Tuesday, 6 February 2018

BUDURWAR KAUYE Page 51-56 (THE END)

BUDURWAR KAUYE Page 51-55 (The End)
.
Har akayi sallan magrib suna daki dan atare sukayi sallah ma

Sai alokacin Fauziyyah tace ya salam tana dafe goshinta

Papa yace lfy baby yana riqota

Tace sam bakaine kasa namanta da hannatu ba

Waye kuma hannatu? Ya tambayeta dan sam yama manta dawata agidan

Mai aikin da momcy tabamu mana tafada tana kallonsa

Afalo kika bartane ? Aa nakaita dakinta amma nace mata zandawo

To miye aciki tunda tana dakinta kika wani tada hankalinki

Da shagwababbiyar murya tace bafa nata da hankalina bane ko ruwa ban bata bafa gashin har dare yayi baran abinci

Haba babyna kada kidamu aidai tasan kina tare da mijinkine ko yanzun muje ki kai mata juice da akwai nama a kitchen wanda nasa aka sayomun banciba inyaso saina fita na samo mana abinci

Toh shikenan muje tafada tana tashi daga jikinsa

Riqeta ya kumayi yace me babyna zataci

Shiru tadanyi tace umm QUNDUN Bauchi Club zanci da graves

Dadi yaji sosai jin tafadi abinda zataci ba gardama

Amma kuma tabasa dariya yadda tace wai qundu, dan qaramin bakinta yaja yace oh baby kwadayi kenan

Bata rai tayi tace nikam bana kwadayi kuma tunda kace haka nama fasa barin ciba

Cikin sauri yace am so sorry bafa dake nakeba nida little babynanefa

Cikin sangarta tace aidai nadauka dani kake

Yace waneni nace maki mai kwadayi muje yanzun nakawo maki ko shalelena

Atare suka fito kitchen ya riqo mata abinda zata kawoma hannatu har bakin qofarta sannan ya miqa mata tare da manna mata kiss a forehead nata ya fice

Washe gari da kyar ya fita office sai wani nan nan yake da ita har bata gajiya da kallon yadda yake mata hidima

Bayan yafita ma ajima kadan ya kirata awaya yana tambayar ya suke ita da little babynsa

Ita kuwa tai ta zuba masa shagwaba tana narke masa

Adaddafe yakai 4pm a hospital sannan ya nufo gida

Ita kuwa tana bararraje afalon qasa hannatu ta mata danmalele ta baza mata a plate, yasha manja da yaji ga kuma robar yajin agefenta

Tafaraci kenan ya dawo

Hannatu tana gaishesa ta wuce dakinta

Shikuma zama yayi agefenta aqasan carpet yana cewa babyna nayi missing naki sosai

Ita murmushi tayi tace me too only, munyi kewarka muma

Tana maganar tana kaiwa loma abakinta

Kallon abinda takeci yakeyi da kyau sannan ya dubeta baby mene ne wannan

Itakuwa tsabar dadi har wani lumshe idanu takeyi tace danmalele zakacine

Kai baby a ina kika koyi cin wadannan abubuwan amma dai dafatan bazaima little babyna illah badaiko

Bata fiska tayi tace nifa wato yamun komaima badamuwarka baneba saita babynka kake ko

No bahaka bane baby ke ai babbace amma babynmu baiyi kwaribafa kike wannan ciye ciye

Tace to nidai inzakacine muci inka qoshi kuma shikenan

Tafada tana qara gumbuda yaji

Kutt baby irin wannan cin yajin haka fa yafada yana daukar roban yajin

Marairaice murya tayi tace pls kabani yajina inbakason yajin barin saka maka agabankaba

Yace nikam barinciba kici dadi lfy amma dai yajin nan ya isheki haka nan

Tace nikam kaban kayana tunda baci zakayiba

Yace ko baxan ciba bazan bakiba

Ganin dagaske yakeyi yasa tace toh naji dan qaramun kadan tai maganar tana langabe kai

Yadda tai maganar yabasa dariya yace shikenan debi kadan to tana diba ya rufe yamayar kitchen

Baby barinje na watsa ruwa kafin kigama ko

Toh afito lfy tafada tana cigaba da cin kayanta

Girgiza kansa yayi kawai yana murmushi yadda tabada hankalinta wajen cin wannan abin

*****
Haka rayuwa yaci gaba tafiya masu cikin kwanciyar hankali da natsuwa

Dan yanzun fauziyyah ta murmure sosai daga laulayin datake ba abinda ke daminta

Sai dai kwadayi kam kamar kullum qara mata akeyi

Hannatu kuwa mutumiyar kirki bata gajiya da yimata wannan da wancan

Hankalin papa ya kwanta tunda tasamu lfy batada matsala yanzun

Rainon cikinsu sukeyi cikin tattali da kulawa

Sannu ahankali cikinta yake girma har yakai yanzu watanni shida

Ya fito yayi mata das dan gaskiya cikin ya qarbeta sosai yaqara mata kyau idan tayi kwalliya sai cikin ya fito yamata gwadas ajikinta

Wani sontane kullum ya ke qaruwa acikin zuciyar papa yadda kullum itama take tattalinsa ta take bashi kulawa dikda cikin dake jikinta bai hanata ta bashi haqqinsa yadda yakamata

Yanzun har girki tana masa hakan yasa hankalinsa ya kwanta sosai yayi wani haske harda wata yar qiba yayi wadda tamasa kyau sosai

Kullum adduar su momcy dasu Abba bai wuce Allah ya sauqeta lfy ba

*****
Yaukuma da shagwaba ta tashi

Kwance tasamesa a bedroom nasa yana nade acikin wani milk blanket mai laushin gaske

