Friday, 19 January 2018

'Yar Mafiya Part 2 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI


Wata giggitafiyar k'ara ta saki tana ja baya, a hankali haske ya gauraye komai ya dawo mata dai-dai.A rikice Yasar ya juyo hakan ya haifar da sub'ucewar sitiyarin hannunsa motar ta kaucewa titi ta nufi daji.Wata k'atuwar bishiya ta daka cikin ikon Allah gaban motar ne ya lotsa,da sauri ya fito ya bud'e sashin da take ciki. Sai sauke ajiyar zuciya take, hannunta ya kama jinsa ya yi yayi sanyi k'alau das!Gabansa ya fad'i sakammakon ganin yadda idanunta ya sauya cikin rikicewar murya yace. 
"Yasiraht lafiyarki kuwa? ".
Ya fad'a da tsorataciyar murya,
Muryar tace ta sauya tare da bud'ewa, "me ka gani ne?" take ya soma ja da baya a tsorace binsa take launinta ya cigaba da sauyawa wasu hak'ora suka bayyana zak'wazak'wa jini na zuba daga idanunta k'ara ya saki ya yi cikin daji da matsanancin gudu take dajin ya kaure da wata hatsabibbiyar dariya ta cigaba da kuwa da karad'e kunnuwansa. Gaba daya ya rikice can tunanin adu'a ya ziyarci zuciyarsa, take ya soma karanta ayatulkirsiyyu.Wata hajijjiya aka yi dashi ya bugu da bishiya take kansa ya fashe ya fadi babu numfashi.
Shud'ewar rabin awa ya farfado ji yayi kansa ya yi nauyi, ya bude ido a hankali shasshek'ar kukanta ta karade kunnuwansa ya shafa goshinsa babu ciwo sai dai jikinsa ya tsamamma sossai. Ga mamakinsa sai ya riski kansa a bigiran da suka bar motarsu lamarin ya girmi kansa an janyo motar zuwa kusa da hanya. Ya bud'e baki zai yi magana,suna hada idanu wani matsanancin tsoro ya ziyarce shi ji ya yi yaka katabus. 
"Tashi mu tafi gida".
Ta fada babu walwala,tayi gaba bin bayanta ya yi tamkar rak'umi suna isa tace "shiga muje".Jiki a sanyaye ya shiga yana tada motar ta tashi suka dauki hanya. Kansa ya yi zafi da yawa, a haka suka karasa gida babu um babu um um.
Ganin yanayin su ya tashi hankalin iyayansu, cikin damuwa suke tambayarsu abinda ya faru haka kawai Yasar ya samu kansa cikin kasa magana Yasiraht ce tayi bayanin cewar hatsari suka yi mamaki ya kashe Yasar amma ya kasa magana saboda fitinan nan kallon da take jefa masa a sace wanda yake hautsina kwanyarsa.Sun jajjanta musu sossai kai tsaye Yasar ya nufi sashinsa bakinsa a nauyayye zuciyarsa cinkushe babu damar magantuwa. Yasiraht taja hannun Yasmin suka nufi sashinta,take akasa masu aiki suka fita da motar bayan an fitar da kayan Yasiraht.
Yasar yana shiga sashinsa ya zube a kan gado, mamakin Yasiraht yake sossai, ji yayi inama ya fad'a abinda ya faru amma daya yi yunkurin hakan sai yaji bakinsa yayi nauyi. Kansa ya sara yana tsananin ciwo.
Tana dawowa daga sallah jakarta ta d'auka ta nufi night prep tana zuwa ajinsu ta zauna ta ciro takardunta tasoma nazarinsu  can zuwa wani lokaci kamar daga sama sai taji wani abu na zagaya k'afarta da sauri ta kalli k'asa bata ga komai ba, a hankali ta d'an matsa da k'afar taci gaba da k'aratu kamar ance juya ki kalli wajen tagan ajin sai ganin wani kujera yana yawo a sama ga kwarangal suna kewaye da gun wani ruwa jini da ke bin ta gefen kujeran yana sauka a kasa sai aka masa hannu da kayukan mutanane a firgice ta mik'e tare da runtse idonta tana hawaye.
