Monday, 5 March 2018

TANA RAINA Page 6-10

13-14 Suhail da kamal ne a hanyan tfyansu kauyen su Sabreen, suna tafe suna hira har suka iso daidai gurin daya had'u dasu sabreen, se uace kamal a daidai nan ne amma dai mu kara gaba kadan, ahankali,suke tfy se suka hango hanya shiga garin sukai tfy kad'an se suka hangi kakan sabreen yana komawa rike da cefene a hannunsa, gunsa suka tsaya da motan tare da dayi masa sallama, bayan sun fitone suka gaishesa cikin girmamawa sannan sukace baba dan Allah muna tambayane, yace toh ina jinku, suhail yace wata yarinya nake nema ko Allah yasa ka santa, kaka yace menene sunanta? Suhail ya kalli kamal se kamal yace wato dai baba muma basusan komai game da itaba kawai dai mun gantane tanan tana sanye da riga da zani da kuma bak'in himar sannan tasa nik'af a fiskanta, kaka yace to gaskya bayin Allah bazan ganetaba, dama ace kun gayamin sunantane ko sunan mahaifinta ko kuma kamanninta,toda zan iya ganewa, suhail yace baba yarinyar an mata fyad'e jiya jiyan nan kuma dai muna kyautata zaton atanan take, kaka yace fad'e kuma subhanalillah to gaskya bata nan bane, domin duk abinda ya faru a kauyennan baya b'uya a masallaci ake sanar da koma menene, kamal yace to ai k'ila baza a iya sanar da magana irin na fyad'e ba, kaka yace za'a sanar ina tabbatar muku da cewa babu abinda yake b'uya a kauyennan namu, wai samari me kuke nema agun yarinyarnan ne, kamal yayi saurin cewa dama daga cikin gari muke, muna neman masu aiki ne, kaka yace wani irin aiki kuma, kamal yace mata dai wanda suke aikin wanke wanke da shara da kuma girki za'a dinga biyansu a wata. Kaka yace haba da gaske, ina da jikata nasan zatayi farin cikin hakan dan ta dad'e da gama secondary tana so taci gaba da karatu amma bamu da hali, tayita neman aikin a kauyennan amma bata samuba, sedai kuma aiyukan daka lissafo sunyi yawa, Suhail yace a'a dama girkine kawai zata dingayiwa mahaifiyata dan bata da lfy, kaka yaji dad'i sosai yace indai wannan ne shikenan jikata ta iya girki amma na gargajiya ne ko kuma ince namu na karkara sam bata iya naku na birnineba. Kamal yace ba damuwa muma ai muna cin abincin gargajiyan sosai dan haka ba matsala zamusa a koya mata. Kaka yace to shikenan kud'an bani lokaci inyaso seku dawo daga baya koh? Suhail yace to shikenan mun gode sosai baba, kaka yace bakomai nine da godiya nasan jikata zatayi farin ciki sosai dan haka sekun sake dawowa...wasu samarine suka karaso a guje suna haki suna cewa kaka gara da muka had'u dakai, Allah yayiwa mammin SABREEN rasuwa yanzu yanzun nan shine aka aikomu donmin muzo mu kiraka, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un dukkansu suka amsa, kaka yace me kace SALE, Mammi ta rasu? Sale yace eh kaka macijine ya sareta a bayan wuyanta kuma harta cika. Kaka yace ina sabreen jikata take a wani hali take ciki? Suhail ya kamo hannun kaka yace baba shiga muje tare, ba musu suka shige gabad'ayansu suka isa har kofar gidan inda suka iske mutane a cike. Fitowa sukayi dukkansu suka wuce cikin gidan, lokacin har matan makota sunyi mata wanka an suturceta kaka ya isa yayita mata addu'a sannan aka fito da gawanta zuwa waje nan akai mata sallah aka d'auketa dan kaita gidanta na gaskya sega sabreen ta fito a guje tanata kuka tana cewa kaka dan Allah karku tafi min da mammina ina sonta wlh karku kaimin mammina rami dan Allah ku tausayamin ita kad'ai ta ragemin fa kaka. Kowa ya tausayawa sabreen musamman kaka da iyayen munira, munirane ta biyota da hijabi danko d'ankwali babu akanta bare takalmi, gashin kanta duk ya tattashi kamar wata mahaukaciya, bayan munna tasa mata himar d'inne se take k'okarin janyota amma ta kasa, kaka yace da suhail dan Allah yaro taimaka ka mayar min da ita gida kaji, ba musu suhail ya kamo hannunta yana kokarin maidata gida seta gantsara masa cizo tana cewa dan Allah ka sakeni zasu tafimin da  mammina nefa nika sakeni. Kuka sosai takeyi hakama munira, Suhail ya rasa meke masa dad'i sam bayaso yaji mace na kuka, ahaka har suka k'arasa kofar gidansu munira wata mata ta riko hannunta suka k'arasa da ita cikin gidansu muniran. Shi kuwa suhail hannunsa yayi jahjazir dan cizon da sabreen tayita mishi, binsu yayi mak'abartan akai mata komai sannan suka dawo sukai musu gaisuwa se suka tafi suna masu tausaya musu sosai
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas)
15-16 Bayan su suhail sun dawo gidane suka sami mum a palo, bayan sun zauna ne kamal ya dauki ruwa a frigj yasha sannan yamikawa suhail mayasha, mum tana ta binsu da kallo tace lfy kuwa kodai baku sami mai girkin bane? Kamal yace mum samu mum nan dai suka bata lbrn abinda ya faru, sosai mum itama abin ya bata tausayi, tace Allah sarki Allah ya jikanta yanzu dai za'a d'auki lokaci kafin tazo, can se idonta yakai kan hannun suhail, tace suhail me nake gani a hannunka, suhail ya shafi gurin yace cizon da yarinyan tayitamin ne lokacin dana rik'e hannunta, shi kansa kamal baisan da batun cizonba se yanzu dayaga hannun suhail yayi jah kuma ya kunbura, mikewa suhail yayi ya shiga d'aki ya watsa ruwa sannan ya fito ya goga mantileta a hannun nasa seya kwanta yana tunanin abunda ya faru, kamal ne ya shigo shima wankan yayi,yazo ya  zauna kusa da suhail fiskar sabreen kawai yake gani dana munira, mamakin irin kyawu na sabreen yakeyi, yace suhail amma kaga fiskan sabreen kuwa, gashi dai kauyene amma har ana samun kyawawa haka, gaskya irin kyawun sabrin sedai a kasar larabawa da indians bade nigeria ba.
