Thursday, 8 March 2018
Home »
'YAR KWALLIYA 1-END
» 'YAR KWALLIYA Page 11-15
'YAR KWALLIYA Page 11-15
'YAR KWALLIYA Page 11-15
.
Abu tace Kura kyaci da Gashi tobaci zakiyiba na me koya karatun higa wuta ne Yaron yace Gashi barina debo miki Abu tace yauwa na gode ga abincin me koya karatun higa wuta a hannun Binta zomuje Binta ba labari idonta nakan kwano baki a Bude Abu tace Binta kinga halin naki ko to cika dan Kibar sauran akwai abinda zanyi kafin yaron ya dawo Kan Abu ta gama magana harbinta tasa hannu tayiwa abincin wawan diba saida yayi rabi takai baki Abu tace kaiiii Binta kincinye ai bakomai zodai muje Binta tace nidai da zaki temaka kibani na cinye abincin yayi hegen dadi Abu tace Bazan baki badain sarkin kwadayi dake Binta tace Bakomai kome zakice kice kinsan idan naga abinci wani shaukine yake kamani sai naji hannuna yana rauwa Abu tace hannun yafadi kasa inyaso cine dai bazan baki kiyiba Abu tayi gaba wajan me abinci tabar binta da side hannun Abu tace me abinci kinada gihiri Eh Gashi Abu tayi murmushin tace nagode Tabude ledar gishirin ta zuba gishirin a cikin abincin tajuya dafa dikan shin kafa ne Ta mikawa me abincin sauran gishirin
.
Tace Gashi nagode Garuwan na debo miki Abu tace na gode ga abincin kakai mihi To yace yatafi kaiwa me koya karatun higa wuta Malam ga abincin Yace to jeka zauna kuyi sauri kugama nasa hannu To malam yaran suka ce Malam ya wanke hannu yabude abinci ya ganshi kadan be damuba ya sa hannu yadebo a abincin yakai baki cikin bacin rai yafurzar da abincin Kai a wurin wa kasiyo min abinci Abu tace Agurin me abinci nikuma na kyara maka abincin yanda zeyi dadi yakaji to Yace Keee nizakiyiwa haka kinsan nawa nasa nasiya kuwa Binta tace konawa kasa be da me muba badai ka daki Abu bako hmmm Me koya karatun higa wuta ya dauko bulala ya nufi gurin su Binta taimaza ta watsa run a hanyar da ze taka rai a bace ko gabanshi baya kalla sai Abu yana sa kafarshi santsi yajashi ya fadi kasa daliban aji suka sa dariya Cikin muryar tsawa yace kuyi shiru nace inba haka ba duk kanku sai kunyi kuka Abu tace mekoya karatun higa wuta a kasa yara kuyi dariya iya san ranku ba abinda ya isa yamuku Yace saikunbar makarantarnan yau din nan nake gaya muku Binta tace idan mubamu bar makarantar ba kaika bari Yace ko haka kuka ce Abu tace kwaraida aniya kaga tafiyar mu Binta tace Abu ina zamu
.
Abu tace gurin shugaban makaranta mana wanda yaya Nura yakaimu gurin hi dazu Binta tace hakane muje kafin ya rigamu Salama Alaikum Wa'alaikumus salam Fatima zainab yaba kwacikin aji yanzu bayan kowana malami na cikin aji Abu ta fashe da kuka Yace zainab meye na kuka kuma wani malamin ne ya da keki Sai Binta tafashe da kukan karya tace damu aka daka ai abin da sauki amma kamar kai wai za a wayi gari wani yana zaginka Yace ni waye kuma ya zageni Fatima Abu tace me koya karatun higa wuta ne yace hiwai ya gaji da aiki a karka hinka ba abinda kake bahi wahalar banza kawai yake maka nibama Wannan bane ya dameni tafashe da kuka Binta tace waikai baki ka ajiye katon ciki kana zaune kana sheniska sukuma kabarsu da yara suna henwuya idan yasamu dama saiya sace maka katon cikin ka dan mun masa maga munce mekai masa yake zaginka hine yace mufita mubar mihi aji Rai a bace yace ban gane malamin da kuke nufiba amma muje ajin naku na gan shi Binta da Abu na gaba yana binsu a baya harsuka isa aji Yanzu kai lawan abinda zaka min kenan duk irin abinda namaka da Wannan zaka saka min Me nayi kuma
.