Doguwar rigace ajikinta ta atampa mai laushi

Tamata kyau sosai sai qamshi takeyi

Bakin bed din tazauna tana kallon kyakykyawan fiskansa mai matuqar annuri

Wani kyau taga ya sake mata dikda baccinsa yakesha peacefully

Sannu ahankaki takai dan yatsanta kan bakinsa tana shafawa ahankali

Dan motsi kadan yayi alamun yanajin ana tabasa

Jikin kunnensa takai dan qaramin yatsanta tana sosawa

Bude idanunsa yayi ahankali yana kallonta da alamu bai gaji da baccinba

Cikin muryar bacci yace yadai akayi babyna

Ashagwabe tace nidai katashi hakannan

Pls baby kibarni sai anjima kadan ko kema kizo muyi baccin atare

Nidai nidai banjin bacci Allah kuma kaima katashi

Oh baby pls fa nace
, tace umum fa nace tana janye bargon nasa

Toh naji zantashi amma saikin bani .....yaqarashe maganar ahankali

Cikin sauri ta waro idanunta tace aa wasa nake maka yi kwanciyarka

Bude idanunsa yayi yace ai tunda kikasani natashi saifa kinbani

Miqewa tazoyi yayi saurin riqe hannunta ya daura hannunsa akan cikinta yanajin yadda yake motsi

Baby kinji little babyna yanason gaisawa da daddynsa, nima kuma inasonjin ya babyna ya kwana

Kwantawa tayi ajikinsa da murya mai sanyin shagwaba tace ba jiyama kaji lfyrsaba nidai bayanzunba

Aa baby jiya ai good night namasa yanzun kuma zan masa good morning yafada yana shafan cikin nata

Narkewa takumayi ajikinsa tana cewa nidai katashi kayi wanka kayi break

Aa baby wani break kuma bayan kinzo kin tayarmun da hankali jifa yadda kike qara kashemun jiki da salon shagwabarki, kuma kemafa kinaso kina kaiwa kasuwa jibi yadda jikinki yayi...

Bai qarasaba takai hannunta tana dukan qirjinsa cikin wasa nidai kasakeni intashi

Aifa nafada ba inda zakije baiqarasaba tace wash cikina tana riqe cikin

Ai baisan ya akayiba yagansa azaune cikin rudewa yake cewa mai yasameki baby mene ne

Cikina kadagani zaune tafada kamar zatayi kuka

Ok ok yafada yana miqar da ita zaune

Kafin ya zame blanket din jikinsa ta tashi da sauri tayi hanyar fita tana cewa saika fito kuma 20mins nabaka

Baby au dama bagaske kikeyiba kika tsoratani ko

Tana bakin qofa tace bakaki katashiba

Good kinmun 1-0 ko bakomai zamu hadu yafada yana miqewa

Ita kuma ta fice....

.

Bayan dawowarsa da kwana biyu,dasafe bayan sun karya zai fita office,saida yagama dik abinda yakeyi sannan yadawo bakin bed inda fauziyyah kezaune,yana zama ta kauda kanta gefe fiskanta babu walwala da alamun fushi takeyi dashi, ganin yadda taci magani tawani juyarda kanta gefe guda saita basa dariya,aifa tanajin yadda yake mata dariya saita qara qulewa,hannunsa yasa ya juyo da face nata yana kallonta kuma baibar dariyar ba,cikin fushi tace nikakema dariya ko saboda ganan mental agabanka, sai anan yayi magana yace no nibadake nakeba baby,to inbadani kakeba kaidawa tunda dagani sai kai ne adakinannan,yadda tai maganar tana murguda mai baki shiyasake basa dariya,haushine yasake kamata ta rarumo pillow tana kwada masa,riqe pillow din yayi yana cewa nadaina baby nadaina barinsakeba kuma bafa dake nakeba,kamar zatayi kuka tace nidai kakyaleni naji da guda daya bakawai kazauna kanamun dariyaba baicin ka hanani fita, baby kece kikasakani dariya da kike fushin rashin gaskiya,tace naji banada gaskiyan katashi katafi abinka ba ruwanka dani sai hawaye sharr,ahankali yace ya salam babyna akan nace kizauna agidane kike fushi hadda kuka?,ita dai bata kulasaba saima cigaba da hawayenta datakeyi,hannunsa yasaka yana goge mata hawayen da murya mai taushi yake cewa ya isa hakanan badai unguwaba zamu tafi tare amma kigane badagangan ne nahanaki zuwaba aa saidan yanayin da kike ayanzun,da kinfita qafafunki sufara ciwo shiyasa amma kinsan ai inda badan haka taya zan hanaki zuwa gidan TJ,tunda kinason zuwa barin hanakiba amma on one condition,dasauri tace nayarda fadi naji,bazaki yini azaune waje dayaba kitakuramun babyna yaqarashe maganar yanajan dogon hancinta,eh nayarda nayarda,yace toh muje kisaka mayafinki muje nasauqeqi kada na makara,cikin zumudi ta miqe ta fice zuwa bedroom nata,murmushi yayi yana kallon yadda tafita da murnanta sai ya tsinci kansa cikin nishadi dan dik abinda takeyi birgesa takeyi har cikin ransa kuma bai qaunar bacin ranta
.
Aqofar gida ya sauqeta yace kigaida mmn mubeen saina dawo da yamma zanshigo mugaisa,tace toh Allah ya tsare tamasa kiss a chiks nasa har data fita yace emm baby jimana,juyowa tayi tana kallonsa,cikin kallon soyayyah mai narka zuciyar wadda akema yace tum apna kayalakna(kikularmun da kanki),cikin murmushi tace i will insha Allah,good my princess yafada ,itakuma tace bye sannan ta fice shikuma yaja motarsa ya wuce,tana shiga khairy da murna ta tareta tana zolayarta barka da zuw mai sarauta,uwargida kuma amarya agidan likita,cikin dariya tace fadi kanki tsaye wannan haka yake,bayan sungaisa sukayita hiransu na yan uwa abin shaawah,haka suka wuni tate har TJ yadawo sai wajen4:30pm sannan papa yadawo amma haka TJ ya hanasu tafiya wai sai sunyi dinner tukun sutafi,haka suka haqura sai bayan ishai sannan sukafi amma kaginnan fauziyyah ta matuqar gajiya sabida yadda qafafunta ke mata ciwo, kawai sotake su isah gida dan tagaji da zaman motanma, tun amotan tafara kuka tana wayyo qafarta,haka yadinga lallaminta har suka iso gida,tundaga ranan fita inba yazama doleba ko antinatal bata zuwa ko ina

