Wednesday, 7 March 2018

YAR KWALLIYA Page 6-10



'YAR KWALLIYA Page 6-10
.
Can saiga Binta ga gare sarkin kwadayi da umman ta suna ta howa    Yauwa Allah na gode maka ga binta cewar Abu     Dan rainin wayo da sassafen nan a aiko gidan mutane ace suzo ko uwar me za a mana cewar Binta   Abu tace Kema dai kya fada gamunan ana surfo mana zancan banza  Eh waye yake zancan banza ke kuma Binta ba a koya miki gaisu waba bakya ganin manyane a gurin nan cewar liman dake zaune a gefen me gari  Binta da umma suka samu  guri suka zauna  Abu tace Wanda yatsargu dahi nake   Babba bangan shiba saidai naga me gari tinda ba a barni naci abinci ba nazo nan to kowa yayi hakuri da abinda zeji koya gani cewar binta  Liman yace kaji yara da rashin kunya   Barsu dani liman cewar megari  Umma ta gaida me gari binta kuwa aikin gun guni kawai takeyi  Sauran mutanen gurin hanci a to she sun kasa cewa komai daga liman sai megarine kawai suke magana  Binta kinji wai dan mun daki wa yancan 'yaran hine aka kawo mu nan gasu 'ya'yan kuli da mai  cewar Abu  Binta tace Kan uba Yasin bazan zauna ba akan su aka hanani cin abinci tafiya zanyi    Yasin karki yarda binta kanki tafi kizo ki daki rabon ki zan taya ki cewar Abu   Sukayi kansu zasu daka liman da megari mutuwar zaune sukayi wato kanhin jikin Abu dana binta da itama tafara hawa layi sukaji sukayi lup kamar basa gurin  Megari yace Karku sake Ku tabasu kuna jiko wai warin me nake ji haka ina kuke kusa baki mana meye aikin ku liman      Caraf Abu tayi da cewa nice nan kanhin tirarena babu inda baya zuwa megari ka gode Allah tinda kaji kanhin tirarena  Megari yace Tirare kuma tab Wannan uban warin shine tirare   
.
liman ba lbr yakasa cewa komai sai kallo da ido sauran ma sunyi shiru   Megari cikin bacin rai yace waime nake gani haka kun dena magana ne kuma banson sha shanci kunwani zuba min ido me kuke nufi  Me gari sai hakuri binta Abu kuzauna cewar inna da umma  Binta hannu a dun kule tana shirin kai naushi take   cewa Inna kubar mu dasu yanzu mu koya musu hankali  Nura cikin muryar tsawa yake cewa kuzauna karku bari na kara magana   Ganin fuskarshi ba alamar wasa yasa suka zauna   Megari yace gaskiya yaran nan abin naku azimun ne kuma da laifinku wajan bata yaran nan kuduba fa Ku gani baruwansu da babba koyaro duk wanda ya musu yi mishi zasuyi  Me gari ayi hakuri zamu gyara insha Allah cewar umma  Me gari yace To shi kenan gaskiya kudau mataki inba haka ba ni da kaina zandau mataki  Wani yaro ya fito daga gidan me gari hannun shi rikeda samira  Tinkafin ya karaso Binta sarkin kwadayi tafara hadiyar yawu wayanda suke kusa da ita saida sukaji karar  Yaron ya gaidasu ya ajiye kwanon a gaban liman    Binta idonta na kan kwanon ko kiftawa bata yi ta janyo kwanon kusada ita   Kanshin abinci yadawo da liman daga dogon suman da yayi  Liman yace Ke me kike nufi yajanyo kwanon gaban shi  Binta ko magana ta kasa hankalinta nakan kwanon  Liman Allah ya yanka maka binta taga abinci ranta ya biya dan haka ka bata taci cewar Abu  Liman yace In naki fa dawani bakinki dayake zuba wari anya kina wanke shi kuwa  Abu tace Yasin wanke baki kahe hakori yake hiyasa bana yi liman kaida kanka kace hi bakin me azumi kanhin Almuski yakeyi hiyasa   nima na dena wanke baki