Baka ma san kome kayiba ko meka fadawa yaran nan Ni lawan mezan fada musu babu wata magana da mukayi hasalima bakaga irin abinda suka minba yakamata akoresu daga makaranta karsu koyawa sauran yaran halinsu Idan ban Kore suba kaina koreka daga aiki irin wadan nan mugayen kalaman zaka jefeni dasu kaje na koreka Dan Allah karka min haka da aikin nan na dogara dashi nake ciyarda kanne na da mahaifiyata idan kakoreni inazani nashawuya kafin ka daukeni aiki Abu da binda sukayi dariya Abu tace su gaban maka ranta ayi mihi hakuri idan ya sake sai kadauki mataki To shikenan na dawo dakai Amma kar hakan yasake mai maita kanshi To nagode sosai insha Allahu hakan baze sake faruwa ba Shikenan nizan koma Fatima zainab kuje kuzauna To suka ce Yana fita suka kalli malam lawan Ya kaga aikin mu kayarda cewa mu zamu iya sawa a koreka cewar Abu Yace kuje Ku zauna
.
Bayan antashe su daga makaranta hanyanzu na komawa gida suka wuce kasuwa wasu maza suka tsaya a gaban su Abu tace lpy kuwa 1 daga cikin samarin yace Lpyar kenan shine kuka sa aka kori yayan mu sannan kukasa aka dawo dashi yanzu abinda kukeyi mukeji a gari ya fado gidan mu Binta tace ba abin mamaki bane dan kana jin lbr yanzu kuma yafado gidan Ku mu ai ruwan darene gama duniya Yace yanzun nan zamu koya muku hankali tinda Ku bakuda kunya Abu tace Allah ko sannu me kunya saika koya mana muna jira Binta tace jama'a ga barayin da suke muku sata dan munce zamu fada muku hine suka ce zasu dake mu Nanfa mutanan kasuwar suka zageye samarin suna cewa dama kuwa ansaba mana sata gashi yau Allah yatoni a sirin Ku Samarin sukace wlh muba barayi bane Dama zakuce haka mekuke jira da sune cewar Abu Nanfa mutanan suka rufesu da duka
.
Abu da binta cikin farin ciki suke Binta tatafi gidan su Abu ma haka Abu na shiga gida taga baban ta ya dawo Naji dadi daka dawo sannu da zuwa baba kaga yaya Nura yasani a bokoko awuta yauna fara zuwa amma sanda me koya karatun higa wuta ya dakeni cewar Abu Yace yi hakuri yar baba shikenan komai ya zo karshe ke bari na zokarshen zancen bazaki sake koma waba daga yau Abu tace Yasin naji dadi hiyasa banaso kana tafiya baba idan kana nan bame min fada komai nayi daidaine a gurin ka kuma nafi sakewa Saiki bishi kutafi tinda haka kikace cewar Inna Yace abin harda kishi yar baba shiga ki cire kaya kici abinci dan nasan wanka ba a yi danga qanshi naji zanyi magana da Babarki Tayi dariya Tatashi ta shiga daki Yace ina kike jiya mukayi wata magana da yayanki Alhaji nasiru Shine yasa meni yace meze hana nabashi Abu tayi karatu a birni kinga Amal tasamu kawa kenan shine nace ya bari nayi magana dake tukunna
.
Inna tace Ehhhto birni a kwai karatu nasani nasan kewa na damun Amal kasan cewar ita kadai ce mace a gidan su abin shine yardar Abu shine matsala dayanda zasu jure hala yanta a can dantani ba matsala wlh saidai yanzu Abu tayi qawa duk inda zata tare suke zuwa komaka ranta da Nura yatashi Atare yasa su Yace To wacece qawar tata dan nasan dole ya kasan ce kucakace irin ta Inna tace au dakanka kake ce mata kuca ka Ashe kasan kuca karce bari na kirata taji da kunnen ta Abu Yace bari mana yar baba yi zaman ki Inna tace daka bari nakirata ai bawata bace illa 'yar gidan malam murtala me rasuwa Binta
.