Haka suka cigaba da rainon cikinsu, inda papa yake matuqar bata kulawa na musamman irin wadda mai ciki take buqata,cikin yana rayuwa.cikin halin lfy har Alah yasa ta cika EDD nata sai dai haihuwa shiru,ganin ta wuce EDD nata kuma haihuwa shiru yasa tafara damuwa dan batada damuwar data wuce ganin tarabu da cikin jikinta cos tagaji dashi sai baqar wahala datake sha,ga ciwon qafafu idan tazauna dakyar zata rarrafa ta tashi,ganin yadda hankalinta ya tashi sosai yasaka papa damuwa amma bai nuna mataba sai lallaminta dayake hadi da rarrashi,yanzunma suna kwance har wajen 12 nadare taqiyin bacci,babyna yakira sunanta ahankali cikin natsuwa,umm kawai ta amsa, meya hanaki bacci har wannan lokacin umm  yana shafan gashin kanta,cikin damuwa tace nibanasonyin bacci dawurine saina farka cikin dare nagagara bacci idanuna su bushe,baby damuwar da kikasama rankinefa yasa har baki iya bacci,tace aiba dole nadamuba khairyfa lokacin data haihu batama cika EDD nataba ammma ni harna wuce da kwana biyu  sai kuma tafara kuka,haba baby ya kike abu kamar wacce bakisan cewar shifa EDD dama 2weeks before or 2weeks after bane,pls naroqeqi ki kwantar da hankalinki kda kije BP naki ya hau baicin bakidashi,haka yasamu hartayi shiru da haka har bacci ya dauketa, washe gari bayan yadawo daga office suna zaune yace baby yadai jikin bakinjin komai,tace babu abinda nakenakeji nikam,yace shikenan Allah ya kawo haihuwan cikin sauqi,tace amin ya Allah

Bayan sallan ishah suna zaune suna cin abinci sai ya lura bataci sai juya spoon din takeyi ,cikin kulawa yace babyna yadai bakicin abincin koba kyason asamomaki wani, aa kawai maratane ta kulle,marakuma baby, tace eh Allah kuwa yace to kidaure kici abincin,tace sai anjima idan tasakeni amma yanzun barin iyaciba,hankalinsane yaji ya tashi amma bai nuna mataba dan tunda yamma daya dawo yaga alamun haihuwa ajikinta yadda cikin yayi qasa sosai fiye dana kullum,shima abincin da bai qarasa ciba kenan

Wasa farin girki tun tanajin abu kamar wasa har yazama gaskiya dan wani matsanancin ciwon mara da qafafu takeji kuma batsan taya zata misaltashiba bama,12am abunfa yaci tura bashiri yadauketa sai hospital akanhanya yakira momcy yafda mata sunkusa isa asibiti fauziyyah tana labour ,aifa nan itada da daddy suka taho asibiti ba shiri,papa suna isowa sibiti aka wuce da ita labour room,shima bayansu yabi ya shiga ciki,sai dai tashin farko ana gwada BP nata akasamu yahau sosai har 160,nanfa hankalinsa ya tashi dik yasan cewan hakan tana faruwa amma dai yadamu sosai sabida tsoron kada eclemsia ya shigeta

Har akayi sallan asuba shiru bata haihuba sai dan karen azaba datake shafawa,nanfa papa yasake inda yakama ya birkice shima lallashi hadi da nasiha su momcy sukai tamasa haryasamu natsuwa,amma ya gagara komawa labour room din cos bazai iya ganinta awannan halinba,suna zaune  saiaddua dasuke mata amma babu wanda akafadama around6:30am ta haiho qaton danta namiji,wani saeedah taji lokaci guda,jin kukan jariri yasa papa miqewa cikin sauri yashige labour room din,kanta ya nufa ya riqe hannunta yana mata sannu tare da adduoi,sai daime anasake gwada BP nata akaga yasake hawa sosai180,aifa nan hankalin papa ya kuma tashi take ashiga bata taimakon gaggawa gudun abinda zaije  yazo.....
.

