Tuesday, 6 February 2018

ALJANA CE KO MUTUM 1-10

ALJANA CE KO MUTUM Page 1-10
.
Na Ummu Ruman
..
kwance yake saman makeken katifarsa dataji lallausar zanin gado' sai juyi yake ya kasa bacci,  tunani yake ina zai sake ganinta? ina zai sake tozali da wannan kyakkyawar fuskar dake hana zuciyarsa sukuni dare da rana? wani irin haske yaziyarci idanuwansa, wanda yayi sanadiyyar saurin runtse idanun don hasken yayi yawa, jiyayi ance  bude idanunka mosoyina, gani nazo gareka  don insanyaya maka zuciya tareda sanyata nishadi" saurin bude idanunsa yayi sukayi ido hudu da kyakkyawar fuskarta, yayi saurin tashi zaune cikeda jindad'in ganinta'  don Allah kada kisake tafiya kibarni, ina matukar sonki, inason kasancewa tare dake' inason mukasance a inuwa guda (aure)
               
               tace" kayi hakuri mosoyina inasonka, amman  banajin zamu iyayin aure yanxu kusa' saboda wasu dalilai' na farko baka sanni ba' baka san koni  wacece ba, akwai babban hatsarin dake tattare da arayuwata'  banason wani mummunar abu yafaru da rayuwarka' hawaye yaji ya siraro a idanunsa, ya dafe saitin zuciyarsa dake baraxanar faso kirjinsa sbd tsabar sonta dayakeji' wani irin had'arine? wani irin had'arine arayuwarki dazai hana mana mana kasancewa da juna?
  jiyayi ance  cikin tsawa ina ruwanka da rayuwarta, inaso  kafita hanyar wannan yarinya' inba haka ba rayuwarka zata salwanta, ke kuma yau saikin d'and'ani azaban da baki taba sha ba arayuwarki, ba an hanaki zuwa wajan wannan mutumin ba? afusace matar ta fizgo hannunta 6at suka 6ace'
wani irin zazzafan hawaye ya gangaro a kuncinsa" meyasa zuciyata zatamin haka? meyasa zata fad'a soyayya da wacce ba jinsinmu guda ba? meyasa zataso wacce ba mutum ba, ohh Allah"  hannunsa ya d'aga sama yana cewa ya Allah ka kawo min agaji arayuwata' kacire min son abunda bazai ta6a yiwwa ba. tashi yayi yaje ya dauro alwala don gabatar da sallan raka'atanin fijir, kasan cewar ansoma kiraye2n sallah farko.
              bayan ya dawo daga masallaci  ya dauko book da kanwarsa ta kawo masa jiya  daddare don yayi mata assignment, yana gamawa  ya kwanta bacci har 9am na safe *NAWWAR* bai tashiba.
                  mami hafsat ce zaune a parlo tana breakfast, yar autar tace tashigo me suna *mimi* zama tayi kusada maminta tareda gaisheta"  mami hafsa tace autana har kin tashi baccin? eh mami nah natashi, gashi duk jikina ciwo yake min wlhy, ayya sannu ga abincinki can keda yayanki idan kikaci sai kisha magani" yau naga shima bai fito da wuri ba, ko lafiya?jeki ki duboshi, to mami, ta tashi ta nufi hanyar dakin shi, abakin kofa sukaci karo.