Yace Auzubillahi karki cemin binta gagare Sarkin kwadayi Inna tace ita dai Yace babu inda za aje da ita idan taje birni ai saita sawa yangidan hawanjini konida ba mazauniba nasan halin Binta amma kinyi kokari tab ya Abu take ita kadai balle an hadata da binta gagare Inna tace gaskiya baze yiyu kazo ka raba suba bacci ne yake raba Abu da Binta wani lokacin binta Anan take kwana abu ma tana kwana a gidan su shine zaka ce haka nasan yaya nasiru sarai bazeki karbarsuba yarike nawasuma balle Binta data zama yargida Yace to shi kenan Allah ya kaimu gobe muga yanda za ayi dan gobe yace zezo amma dan tani babu inda za a da Binta gagare Inna tace ya zaka dinga take halin 'yarka kana hango na wata idan har gaskiya za a fada Abu ma da halin ta dan harwanka tahana Binta Yace ina ruwan ki qawance baya yiyuwa sai hali yazo 1 yanzu kekinsan irin halinda Abu ta koya a gurin ta Inna tace A'a bansani ba Yace to gingani mubar komai dai se gobe in Allah ya kaimu
.
WASHE GARI Alhaji Nasir yazo tafiya da Abu Tin a kofar gida da Abu taga mota ta Tsaya tana shafa motar Abu tace I nama ace na higa cikin jirgin yan binni mu Anan daga amalanke sai keke sai jaki suko yan binni suna jin dadi Ta shiga leka cikin motar tana dariya Baban taya fito ne manta Yar baba aike nake nema zo kiga Kerere ta Tsaya a gaban su ta Ciro hudarda ke soke a kugunta tana shafawa Munzali yace Yar baba ga Alhaji nasiru yazone danya tafi dake birni Zabira tayi ta saki hodarda yake hannunta tace da gaske zani Binni barina kira Binta tazo mu tafi Kaiiii Yasin bazan yardaba hodata ta fahe yanzu mezan dinga sha fawa idan naje birni tafada tana kuka Alhaji nasir yace Yi shiru Abu ni zan siya miki wani idan munje birni akwai wanda yafi wannan a can sosaima Abu tace nidai gaskiya bazan yardaba bayan Ance Ku yan binni bakuda cika Alkawari nidai kawai kabani kudi naje na siyo wani Munzali yace Yar baba yazakice haka yan birni suna cika alkawari Wannan da kike gani shima mahai finkine yayan mahaifiyar kine kuma Amini nane sosai kodan lokacin dayake zuwa kina yarin ya shiyasa baki sanshiba Abu tace nidai ba ruwana abi yani huda ta kuma guda2 nake so daya ni daya Binta Alhaji Nasir ya Ciro 1k ya bata Waiyoo dadi dolema naje binni tahin farko nera dubu me yafi raina Bari naje na hado sa babbin kayan KWALLIYA ta yanda idan nayi KWALLIYA zan sumarda samarin binni da yan mata Munzali yace yar baba bari nafada miki idan kikayi Wannan KWALLIYAR taki a birni sai maza dubu sun suma hamsin sun mutu hamsin kuma suna gadon Asibiti inada tabbacin haka Abu ta gyara tsayiwa tana juyi Baba bari na fadawa binta tashirya mu tafi Yace yar baba wai Wannan Binta dakike fada kanwa tace kota Inna kekadai zaki tafi kina jiko Abu tace baba Nifa idan ba binta babu inda zani ehhhe
.
Alhaji Nasir yace wai wacece binta nan ne da Abu take nagana a kai Abu tace kawa tace baban ta ya mutu ita kadai ce a gurin ummanta Alhaji nasir yace Bakomai indan mahaifiyarta zata yarda sai mutafi da ita Bakomai Abu tace hine magana Nina tafi Gidan su binta Abu taje ko sallama babu ta shiga gidan tana kiran binta Binta tace gani lpy kike min irin Wannan kiran Abu tace jeki hado kayanki kizo mu tafi binni Binta tace anya Abu lafiyan ki kalau kuwa dasafen nan kiwani tasoda maganar zuwa birni nidai bazan kaiki ba kinji na fada miki Abu tace kinga bake zaki kainiba yayan Inna ne yazo ze tafi damu baki gan hiba tahin farko dubu1 yabani Binta tace jirani na hado kayana mu tafi dubu1 tab kice tin yanzu mufara canza tafi Abu tace Yasin kuwa muje na zabar miki kayanda zaki tafi dashi saboda canba qauyen *DARAUDAU* bane sonake mu haukatasu da sakaya da KWALLIYA Binta tace hakane muje
.