Hannunsa sarqe cikin nata ya riqe gagam kamar za'a kwace masa ita,bakinsa yakai saitin kunnenta yana kiran sunanta cikin natsuwa da sanyi,babyna kina jina babyna,da kai ta amsa masa alamun eh tana jinsa, ajiyar zuciyah mai qarfi ya sauqe jin tana cikin hayyacinta,wasu allurai Dr Zainab tamata sabida BP nata kafin tasa aka miqo babyn saitin fiskanta tace mata madam ganan babynki mene kika samu?, kallonta takai kan babyn nata fari sol dashi kuma qato nan take wani qaunarsa taji yaratsa dikkannin jiki da bargo nata, cikin sanyin murya tace baby boy ne,murmushi Dr tayi tace good,sannan aka wuce da babyn dan agyarashi,haka papama sai alokacin yaqarema abinda ta haifa kallo sabida hnkalinsa na akan matarsa da lfyrta,murmushi kawai yake yana dad'a hamdala ma ubangiji abisa kyautar daya masa,yana rungume da ita har aka gyarata aka d'inketa dan ta qaru sosai kasan cewar girman yaron,dikda anmata alluran rage zafi amma baihana papa lallaminta yana shafar knta cikin salon soyayya da kwantar mata da hankali har aka gama mata komai,dakansa ya shigar da ita toilet dake cikin labour room din yamata wanka tsaf sannan ya fito wajen su momcy ya dan karb'an kayanta
  momcy tana ganinsa tace yadai papa su fauziyyah suke,da murmushi sosai afiskansa yace momcy lfynsu qalau kayanta ma zaki bani dan zaa maidata obstatric room,cikin murna tace masha Allah shikuma angonnawafa dan nurse tacemun namijine,sake fad'ad'a fara'arsa yayi sannan yace shima lfyrsa qalau suna shiryashine amma saikinganshi farisol dashi kyakykyawa kuma qato shiyasa ya bata wahala,momcy takama baki tace oh papa babu ko kunya kake jero wad'anannan bayanai haka,d'an sosa qeyarsa yayi yace kai momcy yawanefa yanzun wane kunya kuma ai gara mutum ya nuna jin dad'insa tunda kud'i baxai saya masaba,kayan tamiqo masa tace Allahu ya shiryeka papa kaikam kunyarka da sauqi tafada tana cewa kafin kufito barinje office d'in daddy toh nasanar masa lfynsu qalau sannan ta wuce, shima ya koma ciki
.
Dakansa ya shiryata tsaf,sannan ya sunkuyo da kansa dai2 face nata yace my princess sannuko, murmushi tamasa kawai sabida batajin qarfin jikinta,ina kemaki ciwo? ya tambayeta yana shafan kanta, babu tafad'a, sai dai banjin qarfin jikina ne kawai, Alhamdulillah idan kin huta zakiji kinware kinjiko my life, gyad'a masa kanta tayi dai2 da nurse ta qaraso wajensu hannunta d'aukeda babyn, cikin girmamawa tace Dr ganan babyn tana miqo masa,hannu biyu yasa ya karb'i d'ansa kuma gudan jininsa,cikin so da qauna marar misaltuwa yake kallonsa ga yalwatatticiyar fara'a kwance kan fiskansa,lokaci guda yasakejin qaunar yaron kamar ya maidashi cikin cikinsa,yaro qato kyakykyawa mai kama da babansa dan babu ko tantama kamanninsa sak papa,sai qamshi mayukan jarirai yakeyi,an saka masa kayan sanyi farare sol masu sirkin light blue,ankuma nadesa cikin light blue showel sai qamshi yakeyi,nan take ya tofa masa adduo'i tareda sumbatarsa ta ko ina,fauziyyah kuwa kallonsu take cike da zallar qauna dan sun matuqar birgeta,kallonta yayi yace madam ganan babynmu karb'esa kisa masa albarka ya miqo matashi,karbansa tayi tana murmushi sannan itama ta tofa masa adduo'i
  nurse ce tadawo tace yallaba'ai za'a maidata dkin hutu sabida ta huta sosai, is ok yafada yana karba'an babyn, itakuma tadawo kan wilchair aka turata,abakin qofa sukaci karo da momcy dawowarta kenan sai suka wuce room da aka kai fauziyyahn,papane ya jawo plask ya had'a mata tea mai kauri ya tallafota yana bata inda momcy ke riqeda yaron tanata kan buga waya tanasanar da haihuwan,bayan tasha tea sai anan bacci yafara fisgarta sabida alluran da aka mata,bada jimawaba bacci ya d'auketa,sai anan papa yaji natsuwarsa yadawo jikinsa,daddyne ya shigo momcy ta miqo masa babyn tana cewa ganan abokinka sai bacci yake da alamu zaiyi haquri ba irinsu ooba,tafad'a tana kallon papa,dariya kawai yayi ya fice dan yagane dashi momcy take,yana fita yafara buga waya yana sanarda qaruwan da yasamu, haka ma'aikatan asibitin wad'anda suka sami labari sukaita masa murna,shikuwa bakinnan bai rufuwa tsabaragen farin ciki
.
Kwananta d'aya da haihuwa suka koma gida inda yan uwa da abokan arziqi suka dinga zuwa asibiti gaisheta,hakanan dik wata kulawa da maijego da yaronta ke buqata momcy tana basu,hakan yasa basuda matsala,cikin ikon Allah BP nata ya sauqa sosai dikda bai dawo normal ba
  Kwanansu Abba da mama da qanwar maman umma hajja wadda itake binta amma bata da aure mijinta rasuwa yayi suka zo bh kuma ita zata zaunama fauziyyah zuwa arba'in,fauziyyah taji dad'in zuwansu sosai haka suka yini lis sai yamma suka tafi,bayan magriba ya maida momcyma gida tunda ganan umma hajja,suna shiga falo zaune suka sami daddy yana kallon Aljazeerah news, momcy tace barita watsa ruwa tukun data zauna sannan ta wuce,bayan papa sun gaisa da daddy nan yake tambayarsa umm daddy dama inason tambayarka wanne suna za'a sanyawa yaron,murmushi daddy yayi had'i da gyara zamansa yace kaji kafa Alamin dawani zance,aikai zaka zabi sunan daka yadace saika masa hud'uba dashi,shiru yad'anyi yace shikenan daddy zanmasa hud'uban da sunanka,kallonsa daddy yayi yace anyakuwa bakaso kankaba banason kazamo cikin mutane masu son kansufa,kallon daddy yake cikin rashin fahimta yace menayi daddy?, daddy yace inhar dacewane to sunan Abbanku shiya dace da yaronnan sabida haka nina yafe asanyawa masa sunan Abban fauziyyah dan aminina ya cancanci fiye da haka,papa yace insha Allahu sunan Abba zaa saka masa ,cikin jin dad'i daddy yace masha Allah, Allah ya muku albarka,ya amsa da amin, nan sukaita hira har momcy ta fito kafin yamusu sallama ya tafi