.
Abakin kofa suka ci karo shima yafito cikin shiri, yace a'a autar mami ya akayi? lafiya lau hamma nah, mami ce tace inxo in dubaka, yau baka tashi da wuri ba?
       eh wallahi assingment din kine ya hanamin bacci da wuri, saboda wannan *nahawun* yad'an bani wahala, kai hamma" kai da ka haddace nahawul wadi shine zai baka wahala? nikam ban yarda ba? dariya yayi yace autar mu baki da dama.
           suka karasa wajen *mami hafsah*  duk suka zauna kusa da ita, *Nawwar* yagaisar da maminsa cikin girmamawa, ta amsa tare da cewa nawwar yau lafiya baka tashi da wuri ba? ko bakajin dadin jikin ne? a'a mami lafiyata kalau.
             kawai assignment din wannan autar naki ce ya hanani bacci da wuri, mami tace dafatan dai kagama mata? eh nagama, cikin murna mimi tace yauwa hamma nah nagode sosai, kace yau ni zanyi ta d'aya a ajinmu, murmushi yayi yace aah nibance ba" kika sani ma koban rbt dai2 ba? fuska ta yamutsa cikin shagwa6a tace mami kina jinsa koh? wlhy kabari aka sakamin ziro saina gayama abba, dan nasan ka iya nahawu sosai' idan naci xiro nasan kana sane kamin' kuma mami kicema hamma yadaina min fatar cin zero' ta karashe mgnr tana turo baki"   dariya sukayi gaba d'aya
         mami  tace rabudashi autana jeki kawo muku breakfast kuyi kuci kutafi lkc na wucewa, to"
mami ta gyara zamanta da kyau ta kalli  Nawwar tace kaima  yakamata ace zuwa yanxu kafitar da matar aure, tun kafin baban ku yaza6o maka matar da bakaso, tunda ya dade yana baka lkc.
            wani irin faduwa gabanshi yayi,  sai gumi yasoma hadawa  a goshinsa' yayin da zuciyarshi ke har bawa, saboda tuno abar sonshi, shiru yayi"mami sai magana take amma kamar hankalinshi bai jikin shi, data gama maganar ne tayi shiru ta zuba masa ido, shi bai ma san tayi shirun ba.
            hankalin shi gaba daya ya tafiga tuno masoyiyarsa' kafad'arsa  mami hafsa ta dafa , yayi saurin sauke ajiyar zuciya, ya dago kai ya kalleta, idanunshi har sun kada sunyi launin "JA" , mami hafsa duk ta tsorata da ganin yadda yanayinshi ya sauya cikin dan lkc, cikin damuwa tace lafiya *nawwar*? daga maganar aure har yanayinka yacanza, shin bakada lafiya ne ko aurenne baka so?  ajiyar zuciya ya sauke tare da karnto addu'ar nutsuwa, a hankali ya riko hannun mami dake kan kafad'arsa' yace wlhy mami nikam tsinci kaina a cikin tashin hankali da  damuwa aduk lokacin da akamin maganar aure, sai inji zuciyata tana suya, cikin raunanniyar murya yace mami nah please kitayani da addu'a babu wacce tafi cancanta na fadama damuwata  sama dake,
              akwai wacce  nake matukar so tana yawan zuwa min a mafarki da zahiri sai dai kuma ba mutum bace, mami tazaro ido waje, yace wallahi mami ina tsananin sonta jinake bazan iya rayuwa  babu ita ba.
            dayar hannunsa  yasa ya goge hawayen  daya gangaro a idanunshi, sosai mami ta tausaya ma danta, itama tuni hawaye yaciko a idanunta' tace wannan wace irin masiface? ina nata6ajin anyi syy  tsakanin *aljana* da *mutum* ta jinjina kanta tace Allah mai iko.
           *nawwar* kaci gaba da addu'a insha Allahu nima zantayaka dayin addu'an Allah ubangiji yacire maka son abunda bazaiyu arayuwarka ba, amma gaskiya naji tsoro, ba jinsin mu daya ba, meyasa zasu  Shiga rayuwar d'ana?  meyasa ita wannan aljanar tazabi tayi soyayya da kai alhalin tasan kai ba jinsin su bane? gsky bata kyauta mana ba, insha Allahu addu'ah itace magani, kaima nasan kayi sakaci da addu'ar ne shiyasa'
             mimi da ta dade da kawo musu breakfast tazauna  tanajin abinda mami da hammanta suke tattaunawa,itama ta tausaya masa kuma taji mamakin al'amarin,  tace *hamma* nah kamar yadda mami tace maka addu'a itace magani, toh ita zaka dingayi nima zantayaka kaji hamma nawwar,  murmushi yayi yace nagode autar mami.
          yaji dadin yadda mahaifiyarsa da kanwarsa suka fahimceshi tareda kwantar masa da hankali, da kuma nuna masa muhimmancin addu'a"  nan sukayi breakfast dinsu, bayan sun gama mimi tayi saurin saka  kayan islamiyarta don nawwar ya sauketa a makarantarsu, tare suka fito farfajiyar gdan mami hafsa tarako su tana daga masu hannu har suka fita gidan.