Suka shiga suka hada kaya sukafito Binta tace umma mun tafi binni sai nadawo kikula da kanki idan na tashi dawo wa zantaho miki da kayan dadi Umma tace Binta banganeba Waze kaiki birni niban sani ba Abu tace umma idan kinaso kiji gaskiyar magana dauko maya finki kizo muje kiji Haka ko akayi umma ta bisu suka tafi Abu tace kinga abinda zamu hau mutafi binni tanuna motarda Alhaji nasir yazo dashi Umma ta gaidasu suka amma tashiga cikin gida gurin inna inna tai mata baya nin komai umma ta amince Takuma yi musu addu'a tayiwa Alhaji nasir godiya data fito Abu gaba daya kayanta ta kwaso Innata an she ta zaba mata wanda yadace ta tafi dashi suka fito zasu tafi Abu ta jefa kayanta saman mota ta anshi na Binta ta jefa sama Abu tace kinsan su yan binni mutum 1ne aciki sannan duk wanda ze hau shikuma yana sama kicici bani na fara hawa shi kuma saiya cici boki au ga Inna nanma zata cici boki Binta ta ta ciciba Abu saiga Abu a saman mota Binta tace umma zoki cici bani nima Abu ta hau saura ni Kamar daga sama Alhaji nasir yaji maganar Binta yace acici bani Abu ta hau saura ni Dasauri yajuya yaga Abu a saman mota ta hakim ce Yan gari kowa yafito yana kallon su Abu sai wani yasina take tana shankan shi Alhaji nasir yace Abu sauko waya gaya miki nan ake hawa sauko Abu tace nasauko kace kafasa zuwa dani nafa San komai gameda jirgin nan Alhaji nasir yace zantafi dake sauko kiga Abu tace mezan gani Alhaji nasir yabude mota yace da Binta tashiga binta cikin tsoro ta shiga ta zauna sai taji ta lume da sauri ta fito Binta tace gaskiya a canza min mazauni ina zama yabude baki ze hadiyeni Abu tace nasani ai hi yasa nai zamana Anan kinga Wannan baze taba fada miki gaskiya ba miko hannun ki na janyoki muyi zaman mu Anan Binta ta mikawa Abu hannun abuna janyota Alhaji nasir yace malam munzali da alama sai kasa bakifa Munzali yace yar baba sauko kiga nan ake shiga ba saman mota ba Abu tace baba nayarda dakai barina sauko amma kanaji Binta tace yabude baki ze hadiyetafa Yace ba hadi yeta zeyeba kasa yayi saboda tazaun zoki shiga ki gani
.
Abu ta sauko da kayan su itama ta sauko Abu tashiga tazauna tace baba hakane nazauna Binta shigo Binta tashiga ta zauna tace kawata yakika ji gurin dadi ko danma bamuje canba Abu tace hakane dole idan munje mu nuna musu munsan komai dan karsu raina mu Binta tace to Sanyi sukaji yana shigarsu tako ina suka hau kerma abin bemusuba sukasa ihu suka fito Alhaji nasir da malam munzali dasuke sallama hankalinsu yadawo gurin Abu da binta Alhaji Nasir yace lpy kuka fito Abu tace baba nagane hidai Wannan mutumin bakin ciki yakeyi damu yasan munfi yan matansu na binni haduwa hine ya turo mana jaura dan muce mun fasa Munzali ya kalli Alhaji nasir Alhaji nasir dariya yayi yace AC ne a kunne bari na kashe tinda bakwa so amma ni ban turo muku jauraba hasalima ni ina so kuje birni Ku wayar dasu Alhaji nasir yakashe AC yace kushiga nakori jaura ta bakin naku Alhaji nasir yayi sallama dasu yashiga mota yaja suka tafi Yan gari murna ya cikasu ganin Abu da binta zasubar gari har motar su Abu ya bace yan gari basu dena daga musu hannu ba Kome Abu da binta suka gani sai suyi ihu su buga mota harsuka karasa gidan megadi ya bude musu gate Alhaji nasir yashiga da mota yafaka ya bude musu mota yace su fito Koma gana Abu da binta sun kasa Tsaya wa sukayi suna kallon gidan babban gidane tsayawa fadan haduwar gidanma qauyan cine Amal da hajiya mariya matar Alhaji nasir da gudu suka fito Amal da gudunta ta taho zata rungume su tana zuwa taji kanhin tiraren jikin binta da Abu a haka ta rungu mesu tana murna Amal tace sannunku da zuwa tinda nasamu lbr zuwanku na sa aka gama komai da wuri kuzo mushiga ciki kuyi Wanka kuci abinci
.