*****
Washegari dasafe kamar kullum ya shiga ya dubasu yaga yadda suka kwana,cikin sa'a yau yasamu fauziyyah idanunta biyu harma tayi wanka, dan yau jikinta da sauqi sosai takeji,shima babyn an masa wanka ana saka masa kaya kenan ya shigo, har qasa ya duqa yagaida umma hajjah,bayan sungaisa ta miqo masa yaron dan tagama shiryashi sannan zata fice, cikin girmamawa yace umma nifa fita zanyi nashigo mugaisane dama, tace lah bakomai zanhado mata abin karine kayi zamanka sannan tafice, tana fita ya maida kallonsa kan fauzynsa wanda shigowarsa yakejin wani shauqinta na d'ibarsa amma ya matse sabida idanun umma hajja, wani kyau yaga tamasa tayi wani bulbul da ita irin cikar jegonnan, matsowa yayi bakin bed inda take zaune ya kwantar da yaron abayanta kafin ya rungumeya ajikinsa yanajin tabbas yayi keawarta dan rabonda ya kebe da ita haka tun randa ta haihu,itama sake narkewa tayi ajikinsa cikin salon murya mai sanyi tave  momrning myonly, saida yabata wani hot kiss sannan yace morning my princess,kuntashi lfy dai, lfy lau muke n u?,yace nima haka sai matsanancin keawarki dake damina baby i missed u so much yafada yana kissing dogon hancinta,tace nima hakafa yace eyyah kice zamuna dan fakan idanun umma mudamke rage zafiko yafada yana kashe mata idanu,zaro idanu tayi tace waa tab nikam banceba,dariya yayi yace sarkin tsoro meye nawani zaro idanu, tace bawai tsoro bane kawai banmanta labour room bane,yace indannan wannan ne kada kidamu next nizanyi labour d'in tinda kinyi naki ko sweety, tace ah lalle kuwa naqi wayon,yace toya jikin dai?, tace dasauqi sosai,yace good amma ba inda kemaki ciwo ko? aa babu komai yanzunkam,yace yayi kyau tinda har kinwarke kawai kifara shirin karban new baby tunda yazunma babu wanda zai ganki yace kinhaihu,tace lallekuwa ainida haihuwa bayanzuba, yace tab kisake lale danni dik shekara sai kin haihu sonake natara yara masu yawa yafada yana miqewa tareda d'aukar babyn ahannunsa,tace umm maganarka batada amsa, yace ko,tace yess,yace zamugani to,baby barinje  da my little baby inason zan masa huduba, tace toh, sannan ya fice.........

.
Baifi 30mins ba ya dawo dashi sai kuka yake zabgawa,afalo yasameta tana breakfast,jin kukansa yasa ta ajiye spoon d'in hnnunta ta karb'esa,baby sauri kibsa bincinsa ko yunwane yake dminsa yayi maganar yana kallonta,tace is possible ma hakan cos yayi wanka baishaba kuka fita,cikin tausayin yaron yace ayyah my little baby am sorry daddyne ko yaqarasa maganar yana shafa kan babyn,shikuwa tunda yasamu ya cafke abincinsa yayi shiru sai zuqa yake abinsa,papa cikin qaunarsu ya zuba masu idanu yana kallon yadda take shayar da yaron,qirjinnan acike taf kuma atsaye cak kamar bata haihuba nan yaji ransa ya biya take ya miqa hannunsa yana shafan samansu,d'agoda fararen idanuwanta tayi tana kallonsa kafin tace my one kanason ya kwarene?,aiko cikin sauri ya d'auke hannunsa yana cewa Allah baby nayi missing nimafa gaskiya that's y nad'anji duminsu yaqarashe maganar murya qasaqasa,murmushi tayi sosai tace toko zaka shane?,d'an zaro idanu yayi yace aikam da zuqa 1 dan zuqe masa candy candyn,atare sukayi dariya sabida d way yayi maganar irin so funny d'innan,ahankali yace baby bakitamb ayi sunan da za'a sakama babynmu bafa gashin harna masa hud'uba batareda neman shawarinkiba,cikin natsuwa tace nikam dik sunan daka zab'a masa is ok awajena sai dai ince Allahu yamasa albarka ya kuma raya manashi rayuwar addinin musulunci,cikin jindad'in addu'arta yace amin ya Allah my wife,nagode da kika fahimceni sosai nasan kuma zakiyi farin ciki da sunan dana zab'armasa cos sunan mutum mai matuqar daraja da qima da kuma dattaku wanda nake fatan yadauko halayen maisunan,dan yanada kyau idan zakayi takwara kayima mutumin kirki,kodan kwad'ayin yasamu halayen kirki irinna mai sunan,cikin jinjina kai tace wannan haka yake kuma tayi na'am da zancensa,yace mata kicanki wanni sunane,batareda tunanin komaiba tace sunan daddyn mune dan har ga Allah tada'au sunan daddyne akasamasa,murmushi yayi had'i da girgiza kansa yace nop wifey bataciba,da mamaki ta dubesa kafin tace komai yace sunan Abbanmune wato SA'EED,kallonsa takeyi kurr yayinda taji wani sanyi aranta yadda papa ya mutunta mata mahaifinta,lumshe idanunsa yayi ya bud'e kafin yace yess sunan Abbanmune inyaso zab'i yana wajenki saiki masa alkunya dan bamai kiramun sunan mahaifi direct atow,rasama mezatace masa tayi zata fara godia,yace shshssh ya isa hakanan baby nimafa mahaifinane muyi fatan Allah ya albarkaci rayuwarsa,cikin murya mai sanyi tace ameen my only,sannan tace to zamuna kiransa da FAWWAZ,yace nice name shikenan tunda yamiki nima yamun,miqewa yayi yace barinje office madam zanbiya gida tacan so sai yamma zandawo tunda naga bakwa rabo da baqi,tace Allahu ya kiyaye adawo lfy akuma gaida su momcy dikdama d'azun munyi waya,yace amern babyna saina dawo saida ya paking forehead nata da swt kiss.kafin ya fice yabarga tanajin wani sabon qaunarsa har cikin ranta
.
Bashi ya dawoba sai yamma lis,sabida ayyukan dasuka riqesa a office,ga TJ yamasa waya kancewar zaishigo d'aukar madam nasa dan awajen fauziyyah ta yini dikda itama tsohon cikinne da ita,kaya niki niki sukaga ana shigowa dasu wadda tunda akayi haihuwar kullum acikin hidima yake baiko gajiya,saida ya gaida umma sannan ya wuce side nasa ya watsa ruwa ya fito falonsa na qasa dan TJ najiransa,yana shigowa TJ yafara yayi dai ngon qarni,kashe hannu sukayi papa nacewa fad'i kanka tsayeka qara,yace anahaka ango na fauziyyah mai komai dozen,yace toya son ranka saidawa,TJ yace yakuwa inba nace Allah yaqara dankwan soyayyah, papa yace oho nad'au sab'anin haka zakace ai,TJ yace waneni nan suka sheqe da dariya sukayita hiransu har aka kira sallan magrib, saida sukayi dinner tukun suka tafi
.