.
nawwar ya ijye Mimi a islamiya" shi kuma Yakama hanyar zuwa hospital dinshi, yana tafe yana tunanin maganar da sukayi da Mami,   yana cikin tunani wani abu ya diro mishi kan motar shi, yayi saurin J'an burki" tare da kifa kanshi kan sitiyarin motan  yana maida numfashi, dago kan dazaiyi " yayi ido hudu da wannan matar da dauke mashi abar sonshi lokacin data zo mai, yayi saurin zabura tare da karanto *innalillahi* *wa'inna* *ilaihiraji'un*, da sauri ya rufe glass din motarsa" gani yake kamar zata shigo.
.
         itako tana tsaye tana kallon abunda yake yi, tasaki wani irin gitattaccen dariya, tare da nunasa da dan yasa" cikin babban murya, tace *Nawwar* nazo maka gargadi ne kafita Daga rayuwar *sameeratun* *nawwara* idan kuma ba haka ba , kai da'ita zaku fuskanci" mummunan tashin hankali arayuwar Ku,   don baza mu kyale kowani bil  adama ba yashiga cikin rayuwar mu.
          yanxu haka *sameeratun* *nawwara* tana can tana fuskantar mummunar hukunci, saboda tasaba mawa dokar mu, *nawwar* yayi saurin cewa don Allah Ku kyaleta karku" mata komai, ta daka mashi tsawa  tare da cewa, kai har ka isa kafada mana abunda zamuyi, ina kara gargadin ka" akaro na biyu, Daga fita Daga cikin rayuwar da bata shafe ka ba, Idan kunne yaji Gangar jiki yatsira.
           zai yi magana kenan wuf ta bace mai, ya sauke ajiyar zuciya tare da hawaye mai radadi dake gangaro mai, zuciyarshi sai har bawa take kamar zata fito, sboda tsananin zafin dayake mai.
           jikinshi duk ya mutum kamar Wanda akamai duka,  dakyar ya iya Jan mortar sa zuwa hospital" lokacin dayayi parking din mortar sa alokacin abokinsa shima yayi parking din nasa" nawwar ya bude mortar zai fito yakasa ganin halin dayake ne yasa abokinshi me suna   awwal" ya karaso wajan da Sauri cikin kidimewa, yana fadin nawwara lafiya naganka haka? meke damunka? cikin karfin hali nawwar ke nuna mawa awwal zuciyar alamun ita ke mai zafi, amma yakasa magana" awwal ne ya taimaka mashi suka karasa cikin hospital din.
          dayake shi doctor be a fannin zuciya, ya kwantar dashi kan gadon sake office dinsa ya dubasa da kyau, tare dayi mashi allura da bashi magani" har bacci yayi awon gaba dashi"  awwal ya zauna shiru yana tunanin wani irin damuwa ne abokinshi yake ciki" da har ciwon zuciya takamashi, Allah sarki nawwar, Allah ya yaye maka koma menene.
          
     ***************
tun lokacin da sameeratun nawwara tabar gun nawwara ake gallaza mata azaba aduniyar su ta aljanu" don ta taka dokan da aka mata, daure take jikin wani  bishiya ta tsafi duk kaca ne jikinta, yayin da wasu irin halittu ke jibgarta da bulalan wuta, tana ihu  saboda tsananin azaban zafi.
       gefe daya kuma wani mutum ne azaune  cikin kayataccen kijera ta alfarma irinta sarauta da alamu shine shugaba" sai dariyan keta yakeyi, irinta ta mugaye.
            yana kallon yadda ake wahalar da sameeratun nawwara, saida da ya bari tasha wahala sosai har bata motsi sannan yace adakata"  ya karaso wajanta dai dai fuskarta yasa hannunshi yadago fuskarta, yace haryanxu, kina cikin bakanki na kin" aure na, tayi karfin hali tace eh, bazan aureka ba, ba zan aureka ba, koda zan rasa raina ne , kamar yadda " kuka rabani da farin cikin to kuma har abada bazaku taba samun naku farin cikin ba, don nawwar shine mijina, na har abada,  *Ambar* yayi saurin ja da baya yana cewa,   cewa karyanki ne kija dani sameeratun nawwara, sai kinzama tawa, banga wani bil adaman daya isa yashiga gonata ba , mahaifinki shi yaja miki sameeratun nawwara" ni nan *ambar* sai na mallake ki, duk cikin tsawa yake maganar nan,   kuma sai naga bayan wannan nawwar din, tanaji ya ambato nawwar dinta , itama cikin Daga murya tace karya kake ambar , indai INA da sauran numfashi baka Isa ka halaka nawwar ba, don yafi karfinka"  ji tayi an wurgo mata wani katon dutse dai dai saitin bakinta" har Saida hakorarta yafadi, ta dafe gun tare da juyowa" taga wanene , ido hudu sukayi da kanwar ambar, me suna *kiyara* tana dariyar mugunta.
           cikin tsawa tace baki da hankali kike fada mawa shugaban mu magana " saina koya miki darasi, cikin iska tazo da gudu zata shake" wuyan sameratun nawwara, sai taji ansha ke nata wuyan, bataganin Wanda, yashake ta" saboda wani irin guguwar  iska ce" ke tashi, *kiyar* da *ambar* sunshiga rudu saka makon ganin wannan halittar,  cikin yaransu wannan halittar take cewa " duk da na mutu baza kubarni na huta ba, sai kun binci koni.