saboda Almiskin yazauna a bakina nafita daban daku nawa basai ina azumiba ta fada tana  Dariya  Liman baki yasaki yana kallon Abu   Megari yace ke Abu anya kina da kai kuwa  Abu tamika mishi kanta tace shafa kaji   Inna ta rufe bakinta tana kallon Abu  Megari ina fada maka saika dauki babban mataki akan Abu da binta cewar liman  Bakomai kubani lokaci zansan abinyi kuna iya tafiya amma kubar binta da Abu liman ze musu fada cewar megari  Waaaanii gaskiya babu abinda zan iya fadawa wayan nan yaran banshirya takun saka da suba sunyi nisa basa jinkira cewar liman  Yi shiru liman nagama magana cewar megari  Inna,umma da Nura suka tafi  Binta batama San tafiyar suba itadai burinta taji abinda ke cikin kwanon a cikinta  Liman kabata abincin nan taci yasin tanada cutar duka idan aka hanata abinda takeso hine suke tahi cewar Abu  Liman Ya kalli binta dake zaune hannu a dunkule ido akan kwano tana sude baki  Liman yace Me gari Abuya tabbata duka zatayi kalli kaga 
.
Liman karka zama soko mana kayi musu fada sutashi su tafi ita kuma binta ka bata taci cewar megari   Kwanon ya miki mata ta ansa tabude tana ci kamar kura yaga nama  Binta ta gama ci tasa kafa ta ture kwanon ta kalli 'yar me gari tace jeki kawo min ruwa  Niii kalle ni sama da kasa nayi kama da 'yar aikin gidan Ku cewar yar me gari  Zancen banza meye dan kin debo min ruwa yan matan garin nan kaf yan aikina ne saboda na fisu haduwa cewar Abu  Ya isa kunutsu kuyiwa kanku fada kungirma aure zakuyi gidan wani zaku kuyiwa Allah kudena abinda kukeyi   Dariya suka yi suka tafa kinji wai aure cewar Abu  Binta tace kaika sanshi nidai tinda ba a bani ruwaba bangode ba taso mu tafi   To tace suka tashi zasu tafi       Binta tarike ciki tace washiii cikina ya motsa      Binta tayi nishi saiga tusa ya biyo baya   Megari yatoshe hanci yace liman Sa a kamo min yarin yarnan   Binta da Abu najin haka suka sa gudu           
       
   ****      
  *WACECE BINTA DA ABU*  
ABU 'yace ga munzali          malam munzali fatauci ne sana arsa shikadai yake tafiya inya tafi saiya jima kafin ya dawo sai matarsa Suwaiba yaranta na kiranta da Inna yaransu 4 Ramatu itace ta farko tana aure a garin da suke me suna *DARAUDAU* sai zulai itama tayi aure sai Nura da Zainabu Abu itace auta        
ABU yarin yace mara tsoro duk girman mutum inya mata saita mai farace tas amma qazanta ya maida ta baka dan qazanta kokitso intayi saiya dankare layin ya bace kafin inna tai mata ta karfi ta tsefe   Binta 'yace ga murtala             Malam murtala mahaucine Allah ya masa rasuwa tin Binta tana karama a hannun ma hai fiyarta ta tashi sunan ta Baraka binta kadai ta haifa    BINTA  yarin yace mara nutsuwa ga kwadayin tsiya idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi itama bata barin ta kwana dan haka tasu tazo 1da Abu gasuda taurinkai                  