Abu tace Wanka tab bakiji kanhin tirarena bane Amal tace banjiba saidai naji wari Abu ta dunkule hannu zata kaima amal duka binta tarike hannun Tace Abu gidansu kika zofa kiganar da ita idan taki ganewa saiki ragargaji bakinta nida kaina zan tayaki Abu tace kinci sa a kufa yan bin tsiyata daku hirme warin da kikaji ba wari bane qanhine zokiji Amal ta matso Abu tace rabona da wanka harna manta Hancin Amal ha toshe har Abu ta gama magana Amal tace naji kuma na gane kuzo mu shiga ciki
.
Abu da binta suka kalli hajiya mariya suka ce ina wuni Hajiya mariya tace lpy kalau Abu tace naka gu naga cikin gidan nan yasin binta gani nake kamar na higa haljan na Yasin Wannan yayan Inna dan bakin cikine yasan da Wannan gidan a duniya yaki yazo ya daukeni sai yanzu dana Riga na girma a qauye datini bansan kiba Binta Binta tace nikuma naji dadi dabe zo ya daukeki da kina karamaba daya daukeki da kinmin bakin cikin zuwa binni dubafa kiga girman gidan nan bantaba Tina nin zanzo hiba yausaiga Binta a ciki Abu da binta na tafiya suna hirar gidan Hajiya da Alhaji suka shiga Amal na bayan Abu da Binta Amal tace kushiga mana Abu da binta suka kalli juna tiles ne baje a falon gidan Binta tasa kafa Abu matasa suna tafiya santsi na jansu suka zube kasa Abu tace daga nan bazan dara ko inaba Binta tace nima haka muna tafiya yana janmu dan hihigi Abu tace gaya mata dai Binta kalli kiga hoton ki a nan tanuna mata tiles din dake kusa da ita Binta tace hi Wannan banda tafiya da mutane har hoto yana dauka laaaaaa kalli kiga kema gaki a nan Amal tace dan Allah Ku bari tiles ne baya tafiya da mutane kutashi kuga Abu tace Yasin daga nan bani zuwa ko ina bayan a gabanki yatafi damu bakice komai ba Amal tace to shi kenan zan mishi magana yanzu kutashi Binta tace kai Nifa jinake kamar nakawo kaina inda zan sha wuya daga zuwa naci karoda Wannan abin ze tafi dani gaba kuma mezan gani Amal tace ba abinda zaki gani kuma nadau Alkawarin yiwa komai na gidan nan fada Abu tace dagaske Amal tace dagaske mana nidaku yanzu kawaye ne kutashi Abu da binta suka tashi suka tsaya Cak ganin basuda niyar tafiya yasa Amal ta shiga tsakiyar su ta rike Hanna yen su tafi dasu ta zaunar dasu a kan kujera ta kunna musu kallo Amal tace ga kallo na kuna muku kuyi ina zuwa bari nakai muku kayanku dakin ku yanzu zan dawo Binta sukayi da kallo basu ce komai Ba suka maida hanka linsu kan kujera suna daddan nawa suka shafo tiles din Binta tace Abu kinsan me Wannan shine Aljan nar duniya da malam rabi'u yake fada mana kintuno Natuno mana saidai