Senior da ke ajinne ta daga mata tsawa ta ce"ke Yasiraht lafiyar ki kuwa mai ke damun ki kwana biyu?". Yasiraht ta sunkuyar da kai tare da zubar da hawaye ta ce"Sister nima ban sani ba". Kai Senior ta jin-jina ta ce"zauna to", haka sukayi prep d'in har aka tashi ta nufi hostel tana zuwa ta cire kayanta ta sanya na bacci ta kwanta a gadonta tana tunane tunane kala-kala idonta ta lumshe tana tunano abubuwan da suka faruwa da ita a 'yan kwanakin.
Najwa ne tazo ta dad'e tsaye a kanta tana murmushi Yasiraht da idonta ta d'an rufe sai taga kaman wani irin hallita shi ba cikaken mutum ba sannan shi ba dabba halitta mai ban tsoro cikin sauri ta bud'e idonta sai ta ga Najwa wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki tare da mik'ewa ta zauna ta ce"Najwa  ya kike? Ban san shi gowarki". Najwa tayi murmushi ta ce"na dad'e anan ai", nan suka zauna suna hira sai kusan goma Najwa ta mik'e ta ce"barin tafi d'akin mu", Yasiraht ta mik'e ta ce"nagode sosai fa muje na rakaki". Suna tafiya suna hira har ta kai ta d'aki ta dawo.
Kwanaki sun tafi abubuwa da yawa sum faro Yasiraht ce na hango cikin murna tana had'a kayanta a trolley d'inta sabida gobe zasu tafi hutun zango k'arshe na karatu(thirt term) sai da tagama kimtsawa ta hau gadonta ta kwanta tana tunanin Yasir a zuciyarta Najwa ne ta shigo nan ta tashi ta zauna suka fara hiran rabuwa sun dad'e suna hira Najwa ta tazo ta fiya  har sunyi nisa ta juyo ta kalli Yasiraht ta ce" yauwa k'awata ga chocolate(alewa) nan d'azu naje school shop na sai mana". Cike da murna Yasiraht ta amsa tayi godiya da kyar suka rabu.
Washe gari da safe suka gyara hostel sannan suka nufi assembly suka jeru sukayi layi sai zuwa can principal tazo ta ke d'alibai suka mik'e sai da suka gabatar da national anthem kafin suka zauna aka bud'e taro da addu'a bayan sun gama shugaban makaranta tayi bayani tare da cewa hutunsu zai kasance sati shida tana gama jawabi aka sallami d'alibai da murna suna ihu kowa ta fito gate d'im makaranta.
Yasiraht tana fitowa ta sami su Yasar sun zo d'aukarta jikinta a sanyayae ta gai dashi sai da yayi ta tsokana nanta sannan suka shiga mota suka d'au hanya sunyi tafiya mai nisa Yasmin har tayi bacci can ta tuna da chocolate d'in da Najwa ta bata da sauri ta d'auko ta b'are zata saka abakinta Yasar ya ce"abun 'yar haka ne wato rowa zaki min ko", cikin fara'a ta ce"wacce ni na isa na maka rowa..." Fiskansa d'auke da murmushi ya ce" bazaki min dad'in baki na yarda ba", can idon ta ya kai kan ledar chocolate da sauri ta d'auko ta ce"la ga naka ai kai ka fara min rowama ai.
Chocolate d'inta ta saka a baki ta fara taunawa ta had'iye take tafara ganin wani irin walkiya da tsawa tamkar saukar aradu nan ta bar ganin haske sai duhu can ta hango wasu kwarangwal tare da wani irin suffar halittu suna cewa"Yasiraht muna miki murna da shigowa k'ungiyar mu muryoyi ne da yawa nan gashi sai gani abubuwan ban tsoro da firgici.
*9*
Jikinsa ba k'arfi ya mik'e ya nufi d'aki bayi ya shiga ya watsa ruwa tukun ya d'auro alwala yayi sallah ko abinci bai tsaya ci ba kasancewa lokacin bayan sallah azahar ne, kan katifansa ya fad'a ruf da ciki yayi ya baje k'atifansa sai bacci ne ya d'auke sa mai nauyin gaske.
Yasiraht kuwa tana shiga d'aki ta ajiye Yasmin ta rage kayan jikinta ta d'aura towel ta shiga wanka, sai da ta dirje jikinta sosai bayan ta d'auraye sannan ta k'ara yin wankan acewarta yau ta dawo gida dole tayi wanka na musamman, tana gamawa ta d'aura tawul ta fito tana goge jikinta da d'an k'arami tawul sai da ta goge jikinta tukun ta jawo k'aramin kujeran da ke jikin madubin ta zauna, sai da ta shafa mai tukun ta matso sai tin madubin don yin kwaliya.