Haka kwanaki na tafiya har yau ana gobe suna arananne kuma jama'ar dambam suka iso, aunty mabarukhama yau ta iso aunty niima kuwa kusan kullum saitazo,washegarin suna akayi taro lafiyyen taro wadda fad'in irin kyau da fauziyyah da fawwaz sikayi b'ata lokacine,haka zalika irin kudi da kayan da suka samu abin sai son barka dan Abba sun taka rawar gani matuqa haka yan uwata ba,a barsu abayaba, kaxalika su momcy da daddy sunyi bajinta sosai,haka abokan papa tasamu kyaututtuka daga wajensu,mai kankat d'in kuwa wato uban gayyar DR ALAMIN,kayane na kece raini abin har bazai qirguba,kudi yakashe kamar ba gobe haka ya baje ya nuna farin cikinsa sosai,haka akayi hidima sosai akayi taro lfy akawatse lfy bayan anyi walima da yamma anraba kyaututtuka na abubuwa mai d'aukeda photon fawwaz,jama'a sunata saka albarka haka,kowa ya koma gida cike da farin ciki

Sai bayan sallan isha'i sannan tasamu natsuwarta ga wani uban gajiya dake daminta, fawwaz kuwa tuni yayi bacci dan yasamu anmasa wanka da ruwa mai d'umi yaji dad'in jikinsa sai bacci,itamma wankan tayi ta foto ta shirin bacci  harta kwant saiga wayar papa,da sallam tad'auka,wani sanyi yaji har cikin ransa sabida yau yini guda baigantaba baikumaji koda muryartaba,cikin murya qasa qasa yace my hrt i missed u so much,nazama maraya gani kwance nikad'ai,gyara kwanciyarta tayi tace me too baby nayi missing kwanciya afaffad'an qirjinka mai daukeda  dayalwataccen ni'ima,sake lumshe idanu yayi cos taqara kashe masa jiki sosai d ydda take salon maganarta,ahankali yace pls baby kizo side nawa dad'anji duminki kozan sami natsuwa,murya asanyaye tace haba my one taya harna kwanta zanfito na ratsa mutane nataho wajenka,yace pls mana baby kice nayi baqine zaki kawomun fawwaz,yafayi bacci  tin dazunamma barin dakkosa ahakan ,yawwa my wife that's y nake qara sonki, snnan ya kashe wayar,qatuwarhijab nata tasakaakan kay an baccinta tarungumo fawwaz akfad'antata fito falo nan tasamu su umma suna hira,kamar munafuka tace umma dama ya Alamain yayi baqi barin kaimusu fawwaz suganshi,umma tac e tokaishi mana gashima har yayi bacci,tace toh sannan tafice ta nufi d'akin papa.........

.
Tana shiga side nasa, direct bedroom nasa ta wuce,ahankali ta tura qofar ta shiga lokaci guda sanyi da qamshi mai dad'i ya bugi hancinta,tasowa yayi ya karbi fawwaz sannan ya kwanto da ita jikinsa,ahaka suka qarasa bakin bed ya kwantarda fawwaz tareda manna masa kiss afiskansa,baice da ita komaiba saima d'aukan remote da yayi ya rage qarfin AC, sabida fawwaz,kafin ya jawota jikinsa ya zare hijab dake jikinta, ya nufi kan resting chair dake gefen gadon ya zaunarta shikuma ya miqe ya kwan tareda daura kansa akan laps nata,lumshe idanu yayi yana shaqan qamshin dake fita daga jikinta tamkar bamai jegoba,jin yayi shiru yasa takira sunansa cikin daddad'an muryantamy one,bud'e lumsassun idanuwansa yayi yana kallonta yace umm babyna ya akayine,cikin shagwab'a tace naji kayi shirunefa,sake gyara kwanciyarsa yayi yace badolenaba nasami natsuwa,rabonada najini ajikinki haka sati guda kenanfa,gaskiya kisan yadda zakiyi dan wlh akame nake,d'an zaro idanu kad'an tayi tace ammadai kasan haihuwa nayiko kumama koba hakaba aidai banada tsarki,yace aibacewa nayi zanje canba kawai kimun irin abinda kikemun d'innan kozansami sauqin abinda nakeji, turo baki tad'anyi tace inda natafi wankan gidafa?,aifa tashi yayi zaune yace wankan me aiko da ba inda zakije lalle baby kindaina sona datausayina, tace meya kawo wannan mganar kuma, yace ahto inba hakaba taya zakice wai inda kuntafi to nikuma kubarni nayi yaya kenan, tace cikin zolaya saikayi zamanka agidankaman, yace ah lallaikam kedai Allah ya taqaita umma ta fansheni shiyasa nake dad'a ganin girmanta sosai dan Allah badan itaba birkicewa zanyi kawai ince bamai daukarmun mata wani wai wankan gida,dariya yabata kuma tasan zai aikata hakan,yace au dariya nabakima,yace aa nibanceba ta lumshe idanuwanta ta jingina da jikin kujeran dan bacci tafaraji sosai,jin tayi shiru yasa yace babyna kema kingajiko,nagaji dik jikina ciwo yakemun tai maganar idanunta alumshe,ayyah sannuko barin maki tausa yana maganar yana.....nanfa itama ta biyesa sabida tasan halin mijinta inhar akantane baya kure abubuwa da dama,shiyasa take qoqarin samar masa natsuwa,takai fiyeda awa guda kafin ta miqe itama jiki amace ta d'auki fawwaz da kyar ya miqe sabida shima jikinsa yayi weak sosai harwani bacci yakeji ya rakota har bakin qofa yanata zuba mata albarka sannan yamata saida safe ta wuce b'angarenta,shima juyawa yayi ya wuce toilet, wanka yayi ya fito ya bi lfyr gado lokaci guda bacci mai dad'i yayi gaba dashi zuciyarsa fess