kinsan me yanzu kanhin titaren jikin mu zeyi Amfani sosai ma cewar Abu Binta ta kalli TV tasa ihu tana nuna shi da dan yatsa Abu ma ihu tayi hajiya, Amal, da yan aikin gidan Asibi da kande suka taho gurin su da gudu hajiya tace Abu Binta lpy meya faru Abu tace hajiya Aljanune suka Bude mana ido muna kalla mukaga wani gabjejen kato ya kaiwa wani nauhi sai dukansu yake daga karshe ya dunkule hannu zekai mana nauhi kamar haka Abu ta dunkule hannuta tayo saitin hajiya hajiya ta sunkuya Abu ta samu kaiwa Asibi naushi a baki Amal tace Abu kinfasa mata bakifa
,
Hajiya tace nashiga3 alhaji kakawo mana aiki Binta tace ba laifinmu bane laifin Aljanun canne susuka Ja komai harmu har doke doken mu munga wayanda suka fimu Amal tace Asibi muje ciki yi hakuri Hajiya tace ku bata hakuri Sukace yi hakuri Hajiya tace ba aljanu bane kuje Ku zauna Binta tace tab babu inda zani sun dunkule hannu zasu nau hemu mun kauce kice mu koma Abu tace fada mata dai ga hican yana kallon mu da alama mu yake jira muna zuwa hi kenan ba lbr Hajiya taje ta kashe TV tace kuzo kuzauna nakoresu sun tafi Binta tace gaskiya a canza mana gurin zama sabo aljanunnan zasu dawo inada tabba cinhaka Amal tazo tace kuzo muje Amal ta kaisu dining Abu tace ina ne nan kuma nasaba ganin idan za ayi tafiya sai anhau mahin Ku kuma da kafa a ke zuwa nan Amal tayi dariya tace bawani tafiya bane me tsawo shiyasa kika ga haka Binta tace Abu Yasin idan Akazo rabani da Wannan Aljannar za a shawuya dan nahigo kenan ba inda zani nida *DARAUDAU* sai ziyara Abu tace ke kenan ni ko ziyara bazan jeba duk wanda ya matsu yazo ya ganni damuwata 1 yaya Nura,inna da baba Amal tace Ku zauna muci abinci bayan mungama na zagaya daku kuga dakin Ku da gidan gaba 1 Abu tace bayan nan akwai wani unguwar da zamu tab ba inda zani idan bada jirgin yan binni ba Amal tace shikenan dai Ku zauna zansan abinyi Amal ta zuba musu taliya da miya da na man kaza Tinkan Amal ta gama zubawa Binta take hadiyan yawu tana gamawa Binta ta danki naman kaza tana ci Amal kallon su kawai takeyi tana dariya Abu taliyar take kalla fuska a yamitse tace yan binni da kwada yintsiya tsutsar ma cikuke Abu ta kalli binta dake danbe da naman kaza Amal tace Abu ba tsutsa bane taliyane yanada dadi sosai cikiji Kai bada niba ko a qauyan mu daga akuya sai kaji zabo tantabara agwagwa sune Abinda nasan Anaci banda tsutsa kikawo min tuwo danmalele ko dan bagalaji waiyoo dadi saikin bani lbr cewar Abu Amal tace kici Wannan yanzu kafin nasa a dafa miki abinda kika lissafo To bari na gwada
.
