya koyar mu addu'o'i tun daga kan nashiga bayan gida har da na fita a gida dan Allah mu dage baran yanda zamanin nan ya zama).
    Masu karatu ku biyo 'YA'YAN MUTAN;
Cikin matsanancin tashin hankali ya cigaba da ja da baya. Cigaba tayi da bibbiyarsa bakinta yana hayak'i"kayi kuskure Yasar na shiga komar matsafiya,bazan ragama kaba bana yafiya bana mantuwa saina kassara rayuwarka da duk wanda ya bibbiyi rayuwar god'iyata."Cikin muryar tashin hankali yake fad'in "wacce ce ke? Meye alak'ata da ke? ".
Wata shu'umar dariya tayi,ta huro iska mai tsananin zafi da k'arfi take ta d'agashi sama ta wulwula ta dokashi da bango. Kansa ya tsage, ya soma zubar jini lau ya fad'i k'asa yaraf! 'Dif! Numfashinsa ya d'auke.
Ammar ne ya taho cikin wak'e-wak'ensa kamar an ce dubi can idonsa yakai kan Yasar kwance cikin jini. Wata giggitaciyar k'ara ya saki hakan ya jawo hankalin mutan gidan da gudu sukayo shashin.Ganin halin da yake ciki ya d'aga hankalin kowa, nan da nan aka sashi a mota aka nufi asibiti da shi. Cikin gaggawa aka karb'eshi zuwa emergency (wajan taimakon gaggawa).Likitoci sun duk'ufa a kansa, harzuwa lokacin bai dawo hayyacinsa ba, mahaifiyarsa banda kuka babu abinda take. Saida sa'a uku ta shud'e sannan ya dawo hayyacinsa, an masa k'arin jini sannan aka hana kowa zuwa inda yake saboda suna san auna k'wak'walwarsa.
Cikin tsoro naja hannun Rash cwt muka bar wajan.
Wata shu'umar dariya aka saki, "hahahahahaha! Munyi nasara,munyi nasara".Aka fad'a da wata rikitaciyyar murya gaba daya wajan ya amsa amo suka saki dariya. Sanye suke da jajjayan kaya mazansu da matansu, idanunsu wani irin launi tamkar Rainbow (bakan gizo) akaifarsu zak'o-zak'o tamkar horaye, hak'ora sun zazzago duk gashin kansu ya mimmik'e tsaye dukkansu kayansu jajjayene kowanansu rike da k'ok'on jini suna sha.
Kwanan Yasar uku a asibiti aka sallame shi, saidai an bashi magunguna tare da gargad'i kan ya kiyayye buga kansa saboda saura k'iris yayi loosing memory d'insa. 
Duk tsayin kwanakin da ya yi a asibitin babu Yasiraht babu alamunta wajan zuwa dubiya, lamarin daya tunzura zuk'atan 'yan uwa da dama harya haifar da kace nace a ciki.
Tsayin kwanakin yana samun sauk'i sossai, har ya koma wajan aiki. 
"Yasira gaskiya da sake"cewar Samir dake zaune kan mota fuskarsa babu alamun walwala. Tayi ajiyar zuciya tana dubansa ranta duk a cakud'e hawaye ya ciko ido taf tasa hannu ta share. "Samir bansan ya zamui ba, Baba ya dage kan lamarin sossai.Gashi shugaba kullum cikin gargad'ina take bisa kaucewa dokar k'ungiya".Ta k'arasa maganar cikin raunin murya.
Cikin kaushin murya yace"zanyi hukunci"cikin sauri ta tari hanzarinsa "nasan hukincinka bahagone Samir karkayi pls na rokeka."Bai jira cewarta ba ya kwashi mota da tsananin gudu yabar harabar gidan. Durkushewa tayi take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar.........
Durk'ushewa tayi take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar......
TUSHEN LABARI......
Alhaji Sani Marafa haifafen d'an garin Bauchi ne, iyayensa fulanin ne gaba da baya, ya kasance d'an boko ne sosai yayi karatun boko amma hakan bai sa ya kauce ma hanyar Allah ba, ya kasance mai zafin nima tun yana matashi duk da aikin k'arfin da yakeyi hakan bai hanasa karatu ba.
Cikin ikon Allah Alhaji Sani Marafa ya kammala degrees d'insa na farko a kan Business Administration yana kammalawa bai dad'e ba ya samu aiki a Ministry of Housing(ma'aikatar kula da gidaje) inda aka bashi Accounter (mai kula da kud'i) na gurin.