  *****   
Binta da Abu na cikin gudu wata yarinya kanta dauke da buhu ta tsaya a gaban su ta shaki wuyan Abu      Ke meye haka a ina nasanki cewar Abu  Tace idan maye ya manta uwar diya bazata mantaba nice wadda kika daka kika cimin gyada kika kuma zubarda sauran   Abu tace Kinsan abin da yawa yanzu me kike nufi da kika shaki wuyana  Dukanki zanyi na kwashi saura nakai gidanku cewar yarin yar  Banga Alamaba ance da kuturu a gama lpy ni Abu banga wanda ya isa yamin abinda kika fada ba ba a hai fehiba   Binta tace ke ware inba haka ba hmm jiki zeyi tsami  Ke waya sa dake ni din nan da kike jida gani ban tinkare kuba saida na samo makarin ki ke binta dan nakula kema matsalace ta daban cewar yarin yar  Makarina kuma ni binta banganshiba anan gurin yau banga abinda zesa na bar kiba batareda na sosakida bulala ba  Ko to shikenan nida ke za a ga me gaskiya yarin yar  ta Bude buhun taciro goriba,kurna,magarya da gyada   Tinda ta Ciro Binta ta hadiyi yawu kamar yanda ta saba tabi hannun yarin yar da kallo  Abu tace Ke karki sake ta rudeki da abin hannunta Binta nizan siya miki fiye dahi   Ko jinta binta bata yiba Tamika hannu alamar ta bata harya rinyar ta miko mata saita janye  Binta tace meye haka kuma bana son irin Wannan  Kina zaton kai tsaye zan baki batareda na kafa miki doka ba   Meye dokar cewar Binta  Yarin yar tace zakiyi Alkawarin cewa bazaki sa hannu a fadana da Abu ba inkikasa hannu zan kwace abina  Binta ta kalli Abu ta kuma kalli ledar hannu yarinyar da irin abinda ke ciki  Nan tashiga raba idanu               
.
   Jikin Binta sai rawa yake   Na amince bani   Yarin yar tace in na baki ki tafi ko juyowa karkiyi  Binta tace to bani dai    Tana ba binta tawuce ta tafi  Yarinyar tace yanzu daga ni seke     Abu tace hakane kuma zam miki dukan tsiya kamar mu2 muka miki   Yarin yar ta kama Abu da duka Abu na ramawa Abu ta Bude baki ta sakar mata cizo a hannu   Waiyoo kika cizeni Yasin bazan yarda ba koni koke a gurin nan cewar yarin yar  Saukar duka yarin yar taji bazata koda ta juyo Binta ta gani zatai magana binta ta dauketa da mari binta da Abu  sukayi mata taron dangi saiga   yarin yar a kasa wanwar tana kuka Abu ta bude buhu ta leka taga garin tuwo tayi dariya Binta ta daga ta juyewa yarin yar a jiki   Inkinje gida saikiyiwa tsohuwa bayani yanda Akai da garin tuwo cewar Abu  Suka tsalla keta suka wuce   Binta tace Abu kina jin abinda liman yayi mana dan yaga me gari waimun girma aure zamuyi  Rabu dashi nasan abinda za muyi mihi damu yake magana ba a taba mubama munyi fada bare ka ta bamu zomuje cewar Abu  Ina zamu cewar binta  Zaki gani cewar Abu  Koda suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidan  liman  Abu tace Sallama Alaikum goggo me tuwo   Goggo me tuwo ta amsa da Wa'alaikumus salam Abu Binta yaukune agin namu   Eh wlh cewar Binta  Goggo me tuwo tace Gashi kuma ban gama tuwonba yanzuma na dora   Bakomai mu abindaya kawo muma daban ne bansan ta yanda zanfara fada mikiba goggo cewar Abu  Kar kuji komai kufada min idan baku fada minba wazaku fadawa bayan nasan Ku tin kuna yara nan kuke zuwa cintuwo cewar goggo  Binta tace Hakane munsan da wannan goggo hine dalilin da yasa mukejin nauyin abinda zamu fada miki  Binta Abu kufada min bakomai komai girmanshi zansan abinyi  Abu tafashe da kukan karya taceTo hikenan goggo kiyi hakuri da abinda zakiji sai Abu takara sautin kun da takeyi  Binta ma kukan karya takeyi tace yi hakuri Abu bakomai sakai yar daze mata kenan  Nanfa hankalin goggo ya tashi tace kunga kufada min duk kunbi kun daga min hankali  Abu tace goggo dagir manki da komai liman ze miki kishiya  Gogo ta mike tsaye tarike kirji tana huci      
.
Ni liman zewa haka zezo ya sameni bemin kishayaba tin ina yarinyata saiyanzu dana tsufa  Goggo abinda ze kara daga miki hankali hine irin kalaman da yake mata idan yaje zance cewar binta tafada tana kuka   Dan rahin mutunci hine ta aiko mu da kala man soyayya muzo mu fada mihi Takuma ce karya manta yau yazo zance ita kadai tasan abinda ta tana dar mihi cewar Abu  Kafar goggo ya haurawa taji juwa na ibanta tajin gina da bango ta ciji lebe   a nan gidan ze kwana daiko badamuwa ina jiranka cewar goggo  Binta takara sautin kuka tace babban abin hine mahaifin yarin yar yace liman yaturo anbahi ita   Suna fada goggo ta zube kasa ba nunfashi   Munhiga 3 Abu munyi kisa cewar binta  Abu tace ke bata mutuba tsabar kihine kawo ruwa kigani   Binta takawo ruwa Abuta watsa mata taja dogon nunfashi tabude ido tana  Cewa ina yake kumiko min shi  Abu tace goggo aibaya nan bari zahigo saiku yita takare  Goggo tace bakomai zaka dawo kasa meni liman nida kaine yau agidan     Goggo mu zamu tafi   Nagode muku binta da Abu Allah ya muku Albarka  Goggo me tuwo macace me kishi akan kishi zata iya yin komai sanin hakane yasa Abu da binta sukazo gurinta sunsan ita zata hukun ta musu liman yanda suke so  Ameeen goggo aiyiwa kaine suka ce suka nufi hanyar fita harsun sa kafa zasu fita Abu ta gano liman yana ta howa da alama gidan zezo da sauri ta riko binta suka boye cikin wani duhuwa dake zauren gidan liman  Liman yayi sallama ya fada gida kai tsaye ya nufi bandaki   Goggo na jinshi        binta da Abu Suka dauke sawun takalmi suka matso tayanda zasuji kuma suga Abinda ke faruwa  Liman yafito yashiga daki yasa sababbin kaya yafesa tirare  Nanfa kishi ya turnike goggo me tuwo tashiga waigen Abinda zata samu tarike ta hukun tashi dashi  Me gari ya fito yana gyara hula yace in na kike na fito zan tafi  Goggo tafito tana huci tace nasani kagai sheta wato danka raina min hankali nika ajiyeni a gida kaikuma ka fita kana neman aureko har ance katuro  Yace ni liman a ina kikaji zan cen nan wlh bana ne man aure a ko ina ni liman ke kadai kin ishe ni  Tace karyar banza ba abinda zaka fada min na yarda bayan nasan komai yanzu kayan nan dakasa kafesa tirare ina zaka  Abuda binta na labe suna ji kuma suna ganinsu suna dariya  Yace daliban malam rabi'u ne zasuyi sauka yau shine aka gai yace ni  na shirya yanzu zan tafi     Bata gamsu da abinda yace ba yasa tafara buga kafa tana tsaki   
.