Kwanaki na tafiya inda Fauziyyah da Fawwaz kesamun kulawa na mussan daga wajen ma hajja,gashi kullum acikin yimata had'i na mussam take sabida gyaran jikinta, cikin sati uku suncanza sunyi kyau na mussamman,haka fawwaz ya cika yayi bulnul dashi,ga wayo da kullum yake qarawa, haka afannin papa kullum cikin basu kulawa yake har umma hajja tasaba da halinsa, tun tana jin kunyarsa harta wate yanzu,tunda zaishigo ya dauki fawwaz ya masa wasa kafin ya fice office haka idan yadawoma,kullum burinsa ya faranta masu, momcy ma tana yawan zuwa dubasu akai2,cikin ikon Allah har saura kwana uku suyi arba'in, fawwaz ya qara girma yayi kumatu inka ganshi zakace d'an wata uku ne,ga kyau da kullum yake qarawa,ranan da suka cika arba'in ranan suka tafi dambam,papa dakansa ya kaisu bai kwanaba aranan ya juyo bbayan yayima umma hajja shatara ta arziqi,yabarsu sai bayan sati biyu zaidawo ya daukesu,haka ya dawo bh cikin keawarsu

Cikin sati biyu da tayi. adambam babu inda baya zagaba,gidajen yan uwa da abokan arziqi,tindaga kan danginta harna papa,wadanda suka jima basu gantaba idan sunganta sai dai suce masha Allah,kullum Abba indai yana gida to yana tiqe  damai sunansa, dan wani iri son yaron yakeyi abin sai wanda yagani,ana gobe zasu tafi kusan kwana sukayi suna hira dasu mama,washegari papa yazo yadaukesu inda takejin kewar gida dan tasaba asati biyun  datayi,papa kuwa zuciyarsa cike da farin ciki koba komai farin cikinsa ya dawo,aranan suka sake barje amarci dan papa jinta yayi kamar yau ya bareta aleda dan baqaramin gyara tashaba bayan taje dambam ma,

Rayuwa sukeyi mai tsafta cike da so da qauna,kowannensu yana qoqarin kyautatama dan uwansa, kullum papa yana sake godema Allah daya sake malaka mada fauziyyah,haka suke kula da d'ansu da tattalinsa, gashi sai girma yakeyi kamar wadda ake masa pampon iska,watanninsa takwas cur yafara tafiya abin shaawa,kullum rayuwarsu abin shaawa gashi Allah ya sake budama papa hanyoyin arziqi da dama, yana kuma qoqarin sauqe dik wani nauyinta dake kansa, amma yahanata aiki yace dik abinda takeso zai mata amma banda batun aiki,ita ma taamince tinda bairageta da komaiba

Watannin Fawwaz 13 gudu ko ina ba inda baya shiga,saiyaje gidan momcy ma ya wuni acan dan ba abinda bayaci kamar ya yayyen yato sabisa girmansa,ana cikin haka tsulum saiga ciki na watanni uku murna wajen papa baa magana amma fauziyyah hankalinta ya tashi matuqa......

.

Tunsafe bayan dawowarsu daga hospital take rizgar kuka akan cikin jikinta,tun ahanyarsu ta dawowa yake lallaminta amma kamar zugata yakeyi,hakan yasa haushi ya kamasa ya rabuda ita dan gani yake mene zai dameta tinda Fawwaz qalau yake, sai dai inkuma tana cikin layin matan da basason haihuwa dayawane kuma, shiyasa ya rabuda ita, suna isowa gida bai sauraretaba ya wuce ciki ya had'oma Fawwaz abubuwan da zai buqata ya kaishi wajen momcy ya wuni,yakai irin 3hours kafin ya dawo amma da mamakinsa har lokacin tana kwance a room nata tana aikin kuka,mamaki abin yabasa ya qaraso har bakin bed inda take kwance ya zauna,janyota yayi ya d'aura kanta akan laps nasa,kafin yafara magana anatse akuma tausashe, shalelena wai har yanzun baki haquraba haka kina ta kuka har kanki zaiyi ciwo babyna,batayi shiruba saima qara sauti datayi, hawayenta yafara share mata cikin lallami yace no wifey ya isa hakanan kukan kiyi shiru kifad'amun damuwarki kinji,amma kibar kukannan cos har cikin raina nakejinsa,ahankali ta tsagaita da kukan da dasashshiyar muryarta datasha kuka tace ni ka kyaleni naji da abinda keda muna sai hawaye sharr,haba baby dik akan kinada ciki yasa kika tada hankalinki saikace shine na farko haba my fauzy kada kiyi haka mana ki butulcema Allah akan kyautar da yamana bayan akwai dubunmu da basu samuba,kamata yayi mugode masa bawai kitada hankalinki ba ko kuma dai haihuwarce ba kyaso ko danine bakison haihuwar?, jikintane yayi sanyi yadda yake magana cikin damuwa hakan yasa dasauri ta girgiza kanta tace aa nibance banson haihuwaba ko dakaine banso, yace to fad'amun damuwarki, cikin sanyi tace fawwaz mafa shekarasa daya sannan kuma wlh nibanmanta wahalanda nashaba ko hutawa banyiba ace kuma cikine dani sai hawaye suka shiga zarya akuncinta, is ok baby ya isa haka indan wannanne kada yadameki tunda ya girma abinsa yana gudu ko ina, batun wahala kuma bana cemaki idan kinyi daya nima zanyi dayaba,so kada kidamu yanzu turn nawane nizanyi laulayi da labour iyaka kihaifo mana babynmu kyakykyawa mai kamada keh ya qarashe yanajan dogon hancinta,yanda yake maganar da lallami da taushi dik da tasan cewar bamai yiwuwa baneba amma taji sanyi har cikin ranta lokaci guda murmushi ya kubce mata,ganin tafara sakkowa yasa yace yawwa 'yan matana ko kefa amma da kintda hankalinki da nawa pls yawuce haka mu rungumi abinmu da addu'ar Allah ya kawoshi lfy,ahankali ta amsa da amin

.

Tin daga lokacin ta kwantar da hankakinta, ta haqura ta rungumi qaddara wacce tariga fata, da yardar Allah haka ta cigaba da rainon fawwaz da kuma cikinta,gashi tayi sa'a wannan karon batashan wahalan laulayi sai d'an abinda ba'a rasaba, cikinta nada watansa shida cur sannan ta yaye fawwaz lokacin watanninsa 16, dake yana samun kulawa sosai bazama ace yasha nonon cikiba, ana yayeshi momcy ta d'aukesa ya koma wajenta,haka papa yacigaba da kulada fauzynsa da kuma unborn child nasu,har Allah yasa yakai watannin haihuwarsa,nan suka fara tsammanin haihuwa kuma kullum suna addu'ar haihuwar tazo da sauqi,Allahu maji roqon bawansa wata ranan talata da misalin qarfe 12am naquda ya tashi fauziyyah wacce dama baccin rabi da rabi take tinda cikin ya tsufa, ba b'ata lokaci suka tafi asibiti cikin ikon Allah asuban fari ta haifo yarinyarta mace, batada maraba da mamanta dan tsabar kama wane antsaga kara,murna wajen papa ba'a magana saikace wannan ne haihuwar fari da aka masa,haka su momcy suma murna,washe gari yan uwa da abokan arziqi suka cika anata murna,ranan suna yarinya taci sunan momcy SAUDAH zasuna kiranta da FAIHA, nanma ansha hidima sosai dan baqaramin kud'i papa ya b'ararba,abin sai son barka tare da fatan Allah ya raya baby Faiha

.

*2 YEARS LATER*
Fauziyyah ce zaune awani tangamamen falo na alfarma,tana riqeda jariri tana shayardashi wadda dagani baifice kwana arba'inba,papane ya shigo d'aukeda Faiha akafad'arsa, hannunsa riqeda hannun Fawwaz wadda kesanye da uniform da alamu tasowarsa daga school kenan,da sallama ya shigo fiskansa d'aukeda qayataccen murmushi,d'agowa tayi ta amsa itama da murmushi tace oyoyo har kundawo,zaunarda Faiha yayi yana cewa mundawo kinsan yau friday shiyasa,tace hakanefa ai sai malam saminu yayi magana kancewar zai tafi d'akko fawwaz, nace yau kana gida kama fita daukosa lokacin bainan shiyasa baka sanar masaba,yace ok yaukam nahutar dashi, lami mai aiki takira tadauki fawwaz tacanza masa kaya,sauqarda faiha yayi yace mamana koma nan kizauna barin d'auki daddynako,nan tab'ata rai zatayi kuka, fauziyyah tace kada kiyi kuka momcyna rabuda daddy shida FARHAN (mesunan daddyne) bazasusha ice cream namubako,gyada kanta tayi tana hawa jikin umminta,papa yace haba mamana kinfa girmane shiyasa, fauziyyah tace rikiciba idan bakwanan dik gidannan yamun wani iri gashi nakasa sabawa da sabon unguwannan,papa yace idan sunanan kuma kice sundamekiba tunma bakiyi komaiba,wani kallo tamasa wadda yasashi dariya har itama yabata dariyan tace dole kayi dariya mana,yace aidai ni kece kikasani dariyan da wani kallo da kika nausheni dashi,cikin dariya tace dafatan bakaji ciwoba to?, yace ciwo kai harya ma kunbura wajen, tace oh sorry amma kacancanci fiye da hakama,yace to miye aciki keda bawaan haihuwa kike shaba,turo dan qaramin bakinta tayi tace nifa nagaji dayin kunika yanzunkam, yace to miye aciki bakiga kuma haihuwarsu yafi sauqiba,tace umm nidai yanzunkam dan huta atow tai maganar tana juya manyan idanuwanta,yace muyi fatan samun masu albarka koma yaushene,tace hakane my only,yace yawwa matana nidai ba abinda zancemaki sai Allah ya biyaki da gidan aljanna dan kinmun komai arayuwa ,kinbani so, qaunar, da kulawa ga kuma kyawan yara, kinga banada damuwa sai fatan Allah ya bani ikon sauqe nauyinku dake rataye  awuyana,cikin  tsantsar shauqin qaunar mijinnta tasaka hannunta ta saqalo wuyansa had'i da kwantowa jikinsa ta amsa da amin ya Allah mijina abin alfarina akoda yaushe,saka d'ayan hannunsa yayi ya rungumeta tsam ajikinsa sunajin wani yanayi na musmman wadda sukad'ai sukasan ma'anarsa atattare dasu.......

   TAMMAT BI HAMDILLAH...

0 comments:

Post a Comment