Bai dad'e da samun aiki ba yayi aurensa na farko inda ya auri matarsa Nafisatu, Nafisa macece mai kirki da girmama mutunane tana matuk'ar girmama iyayensa da 'Yan uwasa wanda hakan bak'aramin dad'i ya ke masa ba suma 'Yan uwansa suna sonta.
Yau ta kasance safiya da ta sanya iyalan gidan Marafa kuka wanda sukayi rashin 'Yarsa guda d'aya mai Suna Maryam, Maryam ta rasu ta bar Yaro kwaya d'aya mai suna Yasar wanda akala ya kai shekara biyar aduniya, Yasar yaro ne mai shiga rai gashi da hankali amma ya taso cikin gata don duk abunda yakeso shi za'a masa sabida ubansa yana da kud'i dai-dai gwar-gwado.
Bayan zaman bakwai Yasar yak'i zama gun kowa sai Alhaji Sani hakan yasa suka d'aukesa ya dawo hannusu da zama, duk wani gata da mahaifiya zatayi wa d'anta Hajiya Maryam tana k'ok'arin gwada masa sun sanya shi a makaranta *ANSS* makarantar da ake ji dashi a cikin garin bauchi Yasar ya fara karatun sa cikin kwanciyar hankali, amma sam baya son zuwa Islamiya sai da kyar gashi yana da k'ok'ari sosai yana da hazaka da saurin d'auk'an karatu.
Yau Hajiya Nafisatu ta tashi da zazzab'i sosai wanda har sai da aka kai ta Asibiti ko da likita ya gwada ta ya tabbatar ma Alhaji Sani Marafa tana d'auke da juna biyu ohoho masu karatu karkuso kuga murna a gun S Marafa haka sukayita kula da cikinta tare da ta abubuwan da akeso mai ciki tana ci.
BAYAN WATA TAKWAS..
Yau Hajiya Nafisa ta tashi da matsanacin ciwon mara da baya kasancewan Alhaji na gida bai tsaya b'ata lokaci ba sukayi Asibiti, suna zuwa likita ya shaida masa haihuwa ne yake aka shiga da ita labour room (d'akin haihuwa) sai da ta sami kusan awa guda tana nak'uda cikin ikon Allah ta haifo d'iyarta fara sol da ita, ko da aka sanar da S. marafa Hamdala yayi tare da gode ma Allah ko da aka gyarata suka nufo gida, tun da Yasar ya dawo daga makaranta ya samu Hajiya Nafisa haihu Yasar ya tasa 'Yar gaba ko 'Yan barka in sun zo a hannusa suke ganinta dakyar wani zubin ke bada ita a ganta, Hajiya Nafisatu da S Marafa suyi ta ma Yasar dariya don suna jin dad'in yanda yake nuna ma 'Yarsu k'auna.
  
Ranar suna yarinya taci sunan Yasiraht, kulawa sossai Yasir yake bata. Goyo wankinta har kayan kashi tun Hajiya Nafisat na hanashi harta zuba masa ido in yai wani abun sai dai tai murmushi tace "yarinta".
Kwanci tashi Yasiraht ta isa yayye aka yayyeta, ranar ansha kuka da rigima sossai dan Yasir kusan kuka ya yi saboda ganin hawayanta. Shekarun Yasiraht uku cif tayi girma sossai ga kyau ga surutu, dungui-dungui Yasir ke koya mata A B C D.........nan da nan ta iya kamun kace kwabo ta'iya zuwa Z.Hakan yasa Hajiya Nafisat ta shawarci mahaifinta ya sata makarsnta. Makaranta mai tsada ya sakata,boko had'e da islamiyya in an tashi boko sha biyu da rabi, ake shiga tahafiz sai shida. Karatu sossai ake a makarantar, Yasir ya tsaya mata wajan lesson da bitar karatu. Tana primary four ta haddace izuf sha biyar mahaifanta sunji dad'i tare da shirya mata k'ayataciyar walima.
Manyan Malamansu da dama sun hallata, tare da jinjinawa iyayanta. Haka akeso idan yaro yayi kokari a yaba masa basai kin kashe kudiba koda biscuit kikai masa kyauta zai ji dad'i ya samu karfin guiwa. Kwanci tashi al'amura suka cigaba da gudana. 