Tace malam malam ni goggo ni zakai wa kishiya     Tana juyawa taga murhuna cida wuta ta Ciro icen dayafi ci tasa mai ababban Riga wuta yafara ci liman na ihon temako yana kokarin cire baban riga dakyai ya samu ya cire abin beyiwa gogoba ta dauko tukunyarda ta gama hada kayan hadin miya ta kwaramai a fara ren kayan shi   Binta da Abu dariya harda faduwa   Ta rarimo bokiti tana jifan shi dashi ganin abin nata bana Kare bane yasa liman ya mike ya zuba da gudu  Binta da Abu suka Tsaya a gaban shi        Abu tace liman mun girma aure zamuyi ko toga auren mun  gwada maka tafada tana dariya  Binta tace waiyoo cikina liman mezan gani haka yazaka gudu kaida yadace kai mata fada kamar yanda kayi mana dazu   Amma dai yaran nan kwai shedanu kune kuka hadani da matata bakomai dani kuke magana  Abu tace gogo me tuwo gashinan   Liman yasa gudu binta da Abu na dariya  Raina fesa cewar binta   Duk wanda yace ze higa harkarmu to yadebowa kanhi kwarkwasa cewar Abu  Sukayi dariya suka tafa   Suka nufi gidan su Abu  Liman be tsaya ko inaba sai fada gurin me gari wayanda suke tareda megari ganin liman yashigo da gudu suma suka mike zasu gudu  Megari yace kudawo Ku zauna liman mezan gani haka da girmanka da komai   Allah yabaka yawan rai ai duk abinda ya sameni kaine sila saida nace ba fadan da zanwa Binta da Abu kace kaisam   saina musu gashi abin daya jamin dagir mana da komai na yanko ta cikin unguwa da gudu kowa na kallona   Yanzu binta da Abune sukai maka haka a garin nan cewar me gari  Liman yace hmmm ni nasan su sarai shiyasa tin farko naki kadage kace sainayi yanzu gurin saukarma ba halin zuwa   ta kona babban rigar sukuma wayan nan kaga dai yanda tai musu harda manja a jiki kamar za a Kada miya gashi badamar na koma gida yanda ranta yake a bace  Kai kutashi kuje Ku ne mo min su  A'a kudawo Ku zauna Allah ya baka yawan rai nayafe Abarsu kawai nidai goggo me tuwo itace  kadai damuwata ita taimin hakafa 
.
    Nan yakwashe duk abinda ya faru yafada wa megari  Shine zakace a barsu gwara mu koya musu hankali cewar megari  Eh Bakomai a barsu cewar liman  To shi kenan zansa a kiramin gogo me tuwo zan mata bayani karka samu damuwa   To shikenan godiya nake Allah ya baka yawan rai  Kai tsaye suka shiga gidan ba sallama  Yaushe zaku girma abin naku kara lala cewa yakeyi ko Abu da Binta cewar Inna  Saida suka samu guri suka zauna sannan sukace salama Alaikum  Inna tace Allah nagode maka binta da Abu Nura yatafi maka rantar boko   Yinme inna cewar Binta  Inna tace Yaje saku a maka rantar boko daga nan yamai daku isilamiya dan harda rashin ilimi a abinda kukeyi   Abu tace Boko tab ba inda zani Inna bokoko awuta kike nunfin zamu toko su yan bokokon Awuta tsoron bokon sukeyi ba inda zani saidai ko binta gata nan   Waaaaniii tab namutu Allah yasani awuta ba bokon da zani cewar Binta              
.
Wlh baku isaba haka kuke so mu zauna daku a jahirce cewar Inna  Yasin bazani ba wuta tsilim cikin sauki bokoko Awuta bada niba cewar Abu  Binta ta tashi daga inda take ta koma kusa da Inna  Tace Inna kisa baki akahe maganar nan dan baze taba yiyuba Yasin haka kawai ze Kaimu lahira da kanhi  Kanshi kanshi inna taji yana tashi A jikin Binta  Tato she hanci tace Binta warin me nake ji haka kardai kema kinhau layin rashin yinwanka  Dariya Abu tayi tace Inna nice nan nadorata alayi tam bayeta kiji ita kanta tafijin dadin jikinta yanzu fiye da da  Rufemin baki sakarai qazama nayi dake *'YAR KWALLIYA* Binta kiyiwa Allah karki bari Abu ta koya miki rashin Wanka da Wannan maya taccen KWALLIYAR nata  Inna saidai kar a kuma dankuwa karatu yamin qanhi yabi jiki bakiga irin kallon da megari yake minba nikadai nagane meyake nufi cewar Binta  Abu tace Nagani rabu dahi binta ze fado hannu banda hima ya tema kawa kanhi besa bakiba aida tuni munkoya mihi hankali kamar yanda muka koyawa liman  Oohni Inna ina zansa kaina nan nasamu lbr anga liman yana zuba gudu a gari har ana zaton ya Hauka ce ashe ba Hauka cewa yayiba gamo yayi da 'ya'yan Aljanu binta da Abu babban  gamo yai cewar Inna    Abu kwaso kayan KWALLIYAR muyi muje gidan Amaryar da aka kawo nan bayan layin ku cewar Binta  Abu tace Hakane fa banjeba kuwa   Tashiga ta dauko ta ajiya a gaban binta  Inna tace shiyasa tin farko banso qawan cen kuba wlh nasani sarai cewa abinda kuke da NA yanzu saiya fishi kuma gashi na gani   Suka kafe inna da idanu   Inna tace bance komai ba ni badaku nakeba Allah yabaku hakuri  Suka juya suka cigaba da  KWALLIYA  Salama Alaikum inna nadawo  Wa'alaikumus salam gonda da Allah ya kawo ka   Yi shiru Inna nasamu lbr komai inaji nasan sune zasu aika tawa liman haka komai yazo karshe na sasu amaka rantar boko hakama isilamiya ga kayan maka rantar nasu   Alhamdulillah shikenan kurinkus kandan bera boko Saikun je kokuna so ko ba kwaso cewar Inna  Abu tace Boko Boko dai hikenan naji duk abinda ake fada akan boko ance yan wutane hine mu za a kaimu saboda ba a sonmu   Ba a San naku gobe zaku fara zuwa daga nan idan kuntaso saiku wuce isilamiyar malam rabi'u   Binta ta tashi ta daka tsalle tace rabi'u Yasin ba inda zani Wannan bakin mugun baki da Wannan kan nahi dayake kyalli kamar an cirohi A tandun mai  Malamin naku kinga binta nasan irin takun sakar da kukeyi da malam rabi'u idan kika bari yakawo min karar ki kikuka da kanki irin dokan dazan miki baze faduba harda ke Abu cewar Nura  Abu tace hikenan dai zamu leka wutar bakomai amma idan mukaji da zafi bazamu sake koma waba   Tsaki Nura yayi yatafi ya basu guri   Sukaci uwar KWALLIYA suka fice basu cewa Inna komai ba    
.
WASHE GARI   Abu tana tashi tasa kayan maka ranta ta janyo kayan KWALLIYA zata yi  Nura yace karki sake kiyi KWALLIYA makaranta zaki ba dandaliba   Abu tace Tab yaya Nura gaskiya bazan iya fita banyi KWALLIYA ba ga kanhin tirare i nayi Amma ba KWALLIYA a fuska ta   Nura yace Eh ba a KWALLIYA idan za aje makaranta Abu dole kidena wasu abubuwan yanzu tinda kinfara zuwa makaranta   Binta ta shigo ba sallama  agaban kayan KWALLIYA ta zauna zatayi KWALLIYA  Nura yace ke Binta ba sallama Bakomai kiwani zo gaban kayan KWALLIYA  Binta tace yaya Nura tinda nafito banyi magana da kowaba Gahi yanzu kasa nayi magana Almiskin bakina yafita   Hanci yatoshe yace naji Almiskin kice kema kinbi layin qazantar Abu ko makaranta zaku zakuje kuga yanda Ake safta  Binta tace *'YAR KWALLIYA* mezan gani haka meyasa bakiyi KWALLIYA ba  Abu tace Binta kibarni kibarni kwai ni Abu *'YAR KWALLIYA* ni za a hana yin KWALLIYA badole kiga haka ba    Binta tace shine kike daga hanka linki ina Inna   Abu tace tana ciki   Binta tace yaya I na bayanka gwanda daka hanata bani kayan KWALLIYAR NA shiga dasu au baza kibaniba bari na dauka da kaina  Binta na shiga ta juye kayan KWALLIYAR a Jakarta tafito  Binta tace bata cikifa   Abu tace hakane yanzu ta fita zomuci Abinci bayan sun gama  cin Abinci Nura ya kaisu maka ranta  Duk wanda yaga fuskar Abu ba KWALLIYA sai yayi mamaki dan bata taba fita ba KWALLIYA ba  Suka shiga Aji   Binta tace Abu Albishirin ki   Abu rai a hade tace goro  Binta ta bude Jakarta tace kalli  Abu cikin mamaki tafasa kara ta rungume binta ta tsalle a aji         Hankalin daliban ya koma Kansu  Abu tace muna fukai me kuke kallo da sannu duk zanyi maga ninku           
.