.

duk dana mutu ma bazaKu barni na huta ba? sai kun bincikoni kun hanamin kwanciya cikin natsuwa?, bakin kiyara yafara rawa, cikin rawar murya tace kiyi hakuri sameeratun nawwara  bamu san kina tare da itaba, ambar shima yashiga bata hakuri, cikin daga murya tace" ya isheku haka, meyasa zaku takura ma rayuwar ta? kun manta abunda nace kafin na mutu" kenan baku rike amanar dana barmuku ba? ambar yace a'a ba haka bane, toh inba haka ba meyasa zaku takura rayuwarta? kiyara tace Allah yaja zamanin gimbiya sameearatu, ta taka dokan da aka kafa mata ne shiyasa, soyayya taje tanayi da jinsin bil adama, wanda hakan kinsan yasabawa dokan da aka gindaya mata"  gimbiya sameeratu tayi saurin zabura cikin  kakkauran murya tace soyayya da bil adama, me kukeyi har tafara soyayya da bil adama? tuntuni kuka kasa daukar wani mataki da wuri sai yanxu?, duk cikin fushi da d'aga murya take maganar, nan take ran gimbiya sameeratu ya kara mugun baci, babu abinda ta tsana arayuwarta irin bil adama,  saboda su sukayi ajalinta tabar duniyar su.

*sai agaba zamuji wacece gimbiya sameeratu, kuma menene alakarta da sameeratul nawwara*
.
          ambar ne yayi saurin cewa  kiyara janyo wancan kahon ki busa ma  gimbiya sameeratu" da saurinta ta aikata abunda yace mata, tana busa kahon nan take gimbiya sameeratu tasaki wani irin hargitsatstsan kara mai karfi tare da zuwan guguwa mai karfi, har sai da su ambar suka rike bishiyar dake kusa dasu sbd karfin guguwar zata iya tafiya dasu, zuwa can wajan yayi tsit kamar ba abunda yafaru, ambar ne ya taimakama kiyara data fad'i kasa ta mike.
        dube duben sameeratun nawwara suka somayi, can suka ganota kwance gindin bishiya, suka karasa wajan, kiyara tayi tsafin su suka bace daga wajan.
         haka sameeratun nawwara taci gaba da rayuwar kunci da wahala akan nawwar dinta, duk sanda ta zauna  babu abinda  take sai tunanin rayuwarta tada mai dadi cikin kwanciyar hankali da y'an uwanta, hawayen fuskarta take gogewa  tace kai kajamin wannan rayuwar bakin ciki da tashin hankali ayanzu babana" kaine silar komai ga rayuwata" gashi duk cikin yan uwanta aljanu ita kadai ce musulma, amma sam bata iya ibadan taba, gashi  tanason bautama ubangijinta, sai dai bata san yadda zatayi ba, dalilinda yasa take matukar son hamma nawwar kenan.
  *mafarin haduwar tada hamma nawwar shine*, tashigo duniyar bil adama zagayawa, yakasance ranar sallar su ta EDI can ta hango wani kyakkyawar matashin saurayi yana sallah acikin natsuwa da kwanciyar hankali, bayan ya  idar da sallah, taga ya daga hannayenshi sama yana kwararo kirari ga ubangijinsa" sannan yasoma rokan Allah bukatocinsa na alkhairi, ya kuma kareshi daga  mugun abu.
       duk tana tsaye tana kallonshi yana addu'oi, ya matukar bata sha'awa' tafara tunanin kamar itama ada ta taba irin wannan addu'an, amma kuma meyasa yanxu bata iya ba" wani bangare na zuciyarta yace wani boyayyan sirri ne tattare da rayuwarki, wanda amayar da wannan sirrin bakaramin haddasa bala'i zaiyiba tsakanin bil adama da jinsin aljanu, birne wannan sirrin acikin kokonta zaifi zaman lafiya ga mutane dubu" taja wani dogon numfashi tare da karkata hankalinta gun nawwar daya gama addu'oin shi yakama hanyar gida.
          haka tayi ta bibiyar rayuwar nawwar da yadda yake tafiyar da ibadunshi, anan take son nawwar yasoma mamaye duka sassan jikinta, taji bazata iya rayuwa batare dashi ba" tun daga lokacin zuwa duniyar bil adama yazame ma sameeratun nawwara wajan zuwa,,tun tana zuwa ma nawwar amafarki, har takai da zuwa mai azahiri, anan ne shima yasoma kamuwa da son sameeratun nawwara, yakasa tantan cewan *Aljana ce ko mutum?* kuma   taki bashi dama yamata tambayoyin dazasu gamsar dashi, taki gaya masa wacece ita, yana cikin tsaka mai wuya.
*wannan shine mafarin kulluwar soyayyar su*  