Tunda Yasiraht ta shiga aji biyar Hajiya ta haifi kyakkyawar diya wadda taci sunan Yasmin,ba laifi kyakkyawa ce amma bata kama koda yatsan Yasiraht ba. Shigarta aji biyar ta soma adabar gidansu da batun boarding school, lamarin daya daga hankalin kowa a gidan ssboda basa san nisa da'ita.Tun suna lallab'ata har suka soma yi mata fad'a lamarin daya jawo kukanta sossai. Yasir shi ne sarkin lallashi,  a hakan suka zana jarrabawar gama primary tana da shekaru tara cif, abin kaddara result ya fito Yasiraht taci bording school lamarin daya kawo musayar ra'ayi sossai akan tafiyar. Mahaifinta na ganin tayi kankanta, babu yadda zai yi haka ya barta ta tafi saboda farin cikinta Yasir daya jagoranci tafiyar yafi kowa jigatuwa. 
Makaranta Mata da ke garin Kano ta dabo tumbin giwa aka kaita S Marafa da Yasar su sukaje tare da ita aka gama komai aka bata JSS1A su Abba da Yasar basu bar makarantar ba sai da suka tabbatar da an had'ata da Senior (Na sama da ita) kafin suka mata sallama tana hawaye Yasar na hawaye yana rik'e da hannunta da kyar Abba ya raba hannusu suka shiga mota suka bar makaranta.
Rayuwan Yasiraht haka ya cigaba da gudana aciki kwalejin mata da ke garin kano tana karatu dai-dai gwar-gwado sam bata faye yawan kawaye ba sai k'awarta d'aya wato Shukura Adam ita 'Yar cikin garin Kano ne nasu yazo d'aya komai tare sukeyi wasu har suna musu lak'ani da 2stars(taurari biyu) don itama Shukura ba baya bace gurin kyau amma ita bak'a ce.
Seniors da yawa suna kawo musu farmaki akan suna son su da School daughter(d'iyar makaranta) duk wacce ta tsare su sai suce mata a gida an hanasu yin School Mummy(uwar makaranta) wasu daga lokacin da sukak'i amincewa musu zasu fara gallaza musu da zangwama.
Yau take Visiting day (ranar ziyara) duk wani d'alibin da ke makarantar yayi kitso tare da wanke uniform d'insa na makaranta kowa ya fito tsaf sabida zuwan iyaye da yayu/kanne, hakan yake a gun Yasiraht don gayu tayi tana jiran iyayenta can taji wata 'yar ajinsu tazo tana cewa wai ana kiran Yasiraht S Marafa a bakin gate(gareji) yihuhuhu!!! Tayi wani tsalle tare da rawa Shukura sai dariya ta ke mata ta ce"kai Yasiraht irin wanan murna haka?". Yasiraht ta juya ido ta ce"ya bazanyi murna ba yau My Yasar d'ina ya zo tare da Abba na da Ummi na ga swt Yasmin d'ina". Shukura tayi murmushi suka mik'e suka sanya kaya suka fita tare.
Ko da sukaje gunsu Abba da gudu taje gun fa rik'e hannusa tare da fad'i i miss you my Yaya na(nayi kewar ka ko rashin ka)Yasar sai dariya ake mata tukun tazo ta rusuna ta gaida su Abba kayan abinci suka kawomata tare da girki mai dad'i haka sukayita hira har lokacin tafiyansu yayi wanda da kyar sukarabu.
BAYAN SHEKARA UKU.......
Wata kyakwan Yarinya muka hango sanye cikin uniform d'in makaranta  ta fito sai zun b'ure baki takeyi, Yasar ne ya kalleta ya ce"My sisi dole yau ki koma makaranta tunda ke kika zab'a da kanki". Yayi maganar cikin tsokana tare da yi mata gwalo biyo shi tayi da gudu zata kwad'a masa jaka dake hannuta ya tsere, Abba ne ya fito wanda hakan yasa suka nutsu mota suka shiga suka d'au hanyar kano tun a mota take kumbura har suka iso makaranta ko sallamar kirki bata musu ba sabida fushin da takeyi, ta saka junior (na k'asa da ita) suka tayata d'iban kayan ta ta tafi hostel.