Wak'an ta takeyi ta had'a kayan gu d'aya ta d'ago da zumar kalo cikin madubi da sauri ta mik'e tawul d'inta har na fad'uwa a kasa hakwara ta gani ta madubi suna zubar da jini tare da dariya, cikin sauri ta juya taga Yasmin na wasanta kalon madubi ta sakeyi bata ga komai ba, fauda ta shafa kawai ta fasa kwaliyan ta d'auko riga da skirt d'inta tasaka suka nufi falo don cin abinci.
Gudu ya ke zuba wa tamkar k'afafunsa zai fita ihu ya keyi yana niman agaji amma ko alaman wani babu a cikin dajin ga wasu manyan hallitu hak'waransu a waje suna gudu suna fisgan naman mutane wasu ko k'ok'on jinine a hannusu suna sha yana zubowa bakinsu sai da yayi gudu duk ya gama galabaita ya iso bakin wani k'aton rami wanda in kafad'a sai dai wani ba kai ba ko k'arshe ramin baya gani wani irin iska yaji mai had'e da guguwa a razane ya juya bayansa.
Hahaha sautin wani dariya da yaji cikin hanzari ya kali sararin samaniya inda yaji dariyan gudan kai ya gani a saman kujera yana yawo ga wani rin hayakin da ya turnuk'e kujeran sai da kujeran ta ju-juya a sararin samani tare da tsawa da walkiya takeyi ta soma matsowa gunsa gani haka yasoma ja da baya ba tare da ya kalli bayansa ba dai-dai lokacin ya kai bakin ramin suuuu ya tafi tare da sakin wani razanane k'ara.
Suuuuu! Yai tafiyar burgu zuwa cikin ramin, wata giggitaciyar kara ya saki daidai lokacin ya farka cikin tsananin firgita yana sambatu.Bakinsa na furta kalmar _"Hasbunallahu wani'imal wakeel"_cikin tsoro ya soma dube-dube sai motsi yake ji tare da alamun tafiya yai ta maza ya duro daga kan gadon jikiinsa yana rawa tamkar mazari.Kai tsaye band'aki ya shiga ya d'auro alwala ya tayar da sallah.
Ya jima zaune kan dardumar yana kaiwa ubangiji kukansa, bai tashi ba sai misalin biyu da rabi zuciyarsa ta yi sanyi sossai ya kwanta.
Washegari da safe dukkansu suka hadu a wajan break, gwanin sha'awa Yasiraht ta kallesu daya bayan daya ta lumshe ido a filli ta furta"gaskiya Daddy i really miss u".Dariya suka sa mata su duka Yasar cikin zolaya yace"rayuwar kwaki da k'arago".Cikin shagwa6a ta cunno baki"Daddy kaji shi ko?" "Kyaleshi diyar Daddy tuzurun kawai"dariya sukai baki daya.
Bayan sun gama bresk fast (karin safe) Yasiraht ta langa6e kai tace"Daddy inason zuwa shooping kace Yah Yas ya kaini",suna hada ido ta kanne ido ta daga gira "yes kai" ta furta da tsona. Ya gimtse fuska"kin raina ni ko? " "Yo raini kuma na nawa? ".Ta fad'a tana yi masa gwalo "to ai saiki nemi mai kai ki"saurin zubewa tayi "pls Yayana na daina"dariya sukai mata yace "ki bari sai zuwa yamma".Da haka sukai sallama Daddy da Yasar suka wuce aiki, Yasmin aka tafi kaita makaranta Hajiya ta nufi sashinta haka ma Yasiraht.
Shiru tana zaune kad'aici ya adabeta, ta juya can ta juya can.Tana zaune taga bangon d'akinta ya dare ta mik'e a tsorace ya cigaba da darewa wata irin fadace ta bayyana mai cike da kayan alatu a tsakiyarta wata kijera ce bisa dukkan alamu ta gwal ce. Gefanta Maza da Mata ne jingim sun kai su d'ari sun zagayeta cikin shiga wasu kaya jajjaye.Gaba d'aya kansu s sunkuye alamun girmamawa kujerar tsakiyar babu kowa,daga wani bango wani kyakkyawan saurayi ya bayyana dogo mai tsayi da cikar fadin k'irji.Fuskarsa doguwa yana da manyan idanu, hannu ya bud'emata "munai miki barka da zuwa Yasiraht zoki zauna"kawai saita samu kanta da rashin musu wa umarninsa gadan-gadan ta nufi fadar......... wata giggitaciyar k'ara aka saki daga gefansu hakan ya dakatar da'ita saboda razanar abinda ta gani.
Sanah
Rash
ku biyo mu
[8/8, 8:44 PM] Sanah S Isma'il Matazu: 
💀 *YAR MAFIYA...*💀
Cikin firgita taci gaba da kallon fuskarta ba kowa bace face Najwa, hankalinta ya dugunzuma saboda kalamanta dake ratsa dodon kunnuwanta. 
"Walahi Samir baka isa ba, ni zaka yaudara? Dama saboda haka ka matsa in jawota k'ungiya? Kasani kasan halina sarai zan iya kauda Yasiraht a kan ka walahi bana jurar had'aka da wata......."bata k'arasa ba ya kaimata wata muguwar shak'a a zafaffe.
"Ni zakiyiwa iskanci? Kinja mana asara, kinsani sarai dodon tsafi yace mudun ta hau kujerar nan matsayinmu zai hau-hawa a ko'ina saboda baki da mutunci muna dab da cika burinmu na samun *MATSAFIYA* ki wargaza mana shiri".Kakari ta shiga yi aka rasa wanda zai karb'eta.........Turo k'ofar d'akin ya katse hotan komai, Yasiraht ta soma waige-waige karaf suka had'a ido da Uwani mai aikinsu murmushi tayi.....sai dai murmushinta ya kashe sakammakon jiyo sautin muryar Samir a kunnuwanta"Sarauniya ki bamu wannan"ji tayi bakinta ya furta"na baku".Daga nan dif! Sautin ya d'auke Uwani ta ajiye mata abinci ta fita. Shudewar mintuna goma ta soma jiyo koke-koke cikin gidan,da gudu tai waje zuwa sashin da ta jiyo kukan.
Abinda ta gani ya girgizata da sauri ta juya ta koma d'akinta tana shiga ta kulle d'akin nan hoton fadan da ta gani d'azu ya bayyana a gabanta har yanzu suna kan Uwani mai aiki tana ihu suna yankan naman jikinta jiniko wani d'an rami yake taruwa a ciki sai da ya gama taruwa kamar wani iji ko zance cikin salon Sihiri da *TSAFI* wani hanya k'arami ya fito nan jinin uwani ya bi ramin har ya isa zuwa gun wani irin mumunan halitta mai jan ido sannan cikin kwayan idon ruwan ganye yana da dogayen hak'ora jikinsa ba fata sai wani gashi mai tsayi da bai gama rufe jikinba da inda muke muna hango yanda ya ke sanya harshensa yana shan jinin nan.
Yasiraht ganin haka kuma gata a tana kalon ta cikin mutanen sai ta soma ja da baya Samar ne cikin yananyin da ni kaina bazan iya gane ko me ke k'unshe a fuskansa ba ya soma mik'o mata hannu yana kad'a kai alamar k'arta gudu itakuma tana ja da baya al'amari da yaba ma kowa na gun mamaki don Samar yana matuk'ar ji da kansa ga shikuma d'an *SARKIN MATSAFA*  wanda duk ya ke cikin gunyiyan daga maza har mata bai sakar musu fiska bare har suga murmushinsa.
Kafin Yasiraht ta fita har ya tako yazo ida take hannu ya mik'o mata bata iya yin masa musu ba sai ta kama hannu al'amarin da ya ba ma kowa nacikin gurin mamaki, sai da ya janyota k'usa da shi yana kallon kwayar idonta suna iya jin numfashin juna Samar ya kasa d'auke idonsa gada gareta itama haka duk sun shagala da kalon junansu kalon mai d'auke da sak'onni kala-kala a cikinta.
Najwa da ta tsaya zuciyarta na matuk'ar tafarfasa wannan wani irin abu Samar keyi ma Yasiraht duk irin abunda nake masa ai yaci ya gane irin k'aunar da nake masa amma ko sassauta murya bai tab'a min ba irin yanda yayi ma Yasiraht yau tabbas dole na d'au mataki bazai yiwu ta shiga zuciyar da na dad'e ina muradi.
Cikin zafin nama tare da sihiri ta bi iska ta iso gaban su da sauri ta finciko Yasiraht tare da shiga tsakaninsu tana wani irin kalo ma d'auke da alamomin tambaya Samar da har zai yi magana ko me ya tuna sai ya nuna kujeransa da yatsa nan tabi iska ta iso gabansa tayi kasa-kasa tukun cikin isa da mulki ya taka kan matakalar ya zauna a kan kujeran tukun ta tashi da shi sama ta tsaya a sararin samaniya.
Hajiya Nafisatu ganin dare yayi gashi Uwani zata kawo mata ruwan zafi da sauri taje kitchen (madafi) taga ko ruwan bata d'aura ba ga kuma abincinta bata ci ba, gass ta kunna ta d'aura ruwa sai da yayi zafi ta juye ta d'auko zata tafi wata zuciya ta ce"anya Uwani yau lafiya tunda muke da ita bata tab'a mana haka ba barin kai ruwan nan inzo in duba ta.
'Dakin Uwani ta nufa nan ta sameta a k'asa dai-dai k'ofar fita a kwance a k'asa idonunta a sama duk sun kafe, ganin haka ba k'aramin razana tayi ba ta kira sunanta Uwani! Uwani!! Uwani!!! Ido ta zaro tare da d'aga hannuta ta ga ya saki da sauri ta juya tayi d'akin Abba da gudu ta shiga tana fad'in "Alhaji Uwani! uwani!!". Sam bata cikin hayyacinta sai da ya rik'ota ya soma mata addu'a ya ce"lafiya me ya samu Uwanin?.
Hannuta ya kama suka nufi d'akin yana zuwa ya ganta nan ya d'aga hannuta ya ga ya saki nan Abba ya saki salati don ya gane Uwani ta rigamu gidan gaskiya hannu yasa ya rufe mata idanunta tare da d'auko zanin ya rufe ta ya gyara ta a gefe d'aya hannu Hajiya Nafisat ya kama yana bata kalamai masu dad'i da kwantar da hankali ya kai ta d'aki ya fita ya kira Yasar ya masa bayani tare sukaje aka kira Limamin unguwansu tare da wasu makwabta, a dare aka nimi dangin Uwani aka suturta ta tayi kwanan keso.
Yasiraht sai da safe da ta tashi taga gidansu a cike nan ta tambayi hajiyarta me ke faruwa nan ta fad'a mata take taji wani zufa na keto mata ta razana sosai wato jiya ba mafarki takeyi ba asai da gaske abunda jiya ta gani a bacci ya faru nan ta fara hawaye duk wani tsoro tafaraji a haka aka fita da Uwani aka mata sallah aka kai ta gidanta na gaskiya Allahi Akbar rayuwa kenan.
Kwanakin Yasiraht uku a gida gaba d'aya hankalinta ya soma tashi saboda mafarkan da take yi tare da tsoratata da ake yi. Kwata-kwata yanzu kallon mudubi ya gaggareta saboda zahiri in ta kalli mudubi mugayan gane-gane take yi.Ahaka suka cinye kwanakin su suka koma makaranta,sai dai tunda suka koma ta fuskanci canje-canje daga gun Najwa sossai ko harkarta bata shiga balle magana me tsayi ta had'asu.
Kwatsam ranar Juma'a da azahar sun dawo masallaci, taga shigowar k'awayan Najwa su uku bayan su Najwa ce d'aya bayan d'aya ta kallesu Shany ce 'yar asalin garin ebira sai Merry ita kuma Ibadan sai kuma Emeka 'yar Undo bata tanka ba ta cigaba da bibbiyar littafin dake hannunta fizgar littafin yasata d'agowa kafin tai magana Emeka ta tsinkamata mari.Najwa tai murmushi ta jin-jina hannu alamun jin dad'i Yasiraht kasa magana ta yi suka kad'a kai sukai waje, ranar yini ta yi sukukku ko karbar abinci bata je ba.
Wata sabuwa sai Najwa ta tsiri sata aiki hakan yana bata mamaki matuk'a,amma babu yadda zatai ta fahimci hata Malamansu shakarta suke.Kwatsam rana nan tana zaune a labry tana karatu, ta jiyo shewar su Najwa can taji sautin Emeka"ke wai ya kuka yi da prince a kan tsamin yarinyar can?"."Hmm! Kedai bari sisty Samar na neman had'awa kowa jalalla walahi zanyi sanadin tona asirin k'ungiya saboda Yasiraht, shekaruna nawa tare da shi han samu matsayin da yake son d'orata ba sai ita daga zuwanta. Wace wuya ce banci ba wajan kawota duk zatona zan samu matsayin da take kai amma shi ne zai rainamun wayau? ".
"Laifin kine".
Cewar Shany, cikin k'ufula ta furta"kamar ya laifina ban gane ba walahi? ".
"Hmm! Nagaya miki kawai mugama dashi kin wani tsaya ja mana rai, wai ke so ai saiki ci so bagara kui biyu babu ba ko kigama da Yasiraht d'in".
"Keeeee!  Dakata in gama da Samar? Wa zan kama? " Ta fad'a a zafaffe itama cikin zafinta ta maida martani. 
"Ki kama sabon zuwa".
Kyakkyawan mari ta shimfid'amata, ta cigaba"saboda baki da mutunci Samar din zan gama da shi? Kin san waye shi a gareni? ".
"Waye fa Najwa?  Banda wanda ya samu a hanyar banza ya cuccuce mu ko kin manta Samar ne yasa kika bada jinnin mahaifanki duka biyun ga doddon tsafi? Kin manta shi yasa kika rasa masoyinki na gaskiya kika bada k'annanki har uku ki gayamun yanzu wa kike dashi a danginki da zaki nuna matsayin jininki duk Samar ya k'arar da su.Shi ne kike so itama Yasiraht ta fad'a, to kisani ada ina tare dake,amma a yanzu nayi d'amarar janye muku zan kasance tare da Yasiraht kun yi galabar kawota cikin ku amma sai nayi sanadin da zata zame muku masifa dalilin marin da kikai mun bana yafiya".
Fuuuu! Tabar wajan, kan Yasiraht yai nauyi tanasan gasgata batun Emeka ta kasa, kawai saita shasshantar da batun ta cigaba da abinda take.Kamar almara Samar ya bayyana yana murmushi,cikin tsoro ta soma da baya amma suna hada ido sai taji wani abu na fuzgar zuciyarta zuwa gareshi matsawa ta
Matsawa tayi kusa dashi Samar kalon yake mata mai cike da so da kauna hannusa ya kalli wani zobuna guda uku a jere manya dasu da kuma rubutu a jiki ta baya kuma alamar kan mutum ne wannan zobe ya danna nan take wani irin hallita ya bayyana a gaban sa tare da rusunawa ya ce"ya shugabana ban umurni na bi". Murmushi Samar yayi cikin k'asaita da mulki ya ce"aljani d'an duguzu ina so ka kai mu dajin k'are dugunka zan huta a gun".
Kafin ka ce mai ta ke gurin ya gauraye da iska nan take Yasiraht ta fara kakkarwa da tsoro nan wata dadduma ta bayyana tare da matasai na alfarma ko da ta duba ta gani d'an duguzu ne ya ke rik'e da dadduman a kansa nan tsoro ya k'ara kamata. Samar ne ya kama hannuta kaman walkiya suka hau kan dadduman nan taga su tsaga bango suka fito gashi tana gani suka wuce mutane amma da alaman su basa ganin su a hankali suka haura sararin samaniya sai keta hazo sukeyi suna tafiya cikin kwanciyar hankali.
Yasiaht ta rasa mai yasa in Samar ya mata magana bata iya masa musu kuma in ta kalli kwayan idonsa yana mata kwarjini bana wasa ba a han kali ta sauk'e sassanya anjiyar zuciya.
Najwa da ta nufo library (gurin karatu) taga wulgawan su Samar nan take wani bak'in ciki ya lulub'eta ga mutane a gun bare ta tanza hallita ta bisu da sauri ta nufi cikin library a girgiza ta dawo wata tsun-tsuwa ta fito daga library ta bisu zuciyar ta na mata k'una sai sake-saken wani irin abu zatayi ma Yasiraht.
Samar suna zuwa dajin nan dadduman ya sauk'o dai-dai bakin ruwa suka sauk'a wani abun ban mamaki ga manyan namun daji suna shawagi a gun ba wanda ya kulasu ko ta inda suke basa bi. Samar ne yasake murza zobe nan wata mata fara da farare kaya ta bayyana ba'a ganin k'afarta sabida fararen kaya ya rufe k’afafunta, ta rusuna ta ce"Ranka shi dad'e 'Dan Sarkin Matsafa jikan matsafa mai kake buk'ata a maka sai da ya d'au lokaci kafin ya ya ce"kayan marmari nake buk'ata". Kafin kace me  wani tire na alfarma kamar na zinari sai kyalli yakeyi tare da d'auke ido kayan mar-mari aciki irinsu Tuffa(Apple), Inabi Ayaba, Abarba, d.s.s.
Yasiraht sam tak'i ci Samar ne ya ce"bazaki ci ba ko sai na baki ya d'auko yankake tufa zai sa mata a baki kawai suka ga wani irin abu ya tun k'aro su da gudu ya buge Yasirah ta fad'i k'asa, nan abun ya fito da wani tsini da niyar zuwa ya cakka ma Yasiraht a cikinta, cikin sauri Samar ya bud'e hannusa sai ga wani sanda ya fito da sauri ya nuna wannan tsun-tsuwar sai ga Najwa ta dawo halittanta na asali ta fad'i a gun tana mai da nufashi. Cike da mamaki Samar ke kallonta a hankali ya tako zuwa inda Yasiraht take ya d'agata tukun ya kalli Najwa nan yaji wani haushinta ya kamasa a hankali yasoma takawa zuwa gun Najwa cikin fushi.
         15
Cikin fushi yake nunata da yatsa, "wato Najwa bakya jin magana ko?  Ina kaucewa sab'amiki kina k'ok'arin k'untatamin to walahi zanyi maganinki".Wata giggitaciyar dariya ta saki, tana hucci mai zafi ta dubeshi. 
"Samar ni zaka wulakanta saboda ina bibbiyarka?Walahi kabani mamaki k'warai da gaske, zan nuna maka sharin mace sai kayi nadamar cin amanata".....bata k'arasa ba ya nunata da hannu tuni wani sirririn haske kore ya fito ta tsintsiyar hannunsa ya daki fuskarta take ta saki wata giggitaciyar k'ara data kid'ima dajin.Namun dajin suka dinga gudu suna neman mafaka,yaraf ta zube k'asa babu numfashi.'Daukar Yasiraht ta yi suka bar wajan.
Cikin tsananin gudu suka dinga keta dazzuzuka, a hankali ya sauketa cikin labry d'in ya kama yatsanta yasa mata wani zobe.Zoban yana da tsananin haske in ka kalleshi, jikinsa tambarin kan skelaton ne a jiki daga tsakiya an masa ado da gwal yanata k'yali b'at ya b'ace.A hankali idonta ya soma washewa ta saki ajiyar zuciya kanta yai nauyi sossai a jigace ta nufi hostel saboda gajiya.Turus ta tsaya lokacin data fito, sakammakon ganin d'alibai dandazo guda sun zagaye Najwa cikin galabaitaccen yanayi.
A sanyayye ta karasa wajan tana tambayar abinda ya faru, wata muguwar shak'a Shany ta kawomata wani shock da hannunta ya yi yasa ta sakin Yasiraht bata shirya ba tai baya tana muzurai.Ita dai Yasiraht rakata ta yi da idanu zuciyarta k'war cike mamakin ganin Najwa a wannan yanayi.Take abinda ya faru ya dawo mata, kanta ya sara ras!  Ta dafe ta wuce area d'insu jikinta na rawa.Emeka dake gefe ta kwashe da dariya, cikin gurbataciyyar hausarta tace "yaro bai san wuta ba".
Wani rikitaccen kallo Shany ta aika mata, a daddafe ta wuce hostel  tana zuwa ta zube kan gadonta tana numfarfashi.Ta dafe kanta da yake juya mata sossai, a haka ta yini kwance.Najwa sai da tai kwana biyar kwance sannan ta dawo hayyacinta.
Tun daga lokacin wata gaba ta k'ulu tsakanin Najwa da Yasiraht, kwata-kwata basa ga miciji idan hanya ta had'asu sun dinga hararre-hararre kenan.Abinda yake tada hankalin Najwa yadda duk yadda taso cutar da Yasiraht sai zoban hannunta ya zamo shamaki wajan afkuwar hakan, haka take hakura kiri-kiri kwatsam aka nemesu taron gaggawa a k'ungiya.
Harabar wajan cike take da manyan motoci ababban kalo, abin sai wanda ya gani an kawata fillin ra jajjayan furani da bak'ak'k'e komai na wajan ja da bak'i ne har  kayan jikinsu.A hankali aka soma darewa ana bashi waje yana rik'e da hannunta har suka samu waje suka zauna.Nan aka saki kida sossai taro ya soma gudana, an gama gabatarwa an ci an sha Najwa da Shany na gefe suna kus-kus.Can Samar ya mike ya gabatar da jawabin godiya ga mahallata taron,ya juya yana murmushi ya kali Yasiraht hannunsa ya mika sama yana karanta wasu dalamusan tsafi take wasu kwarre guda biyu suka bayyana kan hannunsa.