*******************bayan nawwar yatashi daga bacci awwal yasa aka kawo mishi abinci yaci" sannan yabashi magani yasha, Dr awwal ya gyara zama da kyau  ya kalli nawwar, wanda haryanxu tun tashinsa baiyi magana ba.
            Dr awwal yace nawwar meke damunka halan? jin yayi shuru bai amsa masa ba, yakuma cewa wani irin damuwa kasama ranka haka? wanda ke barazana da lfyr ka, duk irin amintar dake tsakaninmu ka kasa fada min matsalarka?, kana wasa da lafiyarka nawwar, gashi ciwon zuciya na kokarin  kama ka, what" sai a sannan yayi mgn, ciwon zuciya fa kace doctor, kai ya d'aga masa alamar tabbatarwa,  mekasa aranka haka? me kanema  karasa, me kakeso wanda baka samu ba? kana so ka kashe kanka ne,  kar ka manta kaifa likita ne, mai kare lafiyar al'umma, to meyasa kai kake wasa da taka lafiyar?
            hawayenda awwal yagani a idanun nawwar shiyasa shi saurarawa ga tambayoyinda yake jero masa, jikinsa yayi sanyi, duk yabi ya rude, yasan ba karamin abu zaiza jarumin abokinsa kuka ba"  haba nawwar meye damuwarka? kafada min ko zan iya taimaka maka," nawwar  ya kalli auwal, yace duk akan *SO* ne awwaal,,Allah ya jarrabi zuciyata dason *AlJANA*  bama  *MUTUM*  ba, a tsorace Dr awwal ya mike tsaye  da sauri, yana yima  nawwar kallon wanda yayi gamo, yace anya nawwar  kana cikin hankalin ka kuwa, kataba ganin Inda akayi soyayya tsakanin aljana da mutum , wlh nawwar kayi gamo, kana bukatar rukiyyar gaggawa, idan ma mafarki  kakeyi,kara ka farka, wannan abu ne  da bazai taba yuwa ba"  kafin nawwar yabashi amsa sai ji sukayi ance , karya kakeyi  awwal sai na auri nawwar  koda zan rasa raina ne wlhy saina aureshi, ae tuni awwal ya kwasa a guje sai bayan kofa yana salati jikinsa na karkarwa"

*.