Sam yanzu bata jin dad'in makarantar sabida an cire Shukura a makarantar yanzu bata da k'awa sai wata Najwa da ke damunta akan suyi kawance dole ba yanda ta iya ta fara bin Najwa sabida Najwa ta faye naci, wani saran da Yasiraht ta samu sam yanzu bata yawan addu'a komai yinshi take batare da ta nimi kariya daga gun Allah ba.
Wata rana ta kwanta cikin mafarkinta ta ganta a cikin dokar daji sai jin tayi ana kiran suna ta kuma muryan bibbiyu yake fita ga daji ba haske ko tafin hannuta bata gani sai daga can nesa ta hangi wani haske cikin sauri ta k'arasa nan taga wasu irin halita tare da jajayen kaya ajikinsu suna cewa" Yasirah mu na gayyatar ki cikin mu ki zo zamu baki matsayi babba". Muryan mutane dayawa takeji take ta toshe kunnenta aiko sai guri ya fara tsawa rugugugu!!! Tamkar zai zaga kasa ta shiga ciki ko ina na jikinta b'ari yakeyi.
Kasan gurin ne ya fara darewa gida biyu nan tasoma ja da baya tana gudu yana tsagewa ko da ta kalli cikin k'asan da ya tsage ba komai ciki face kogon jini da kwarangwal suna kiranta. Cikin ihu da k'araji ta farka sai gumi takeyi sam ko addu'a ta kasa bare tasamu nutsuwa Sanah ta ce"ni ko anya Yasiraht tana addu'a?". Can na tsaya tunani na ce" ni dai ganina da ita na k'arshe da tayi addu'a tun tana JSS2 aji biyu a zango karatu na farko(first term) Sanah ta jin-jina kai(lalle tana sakaci da addu'a kamar yanda wasu acikin mu suke wasa da addu'a ma kansu bare 'Ya'yansu dan Allah mu kula muringa addu'a don neman kariya Allah ya kare mu da iyalan mu ameen).
Tun daga wannan lokacin aka shiga tsorata Yasirsht, tana gayawa Yasar musamman in yazo mata visiting amma data ayyana hakan sai wani gaggarumin tsoro ya dumfari zuciyarta. Lamarin daya haifar da tarin k'alubale cikin lamuranta na yau da kullum ta soma bak'i da rama ga yawan kad'aici da san kusantar wajan da babu hayanniya musamman dajin cikin makaranta, Lokuta da dama can take tafiya, tai ta shawagi tana yawace-yawacenta.
Abin ya soma ta'azara a gareta, musamman in zata ci abinci ko ruwa sai taga sun sauya launi zuwa jini. Gashi met d'inta sun fara damunta idonta yana tsoratasu saboda rikid'ar da yake yi. Ana haka kwatsam wata rana Yasar ya kawo mata ziyarar bazata shi da Yasmin tayi murna sossai. Suna tsaye suna hira,Yasiraht ta hango abinda yasa ta dinga jan baya..........
Wani k'adangare ta hango suffarsa sake, irin ta mutane ya mik'e yana tafiya zuwa wajan da suke. Dariya yake mata sossai ya bud'e hannayansa yana fad'ar"maraba da mataimakiyar shugaba ki zo garemu zamui miki kyakkyawan masauki".Wasu hallitu masu kawuna suka bayyana gefansa, suna masu biyo bayansa bakunansu biy-biyune wata giggitaciyar k'ara ta saki tai baya. Yasar yai saurin kai mata cafka, lau ta fad'o jikinsa babu numfashi babu alamunsa.
Hankalinsa ya tashi sossai, da sauri ya bude motarsa yana neman ruwan da zai yayyafa mata da kyar ya dai-daita nutsuwarsa ya samo yana zuba mata ta saki  ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta.Zuba mata ido ya yi yana nazarinta.
"Lafiya Yasiraht? "
"Babu komai".
Ta bashi amsa tana inda-indar rashin gaskiya kai ya jinjina kawai suka cigaba da hira jikinsa a sanyayye.
Sun dad'e suna hira kafin ya bata sayyya sa suka mata da 'yan kud'ad'e suka mata sallama cike da kewar juna suka tafi, ita kuma ta dawo hostel tana kewan gida kayanta ta jera a locker tana gamawa ta kwanta a kan gado tare da lumshe ido tana tunanin gida don yanzu duk makaranta ya isheta baran ma da Shukura ta bar makarantar sai da lokacin sallah magriba yayi sannan ta tashi tayi alwala ta nufi masallacin makaranta. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment