Monday, 26 February 2018

AUTAR HAJIYA Page 21-30

AUTAR HAJIYA Page 21-30
.
Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar gidan akwai 'kofa waccce zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a 6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida khaleed da yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake.
Fadaila ce ta kalli agogon dake manne  jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar amma bataji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta d'auko wani tsadadden less ta sa, bata tsaya d'aura d'ankwaliba, bayan ta tsara make-up yafa d'ankwalin kawai tayi a kai, sannan ta fito general falo ta zauna jiran shigowar angonta.
Auta kuwa itama tana d'akinta ta gaji da jiran shigowar ango, saboda haka, itama wanka tashiga, bayan ta she'ka wanka, ta fito, ta tsaya gaban dressing mirror tana tinanin me ma zatayi, yanzu dai kam batada lokacin yin make-up da wannan daren, lotion kawai tashafa me d'adin kamshi, sannan ta feshe jikinta da turarruka masu kyau, tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta, ta Sanya, tsayawa tayi tana kallon kanta, yanda rigar tayi mata, sharara tamkar batasa kome ba, dan duk illahirin surar jikinta bayyane take, tayi niyyar canja riga saboda tana kunyar khaleed yashigo ya ganta haka, amma kuma tana jin zafi-zafin da ake a garin, saboda haka tace bari ta d'an sha iska, idan taji shigowarsa sai ta caja, gado ta haye,ta kwanta lamo, zuciyarta cike da tinani kala-kala, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.
Karfe sha d'aya da rabi khaleed yayi horn Bakin get d'in gidan me gadi ya bud'e mashi yashiga,.
Fadila na zaune Falo saboda haka, da sauri tanufi d'akinta ta 'kara shafa humra, me dad'in 'kamshi sannan ta dawo falon ta zauna.
       Da sallama ya shigo falon, cikin kashe murya Fadila ta amsa salamar, tare da mi'kewa ta rugomeshi tayi Mashi sannu da Zuwa sannan ta kar6i ledar daya shigo da ita ta ajiye gefe.
d'akinsa ya nufa tabishi, acan ta had'a mashi ruwan wanka, sannan ta taimaka Mashi ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka, bayan ya fito daga wanka, wasu 'kananan kaya ya sanya masu sakai-sakai, sannan ya umarci Fadila da ta tashi suje falo.
Bayan sundawo falo sun zauna, khaleed ya umarci Fadila data d'auko ledar daya shigo da ita, ta tashi tana wani yanga tana karairaya, ta d'auko ta ajiye, sannan ya umarceta ta d'auko plate da cup's, kitchen tanufa ta d'auko duk wani Abu datasan zasu bu'kata.
Tana fitowa daga kitchen d'in taga ba khaleed, bata kawo kome a ranta ba, tana tinanin yana d'a'kinsa, saboda haka zama tayi tana jiran fitowarsa, amma har kusan minti talatin be fitoba, saboda haka d'akinsa tanufa, da sallam ta Shiga d'akin amma saitaga ba Kowa ciki, sai tayi tinanain koyana toilet ne,
Bakin 'kofar toilet d'in ta kanga kunnenta bataji alamar mutum aciki ba, Ahankli ta tura 'kofar toilet d'in nan ta'kara tabbatar da baya ciki.
Take zuciyarta ta ayyana mata inda khaleed yake, a fili ta furta *~Wallahi bazan yarda ba~*
.
khaleed kuwa a lokacin daya umarci Fadila data d'auko plate kitchen, tana shiga kitchen d'in da sauri yanufi d'akin Auta , dan tunda yashigo hankalinsa na gun d'akinta ko zata fito amma shiru bata fitoba.
Ahankali ya tura 'kofar d'akin kwance ya hangota kan katafaren gadonta wanda yasha shimfid'a da wani 'katon bedsheet, da manyan filo da 'kanana.
Baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ahankali ya isa Bakin gadon ya tsaya yana k'are mata kallo, kaf surar jikinta bayyane take, ga fitila d'akin kunne haske fayau ko'ina, lokaci guda yaji jikinsa yafara kyarma, besan lokacin daya hau kan gadon ba ya rungumota jikinsa baki d'aya yafara shafata, yakai hannunsa kan kirjinta yafara wasa da dukiyara fulaninta.
Cikin bacci tajita jikin mutum, gashi kuma anata romancing d'inta, cikin firgici ta bud'e idonta khaleed tagani ya 'kura mata ido baya ko 'kiftawa, ta bud'e baki tana shirin yin magana, ya had'e bakinsa danashi yacigaba da kissing d'inta, lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi, itako auta 'kara narkewa tayi jikinsa, tana mashi shagwa6a shikuma sai kara matseta yake jikinsa kamar wani ze kwace mashi ita,
Ji yayi anturo 'kofar da 'karfi, a firgice yakai dubansa ga 'kofar, Fadila yagani tsaye tana cika tana batsewa, shi kwata-kwata yama manta da ita, wani irin haushinta yaji dan ta yankemashi jin dad'insa, cikin d'aga murya yace, "Fadila meya shigo dake nan? Bata bashi amsa ba kuma bata motsa daga inda takeba, cike da jin haushin abinda tayimashi yace "get out, ki fita nace maki ganinan zuwa.
Ita kuwa Auta ganin Fadila yasa ta'kara narkewa jikin khaleed, ta dauki hannuwanta duka biyu ta sa'kalosu a wuyanshi, tana mashi wani shu'umin kallo wanda ya'kara rikitar dashi, tace "haba my dear, meyasa ka shigo baka sallameta ba, kamata yayi ka sallameta kuyi sallama kafin ka shigo, kaga yanzu tazo muna cikin jin dad'in rayuwarmu ta mana cikas.
Da gudu Fadila ta juya tabar d'akin dan jin hawaye na niyyar zubo mata saboda tsabar takaici, falo ta zauna tana share hawayen ba'kin ciki, a zuciyarta tana cewa
*_Lallai yarinyar nan ni zata gwadama duniyanci, to wallahi sai nayi maganinta cikin gidannan saina nuna mata nafita iya duniyanci_*
Nan suka isketa zaune suma suka zauna, Auta yanda take haka tafito, bako d'an kwali kanta, gashin kanta ya zubo kan kafad'unta, saboda haka hankalin khaleed yana kanta duk wani motsi nata sai ya had'iyi yawu,
     Da kanshi ya d'auko ledar ya d'auko plate ya juye dankwala-dankwalan kajine guda hudu, sai fresh milk daya ajiye masu gefe, da ruwan roba na swan.
Nan ya Uamrcesu dasu zo su ci, Auta dama ta kwanta da 'yar guntuwar yunwarta saboda haka matsowa tayi taci me isarta, sannan ta kora da fresh milk tasha ruwa, shima khaleed yaci sosai, sannan yasha ruwa, Fadila kuwa kasa cin kome tayi saboda zuciyarta cunkushe take da ba'kin ciki.
Bayan sun kammala ne khaleed yayi masu basiha akn zaman tare, sannan daga 'karshe, ya sanar dasu abubuwan dayake so da wanda bayso, dan su kiyaye.
Sannan ya kallesu yace idan akwai me magana zata iyayi, Fadila tace "babu,
   Auta tace ni maganata kawai itace duk abinda kakeso shi nakeso wanda bakaso kuma shine baniso kaga ra'ayimu yazo d'aya kenan.
Nan suka cigaba da fira sam-sama, yawancin firar ma tsakanin Auta ne da khaleed, Fadila duk takaici yahanata magana.
Saida suka kai 'karfe sha biyu da rabi suna falo, lokacin khaleed yafara jin bacci dan dama akwai gajiya tattatare dashi, saboda haka yace to yakamata mu kwanta hakanan dan dare yayi saosai, Fadila tace "Eh gaskiya nima baccin nakeji, kazo mutafi dan nima gajiyarce a jikina, Fadila ta tashi tanufi d'aki tana lumshe ido alamar bacci, ganin Auta bata tankaba yasa khaleed ya tashi yabi bayan Fadila, Auta tayi saurin shan gabanshi tace "Ai d'akina zamuje ko, Fadila najin haka ta juyo tace "kamar ya d'akinki, amma kinsan ay na girmeki, kuma niyakamata ace anba girmana, Auta tayi murmushi tace "ay nan gidan aure ne ba maganar girma, saboda haka kazo muje kawai,
  nan rigima ta kaure tsakaninsu, wannan tace d'akinta za'a fara kwana wannan tace nata za'a fara kwana, khaleed yarasa yanda zeyi dasu kawai sai ya koma falon ya zauna kan kujera three seater ya zauna, suma suka biyoshi suka zauna, kowace da abinda take sa'kawa a zuciyarta.
Shikuwa khaleed daya gaji da zama kwantawa yayi kan kujerar, tin yana kallonsu yana mamakin halinsu, har bacci yayi awon gaba dashi.
Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tasheshi daga baccin dayake, zaune yagansu, suduka sunyi shiru, da Alama ba wacce ta runtsa cikinsu, tashi yayi yanufi d'akinsa yashiga toilet yayi wanka sannan yayo Alwala ya kabbara sallah.
Sai lokacin sukuma kowace tanufi dakinta dan gabatar da tata sallar.
.
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a gidan khaleed, yau kimanin kwana ukku kenan kullum kwanan zaune sukeyi a falo, dan Auta ta kafe ita a dole sai anfara kwana d'akinta, ita kuma Fadila tace Sam bata yardaba, hakan ke sawa khaleed yayi kwanciyarshi kamar yanda ya saba, wato falo kan kujera three siter sukuma haka zasu zauna su tasashi gaba sunata hararar junansu.
Yauma kamar kullum, zaune suke babban falon gidan, da musalin 'karfe biyu da rabi na dare, shikuma khaleed yana kwance yanata sharar baccinsa hankalinsa kwance, yau ma atakaice haka sukayi kwanan zaune, asubah nayi ya wuce d'akinsa dan gabatar da sallah suma kowace tanufi d'akinta.
Khaleed abin na damunsa yarasa yanda ze 6ulloma Al'amarin, saboda haka bayan yayi break fast ya shirya cikin 'kananan kaya, wandon jeans ba'ki da jar T-shirt yayi matu'kar yin kyau.
'Dakin Auta yashiga, zaune ya isketa tsakiyar falonta, kan carpet hannunta ri'ke da waya tana game, da sallama ya shiga d'akin bayan ta amsa ya'karso inda take ya zauna kusa da ita, ta d'ago da manyan idanunta ta kalleshi tace "barka da kwana, yace "ku zanyima barka kuda ke kwanan zaune,
     Kafin tayi magana yaci gaba da cewa, yanzu Zainab rayuwar da kuka za6ar mana agidannan kuna ganin ya dace, ace ku duka ba wacce zatayima 'yar'uwarta hakuri,
   Amma Auta kinga kece 'karama yakamata kiyi hakuri nafara kwana d'akin fad'ila duka fa kwana biyu ne zan dawo d'akinki, haba Auta bakison kwanciyar hankalina ne?
     Wani irin kuka ta fashe dashi, cike da mamaki khaleed ke kallonta, cikin maganar dayayima Auta miye abin kuka.
    
Kuka tacigaba dayi tana cewa "shikenan khaleed ka nunamin kafi son Fadila akaina, kaje ka kwana d'akinta d'in wallahi nikuma idan har ka kwana d'akinta ranar zan bar gidannan, kuma idan natafi kada kayi tinanin gidanmu zanje, a'a zan tafi inda ba'a sanniba inda bansan kowaba, incigaba da rayuwata acan.
"Idan abin gaskiyane it's kace ta hakura ta barmin mana.
Haka khaleed yayi rarrashin duniyar nan amma Auta ta kafe akan sai dai ya fara kwana d'akinta, haka khaleed yabar d'akin Auta yana mamakin rigima irin tata.
A d'akin Fadila ma haka yasha daga da ita yana rarrashinta akan ta ha'kura ya fara kwana d'akin Auta, amma tace sam ita  bata San wannan ba, aiko abin ya 6ata ransa nan ya balbaleta da fad'a ta inda yake shiga ba nan yake fitaba, yace "shikenan kuyi duk abinda kuka iya, yanzu ke Fadila bazakiyi hankali ki ri'ke girmankiba ki kawo 'karshen wannan kwanan zaunen da kukeyi,
Cikin masifa itama take magana "Wallahi bazan yardaba, yanda ita bakace ta hakura ta barmin  ba nima wallahi bazan barmataba, ai ba fina sonka tayiba.
Cikin fushi khaleed yafita, a harabar gidan yanufi gurin ajiye motoci ya hau motarsa ya kunna, me gadi ya bud'e mashi get yadau hanya,
        Gidan abokinshi ya wuce Ahmad, a ranar can ya wuni be baro gidan ba sai bayan magrib, daga nan kuma gidansu ya wuce be dawo gidaba sai 'karfe tara da rabi na dare.
.
Da sallama ya shigo falon, Abin mamaki yau bega kowa a falon ba kamar yanda yasaba kullum nan yake iske matan gidan zaune suna jiran dawowarsa,
A hankali take tafiya dan bayaso suji karar dawowarsa, su fito su sashi kwanan falon nan,
  d'akinsa yanufa toilet ya shiga ya she'ka wanka sannan ya saka jallabiya marar nauyi, a hankali ya fito daga d'akin yanufi d'akin Fadila, kwance ya isketa kan katafaren gadonta tayi dai-dai tana sharar bacci.
Dalilin baccinta kuwa shine, bayan fad'an da khaleed yayimata yana fita ta fashe da kuka, a zuciyarta tana cewa
_(Shikenan ni dama nasan khaleed ba sona yakeba, hakanan su Momy suka ma'kale akan sai ya aureni, kuma nima ina masifar sonshi, sai yanzu na tabbatar da son maso wani nakeyi, dan kuwa kome Auta zatayi khaleed baya ganin laifinta, dama hausawa sunce so hana ganin laifi)_
Haka tasha kukanta ta gaji, 
    Nan take kuwa kanta yafara ciwo, dama ga rashin bacci na kwana ukku, bayan magrib taji ciwon kan yayi tsanani tasamu magani tasha, da misalin karfe takwas na dare tad'an kwanta aikuwa bacci yayi awon gaba da ita.
Nan khaleed ya 'kare mata kallo, yayi murmushi, sannan ya fito daga dakin, cikin hankali yakeyin kome dan kada 'yar rigimar tajiyoshi, aiko yana fitowa daga d'akin Fadila ita kuma tana fitowa daga d'akinta.
Da sauri ya 'karaso inda take ya had'a jikinsa da nata yayi mata ky'k'kyawar runguma, ita kuwa ganin ya fito daga d'akin Fadila yasata jin wani irin ba'kin ciki, ta bud'e baki zatayi magana yayi saurin had'e bakinshi da nata, hot kiss yake mata, yana romancing d'inta lokaci guda ta mance duniyar datake ciki.
'Daukarta yayi kamar wata jaririya, bezame ko'ina da'itaba sai bedroom d'inta ya kwantar da ita kan gado yacigaba, da aika mata da sa'konni, a ranar dai saida khaleed yasan Auta a matsayin mace, aiko Auta tasha wahala ba kad'anba, shikuwa khaleed banda rarrashinta ba abinda yake,yanata shimata albarka, sai gurin 'karfe d'aya da rabi bacci yayi awon gaba dasu Auta tana jikin khaleed duk ta wani shagwa6e mashi.
Kiraye-kirayen sallar asubah ne ya tashesu daga baccin da suke, khaleed ne yafara tashi yashiga  toilet d'in dakinta yayi wanka, sannan itama ya ha'da mata ruwa me dumi da Kansa yazo ya d'auketa yakaita toilet yayi mata wankan tsarki tare da gasa mata jikinta, sannan yasa sabulu ya wanketa ya d'aura mata towel ya d'aukota, kan gado ya direta sannan ya d'auko mata doguwar riga ta atamfa, simple ta sanya sannan suka gabatar da sallar asuba, bayan sun gama suka koma kan gado suka kwanta.
Wani sabon bacci yayi awon gaba dasu me cike da nisha'di da tsantsar 'kaunar juna.
.
Ahaka Fadila tayi kwana biyu tana masu girki, kullum daurewa kawai khaleed keyi yana cin abincin ba dan yana jin dad'insa ba, Auta ma daurewa kawai take dan ta lura da yanda shi kanshi me gidan yake cin abincin yana 6ata rai kamar yana cin magani, amma beta6a bud'a baki yace beyi dad'iba, saboda haka itama bata ta6a nuna kome ba.
6anagaren Fadila kuwa tayi mamakin yanda khaleed ke daurewa yana cin abincinta, wanda ko ita kanta data girka shi bata jin dad'insa.
Da misalin 'karfe shidda na yamma Auta ta shiga kitchen ta d'ora girki, kasancewar yau Fadila ta cika kwanakinta biyu.
Cikin tsari da tsafta da 'kwarewar girki Auta take aiwatar da girkinta, jalouf din shinkafa da makaroni ta dafa, Wanda yaji kayan lambu da kayan kamshi, da kayan d'and'ano na girki, hanta zallah tayi girkin dashi maimakon tasanya nama, cikin 'kan'kanin lokaci 'kamshin girkinta ya gauraye gidan.
Fadila na d'akinta taji k'amshin girkin Auta ya daki hancinta, take ta had'iyi wayu, dan tasan yau zasu debi girki, 
```{Kaji fadila iyayen kwadayi ansan aci da dad'i amma ba'asan a girka da dad'i ba }```
Haka Auta tagama girkinta ta kammala kome ta jera kan dining table, gefe kuma ga kunun ayar data had'a Wanda yaji dabino da kwakwa tun a gurin markad'en ayar, sannan ta zuba mashi sugar dai-dai kima saboda bataso yayi za'ki da yawa, ga kamahin flavor mai d'andanon ayaba, sai 'kan'kara data jefa ciki lokaci guda jug d'in yayi ra6a.
Da misalin karfe takwas da rabi suka hallara kan dining domin cin abinci, Auta ce ta zuba ma kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda suka d'ebi abincin suka kai bakinsu, Fadila taji dad'in abincin har cikin kwanyarta, khaleed kuwa lumshe ido yayi, yana taunar abincin cikin nishad'i ya kalli Auta yace " Zainab amma bayan kinyi candy kin shiga makarantar koyon girki koh?, Auta ta tuntsure da dariya tare dasa hannunta ta tallabo bayanshi, tace "bari ayima waigi kada ka fad'i daga kujerar, shima dariyar yayi yace "Allah kuwa da gaske tambayar ki nake, indai ba makarantar koyon girkiba yaushe mace zata iya tsara abinci haka wanda ko hotel baze kama 'kafarsaba, lokaci guda ta rage dariyar datake tare da gyara zama tace "wannan makarantar Hajiya ce, domin itace ta dage gurin ganin na iya girki kala daban-daban, tin daga na zamani har zuwa na gargajiaya, cike dajin dadi da nishad'i khaleed yakara kai abincin bakinsa, yace "Amma gaskiya Hajiya ta kyauta mana Allah saka mata da Alajannah Firdausi, Auta tace Ameen ya rabbi.
Fadila kuwa wani irin kishi ne ya tokare mata zuciya, lokaci guda taji bata iya cin abincin duk da dad'insa datake ji haka tabarsa.
Bayan sun kammala cin abincin, Auta ta zuba masu kunun ayar suka sha, nan ma saida khaleed yayi wani santin, Auta kuwa dayayi saita tareshi tace bari ayimashi waigi.
Fadila kuwa Auta tagama 'kuleta wani irin haushinta takeji,
    Auta kuwa ta lura da yanda Fadila ta 6ata ranta saboda haka, ranar dad'i har cikin ranta, basu wani dad'e suna fira ba Auta ta nuna tana jin bacci, haka suka tashi suka nufi d'aki tare dayima Fadila saida safe, itama d'akinta tanufa tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, cikin ranta tana ganin laifin momynta da bata koya mata girkiba, kodayake itama Momyn tata ba dakanta takeyiba masu ayki ne kemata koda kuwa dahuwar ruwan zafine.
Haka tacigaba da tunani kala-kala, daga 'karshe bacci 6arawo yayi gaba da ita.
.
washe gari da safe Auta ta had'a break fast, nan suka zauna sukaci kamar yanda suka saba, bayan sun kammala khaleed ya tashi tare da d'aukar makullin motarsa, yace "nizan wuce gurin aiki saina dawo, Fadila tace Allah kiyaye hanya ya kuma bada sa'a yace "Ameen, sannan ya kalli Auta yace "zan tafi amma zan dawo da wuri, inaso kiyi mani girki me dad'i wanda zesa kunnena ya tsinke, wani tattausan murmushi tayi mashi tace "zan yi maka girki me dad'i, amma ba wanda ze tsinka kunnenka ba, sai dai Wanda zesa kayi santi wanda yafi Wanda kayi jiya, yace to shikenan nizan tafi, ita ta d'aukar Mashi jakarsa tarakashi har bakin mota saida taga tafiyarshi tana daga mashi hannu harya fice daga gidan sannan takoma zuciyarta cike da farin ciki.
Fadila tariga ta gama 'kulewa da yanda koda yaushe khaleed ke yabon girkin Auta, amma ita idan girkintane yanaci yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta.
Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba.
Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da sauransu, ga kamshin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake.
Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa.
```{ kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}```
Da karfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya, wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan dining, Auta cike da nishad'i da jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya cokali, sannan ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido.
```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa```
Lokacin itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan komin dauriyar mutum baze iya cin saba.
Cikin tsananin rud'ewa Auta ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta *Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka, yaushe na zabga gishiri cikin abincina har ya wuce misali.
Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya bu'katar a can-cana maganar.
Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har gidan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special coaking .
Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wani sabon d'and'ano a zo6on wanda beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata motsawa daga inda take,
      Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi ya wuce d'akinsa,
      Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa,
    Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6aci, nan tashiga rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o.
Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki  wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Auta dani kike magana```~

0 comments:

Post a Comment