Tasa hannu ta debo taliya takai baki ta fara tauna ta furzar da shi Tace tab Yasin bazan iyaba kibani tsutsa da ranhi da komai inaci yana motsi gaskiya yan binni bakuda tausayi Abu Wannan fa ba tsutsa bane kamar yanda kike Tina ni amma Bakomai muje kisami Asibi kifada mata abinda kike so a dafa miki Sai lokaci binta ta dawo cin hanka linta bayan ta cinye kaf kajin gurin tana gyatsa tace dadi binni wai bani komawa ko ina zama dis saita fashe dakuka waiyoo umma tana can tana fama da tuwo tafada da muryar kuka Ta kalli abincin da kyau ta fasa kara ta koma bayan Amal Binta tace gaskiya bazan iya cin tsutsa ba nadai ci kaza zan iya zama daku amma abinda nake ci kubakwa ci shine kawai matsala Amal tace karki damu shima zaki saba dashi zo muje Takaisu gurin Asibi suka fada mata abinda zasuci tace su bata lokaci kadan zata dafa ta kawo musu suna fitowa daga kitchen Amal tace kujirani Anan karkuje ko ina ina zuwa nazo na za gaya daku Amal ta tafi Abu tace mutsaya kar muje ko ina karya ma kenan binta biyoni Suka fara tafiya suna Kalle kalle Abu kinsan me fasa har kawunki a dakuna ta kare kalli kiga irin dakunan dake gidan nan nasani mutanan garin nan gaba1 Anan suke kwana sun fita Neman abinci anjima zakiga gidan nan yacika da mutane Abu tace Yasin be birgeniba dayabar su Anan daya musu a wani guri daban sukuma su zauna Anan Binta tace Abu kinji abinda nake ji kuwa Abu tace naji wakar daga daku nan nan2 suke fitowa saidai ba irin wakarda mukeyi a dandali bane Wannan yafi dadi Yasin Tana fada tana rawa Binta tace sosai ma bazaki hadaba binni yafi qauye kalli gidan nan kamar gidan sarki hiko me gari gidan muma yafi nahi kyau Abu tace nidai zan higa dakin nan naga waye a ciki ke kuma ki duba dakin nan To hi kenan
.
Abu ta Bude tana lekawa da bataga kowaba saita shiga sautin wakar nashigarta tafara rawa Binta kaitsaye data Bude ta shiga lemo ta gani a ajiye a cikin Kofi ta dauka Tace giyar yan binni barina sha abina meyafi raina ba yaya Nura balle yamin fada cewar Binta takafa kai tana sha tace dadi gaba daya zan shanye takai baki tana sha Me zan gani haka yadaka mata tsawa yace me kikeyi Anan cewar Arif Binta najuyowa saboda tsoro ta fesa mai lemon bakinta Kai keee ni kika fesawa lemo wacce ke tukun nama dahar zaki fesa min lemo kinsan koni waye kuwa cewar Arif Binta tace kokai waye be dame niba wa yace ka tsora tani Arif yace haka zakice ko Binta tace kwarai da gaske Arif ya nufo inda take yace ke warin me kikeyi Binta tace kut Yasin yanzu bakinka zeyi jini indai kasake cewa wari kudama yan binni kwai rainin han Kali Arif cikin tsawa yace fita kona dakeki kowaye ya kawoki gidan nan ma oooho Abu rawarta kawai takeyi tsabar dadin wakar yasa ta danne danne harta kara sautin wakar Waye waye a nan Yaji ba a amsaba yace sister ba a amsaba yace Amal shiru saiya fito da kanshi MaMaki yakeyi yanda akaita shigo yaje ya kashe wakar yace me kikeyi Anan fuska kamar Aljana kifadamin Aqeel ya fada cikin tsawa Abu tana rawa dukda ya kashe wakar take cewa duk inda ake kida da waqa kirana ake dan haka wakar kace ta kirani Aqeel ya toshe hanci kinga dadawar cikin gida zaki kai sune masu amfani dashi ba niba Abu tace a ina kaga dadawa kuma kanhi dai gaskiya kanada babban sa'a tinda kaji kanhin tirarena Aqeel yace tirare karkice daga jikinki warin nan yake fitowa Wari Yasin karka bari na fara dakai karka sake cewa wari kanhidai Wari ko kanshi beda meniba fita daga dakina kokuma na yankaki Eh yankani zaka aikata dantinda naganka naji tsoronka Ashe kisa kake Aqeel ya dauko wukarda ya yanka lemo dashi ya rike a hannu Arif yace bazaki fitaba ko duka nakeyi kuma dukana yana karya mutum koma ya mutum Eh karka kasheni zanfita Arif yace fita cikin sauki kona dauko abinda nake duka yanzu na fasa miki jiki Abu tace kakasheni a kasheka amma dai kabarni darai zan fita Aqeel ya biyo abu da gudu Abuta fito Arif yabiyo Binta da gudu Binta ta fito Abu ta kalli Arif Binta ta kalli Aqeel Atare suka kurma ihu mai kara suka rungume juna Abu na nuna Arif Binta na nuna Aqeel
0 comments:
Post a Comment