  Daliban Suka dena kallon su  Suka baje kayan KWALLIYA sunayi malami ya shigo aji akatashi ana gaisuwa banda Abu da Binta KWALLIYA kawai suke yi  Malamin ya karaso gurin su yace Ku meye haka kwalliya a cikin aji me kukeyi a nan aji bantaba ganin kuba   Abu tana shafa Jan baki tace baza kasan muba hime maka rantar be sanar dakai komu suwaye bako hege wato ya cinye kudin ko to hikenan  Yace bagane me kuke nufiba fa   Binta tace kaga waimu sa babbin dali baine kuma nanne ajin mu kana jiko jeka to  Yace kee Nifa malamin kune kibani girma bakowana magana zaki dinga fada minba   Abu tace inji kaba girma idan karike girmanka mutayaka rikewa idankuma kaki rikewa mubi takai mu wuce  Malamin yayi murmushin keta yace kugoge fuskarku sannan kubani kayan KWALLIYAN  Abu tace tab ba abinda zamu baka kuma ni Abu bazan goge KWALLIYA ta ba  Binta tace nimadai bazan gege ba malam kabar daliban naka a tsaye fa  Yace kuzauna yayi murmushin yaje gaban Allo yafara koyar dasu kamar yanda ya saba  Abu tace gaskiya nagaji baza a yi wani abin bane bayan Wannan kazo ka I hemu da surutu  Binta tace a he kekina jin hi tinda yafara har I  yanzu banji komai ba ni yunwa ma nakeji  Yace Anya karatu kuka zoyi kuwa   Abu tace waya sani Abu a duhu Nifa karatun higa wutan nan beda meniba dahi da bahi duk1ne  bokoko Awuta   Binta tace gaya mihi kadai koyarda su dan naga kamar suna gane wa  Yace anya Ku muta Nene kuwa ke dawani fuskarki kamar aljana waya gaya miki karatun shiga wuta nake koyawa  Binta tace baka jiba bokoko a wuta hine zakace bakaratun higa wuta bane  Yace kutashi Ku fita daga ajin nan kufita kuyi shir menku a waje   Abu tace seme danka koremu kahiga wutar kaika dai kacike gurin karkabari asa wani  Yace keni zaki fadawa haka  Tamurguda baki   Yadauko bulala ya zuba mata  Tasaki kara        
.
  Binta tace meyasa ka daketa kai ko a qauyen mu mune muke yiwa maza duka hmmm  Yace me kike nufi nima dukana zakuyi kenan  Abu tace meze hana tinda ka dakeni saina rama  Yace waya gaya miki idan malami yadaki daliba tana ramawa  Binta taja hannun abu      Tace Abu rabu dahi zomu fita ze fito ya same mu damu yake maga mekoya karatun higawuta dole mukoya mihi hankali        Suka fita  Abu kinga ya aika a siyomai abinci            Abu tace waye ya aika asiyo mihi abinci mekoya karatun higa wuta  Binta tace Eh hine zomuje  Yaron ya siyo abincin zekai wa malam binta da Abu suka tsare shi  Abu tace Kai bamu abinci kaje kadebo min ruwa zansha kagani ba quwace  Yace malam ya aikeni bari nakai mishi nadawo saina debo miki   Binta tace harna hadiyi yawu banga abin dake cikiba amma nasan zeyi dadi tafada tana dariya             

0 comments:

Post a Comment