Cikin kasaita ya tsareta da ido"karbi kisha" jikinta ko ina rawa yake take ta kafa kai ta hausha wajan ya rude da shewa"kinzama sarauniya!  Kinzama sarauniya!!  Kin zama sarauniya!!! ".Wata giggitaciyar kara Najwa  ta saki tai kanta da wata takobi mai tsananin haske, take Samar ya dakawa Yasiraht tsawa itama tai kanta tana shafa zobanta takobi ta bayyana irin ta Najwa nan da nan wajan ya hautsine sai karar k'arafa kake ji na tashi can Yasiraht tai nasarar yankar Najwa a gefan wuya take ta kwala kara tai lau zata fado kasa. Caraf Samar ya rikota Yasiraht ta diro kan kafafunta tana murmushi ganin Najwa a hannun Samar yasa ta jefa masa wani shu umin kallo ta danna zobanta b'at ta b'ace....
*16*
Ganin Najwa a hannu Samar yasa Yasiraht ta sakar masa wani shu umin kallo ta b'ace, bata bayya na a ko ina ba sai a bayan hostel d'insu  gindin bishiyar d'aurawa ta zauna ta had'a kai da gwiwa tana kuka mai tsuna zuciya sam ta rasa mai yasa take jin wani abu game da Samar duk lokacin da ta gansa da Najwa sai ta ji zuciyarta na mata zafi. Labb'an bakinta ta ciza a fili ta ce"Najwa ni Yasiraht sai na koya miki hankali duk wani hanyan da zanbi na nuna muku kwarewa ta sai nabi kuma sai na fitini kowa a gun sai na zama mai bada umarni abi nice nan zan dawo mai jiran kuren Samar". Murmushin mugunta ta saki sai kuma taci gaba da kuka.
Najwa tana far-fad'owa ta ganta hannu Samar sai taji sanyi a zuciyarta tazo juyawa taji wuyanta ya rik'e sai da ta saki k'ara kad'an Samar cikin sauri ya k'ara rik'e ta tukun ya fara wasu surkulle sai ga kwarya ya bayyana a gabansa nan take ya sanya hannusa ya d'ebi garin magani ya shafa mata tare da wasu sirutai wanda ba musan ko na miye ba take waje ya goge kamar ba ta tab'a jin ciwo ba Najwa sai murmushi takeyi fiskanta d'auke da annuri yau tana jin wani sanyin dad'i ya mamayeta wai ita ce a hannu Samar lalle yau jin kanta take tafi kowa, cikin yanga ta mik'e tare da zuwa kusa da Samar ta tsaya sai da ya aika tama da kalon mai d'auke da tuhuma kafin ya ce"Najwa mai yasa bakiji na ce ki fita a hark'an Yasiraht amma kin k'i ji kinga irin ta nan ko in baki mai da hankali ba zata fara mayar miki da martani kaman yanda tayi yau". Najwa ko ajikinta bata kuma ce da shi k'ala ba sai murmushin da takeyi nan ran Samar ya k'ara b'aci take ya bada umarni da a watse a mitin d'in yana gama fad'a ya bace...
Bai bayya na ko ina ba sai gun da Yasiraht take ta had'a kai da gwiwa tana kuka a hankali Samar yazo ya dafa ta a hankali Yasiraht ta d'ago idonta tab da hawaye cikin sanyin murya Samar ya ce" Yasiraht ki dai na kuka ban son ganin hawayenki na zuba ko kad'an". Cikin fushi ta d'ago dara-daran idonta da sukayi ja ta sauk'esu a kansa da niyar masifa amma sai me kwarjininsa yasa ta fasa Samar ne ya sanya hannusa ya share mata hawaye ya rik'o hannuta suka mik'e tsaye suka nufi hanyan hostel.
Sai da ya kai ta har d'aki ya rarrasheta suna tad'i har tana dariya kafin ya tafi, tun daga wannan rana Yasiraht ta soma canza salo don Najwa bata isa ta tab'ata ba ta share ga salon tsafi da sihirin da Yasiraht takeyi abin har na ba ma Najwa tsoro kuma ko a gun mitin nan danan zakaji ta kawo mutane hakan yasa suka k'ara girmamata. - ISMAIL SANI
Ku biyo mu

0 comments:

Post a Comment