taci gaba da cewa awwal karka shiga hurumin da ba naka ba, kar kasa nawwar ya gujeni, zuciyata bazata iya jurar rashin saba" awwal ina matukar son nawwar" idan ban sameshi ba banajin zan cigaba da numfashi a duniya!!  shi dai nawwar yananan akan kujera ya zuba maa sameeratun nawwara ido, cikin wani irin matsanancin sonta" dakuma jindad'in ganinta aransa' tabbacin yanxu andaina azabtar da ita kenan, kamar yadda matar nan tafad'a masa"
          awwal da har yanxu yananan a bayan kofa' ji yake kamar kasa ya bude yanitse aciki, saboda tsabagen tsoro' tuni ya rufe idanunshi, cikin dauriya yake cewa   baiwar Allah kiyi hakuri baso nake nashiga rayuwarki ba, ina so ne inceto amini na daga hadarin daya shiga"  sbd zuciyar shi tana dab da bugawa" wanda hakan zai iya rasa ranshi ako wani lokaci ta dalilin sonki"  nawwar ya runtse idanunshi, ya juya da kallonshi wajan awwal, yace aboki na taho ka zauna baza ta maka komai ba!!!   saneeratun nawwara tayi dan murmushi, tace awwal kenan, ni ba muguwa bace kuma banida niyyar cutar da mutane, kasaki jiki dani, kutaimaka ma rayuwata kai da nawwar.
           sai alokacin nawwar yafara magana yace baiwar Allah  me na mikine kike wahalar da rayuwata? kin hana min sukuni"" sonki yana azalzalan zuciyata, ban taba zama nayi second guda ba tare da tunaninki ba,  sannan kuma ban san ke wacece ba? ban san ke wace jinsi bace? shin ke ALJANA ce  ko MUTUM? meyasa kuma kika zabe ni amatsayin nazama abokin rayuwanki? dan Allah don   son annabi ki amsa min tambayoyi na, shima awwal dake mak'e haryanxu a bayan kofa yace kitaimaki abokina please.
       .
  Ta numfasa tace duk naji bayaninku, tabbas baku san koni wacece ba' hakazalika nima bansan nid'in wacece ba" illa abunda nasani shine!!!
        sunana sameeratun nawwara,  nakasan ce aduniyar aljanu' nataso naganni a fadar sarki *GULMIYANU*  tare da ya'yan shi biyu mace da na miji *Ambar* da *kiyara* ambar ne yake son aure na, ni kuma bani sonshi adalilin hakan ne nake fuskantar mummunar azaba"  ban san su waye iyayena ba, kawai nata so naganni awajan  kanwar sarki" *gulmiyanu* wato me suna  *gimbiya *sameeratu*  duk fadin duniyar aljanu ana jin maganar *gimbiya samiratu*   sbd ita take mulki alokacin, amma yanxu ta mutu kuma bil adama su sukayi ajalinta, wanda ban san dalili ba"  nayi nayi binciki afada min ni wacece amma haryanxu ban samu amsata ba"haka rayuwata taci gaba da gudana.
           Akwai watarana da bazan taba mantawa ba ina zaune bakin ruwa ina wasa da tsuntsaye domin suke debe min damuwar dake zuciyata!! sai naji abayana ana min magana juyawan dazanyi, naga wata kyakkyawar matashiya  kuma bafulatana" dauke da kwaryan nono tana min murmushi, tace nawwara ko zan iya zama kusa dake? na daga mata kaina tare dayin murmushi,  kafin tazauna sai naji tace *bismillahi*sannan tazauna na kara kallonta, itama ta kalle ni,  sai naji ta ambato  sunana, tace nawwara, nasan baki sanni ba kuma baki taba ganina ba" amma ni nasanki, nasan asalinki, nasan labarinki me dauke da tausayi.
        kullum in zan wuce ta bakin ruwannan ina ganinki kina cikin damuwa, abun na damuna" shiyasa nace bari yau nazo  nafada miki asalin wacece ke, kuma suwaye iyayenki, kuma infada miki" awani jinsi kika fito , *jinsin aljan* ko *mutum* dannasan shine abinda kikafi damuwa akai" cikin murnata na rungumeta ina cewa nagode yar uwata, tace bakomai, yar fulani taci gaba da cewa amma inaso kimin alkwarin bazaki fada ma kowa idan nafada miki asalinki ba" sbd idan akaji sai ankasheni.
         kuma addinina dana su ba daya bane, ni musulma ce sunana *Ameena Bintu saifullah* , taci gaba da cewa nawwara ke diya ce ga abdullahi da asma'u, kin kasan ce ajinsin _____ sameeratun nawara tayi ajiyar zuciya, awwal yace kinyi shiru baki karasa ba,ta dago idonta wanda yayi jajir ta kallesu, nawwar ya rikice  yace lafiya nawwara" cikin murya mai rauni tace Aminatu bintu saifullah bata karasa fada min ba, naji tasaki wani uban ihu tafadi kasa, juya wan dazanyi naga *kiyara* ce da wasu kartan maza, su suka aikata ma ameena haka, ashe sunji abunda ameena zata fadamin shiyasa suka mata haka"  nashiga rokon kiyara dasu bar azabtar da ameena amma ina, tun ameena tana cewa nawwara ki taimakeni nawwara kitaimake ni, nayi nayi iya kokarina" intaimaki ameena amma ina sun bace da ita!!! nawwar da awwal  wanda hawaye yagama wanke musu fuska nawwar yace yanxu ina suka kai ameena bintu saifullah? tana raye ko bata raye? tace tana raye amma tana cikin wani ma ajiyan mu da ake kulle me lefi, tana shan azaba kala kala,  banta6a mantawa lokacin dana yima ambar wayau ta sigar soyayya daya kaini wajan ameena dana ganta, da kyar ya amince" da mukaje naga duk ta canxa kamanni sbd azaba, kalmar data fadamin shine, tace nawwara kibazama duniyar bil adama kine mi addinin musulunci domin shi zai iya taimaka miki wajan gano asalin jinsin da kike.

0 comments:

Post a Comment