  Suhail yayi murmushi yace abokina ni gaskya banganta sosai ba, saboda gabad'a kukanta ya d'aga min hankali, kamal yace dama na tuna hakan a raina wlh, yauzu me abin yi? Suhail yace se ranan da za'ayi uku semu koma muyi musu gaisuwa, tunda wani sati zanyi tfy zuwa ranar da za'ayi bakwai seka sake komawa kaji me kakan nata zaice. Haka za'ayi suhail Allah ya kaimu.
   Haka sabreen ta kasance cikin kuka koda yaushe, nasiha sosai malaman kauyen nasu suke mata harta dena kukan, amma dai ba'a rasa ganin hawaye a fiskanta. Kullum zaka ganta tare da munira dan a gidansu take zaune, maganganu masu kwantar da hankali munna take mata harta d'an ci abinci kad'an, amma idanunta sun kubura dan kukan mamminta.
  Yau ne za'ayi uku, suhail da kamal suka shirya cikin fararen shadda dasu akayi addu'oi sakamakon sunzo da wuri, bayan an gamane suka sake keb'ewa da kakan sabreen sukace sunaso su mata gaisuwa, kaka da kansa yaje ya kirata, himar suka saka ita da munira suka fito lokacin kaka yaje gaisawa da wasu. Kamal ne ya fara magana yace sabreen ya hakuri, kanta ta d'ago tace Alhamdulillah tana kallon kamal din, yace Allah ya jikanta, tace ameen sannan ya juya gun munira suna gaisawa se suhail yace sabreen ya hakuri, kai ta d'ago don kamar taso ta gane muryarsa, idonsu na had'uwa ta ganeshi tana masa kallon mamaki, Alhamdulillah tace dashi, yace toh Allah ya jikanta da rahama, ameen tace nagode sosai harda yar mirmushinta. Suhail ma kallonta yakeyi har cikin ido, se kuma ya kau da kansa yace kamal muje koh, kamal yace to sabreen ya sunan kawarki ne, sabreen tace sunanta munira, ok dukkanku kuna da suna masu dad'i mu, sabreen tace mungode Allah ya bada lada tana kallon suhail shida yake kokarin wucewa gun motansa yace ameen mum d'inmu tace amik'a mata gaisuwa agareku, sabreen tace mungode sosai, murmushi suhail yayi mata sannan ya kira wasu yara tare da bud'e but na motarshi yara suka fara shigowa da kayan abinci juice, taliya, indomie dasu buhun shinkafa. Sabreen ta kalli kamal tace wannan fa, kamal yace sadakace muka kawo muku, hawayene yake fitowa daga fiskarta daidai lokacin suhail ya karaso, hanki ya ciro a aljihunsa ya mika mata, hannu tasa ta karb'a tana kallonsa har cikin ido tana zancen zuci, duk lokacin da nake cikin wani hali se in ganka agun ya akayi kazo nan kuma? Suhail ne ya katseta da cewa shide mamaci babu abinda yafi bukata irin addu'a kukanki azabane agunta sabreen, dad'in zancen nashi taji atake tare hawayenta da hankinsa sannan ta mika mishi tace mungode sosai Allah ya bada lada, ameen sukace se suhail yace ki rik'e nabar miki, itama murmushin tayi tace se anjumanku sannan tajawo hannun munira suka wuce gida. Kamal se binsu da leke yakeyi, suhail ne ya janyo rigansa yace inaga dai ba k'alau kakeba, gaisuwafa mukazoyi ba kallonsuba malam, dai dai lokacin kaka ya k'araso yana musu godiya sannan sukaci gaba dayin magana. Sabreen kuwa mamaki takeyi ya akai suhail yazo nan樂, maman munirace tace sabreen wannan fa suwaye suka kawo, sabreen tace sune wanda muka gaisa dasu yanzu nima ban sansuba sedai mu tambayi kaka idan ya shigo k'ila shiya sansu.
   Bayan kaka yayi sallama da kowane saiya shigo gidan su muniran, nan gaya kayan abinci kam dewa. Baban munirane yake tambayan kaka suwaye suka kawo wannan  sadakan haka? Nan kaka ya kwashe lbrn had'uwansu dasu suhail tas ya gaya musu. Munira tayi saurin juyowa ta kalli sabreen, sabreen ta kyafta mata ido sannan ta fara murmushi a zuciyarta tace to meyasa yake nemana, kodai d'ankwalina zai bani? Alhamdulillah tunda baiga fiskanaba, kuma koda naje yin aiki a gidansu bazan tab'a sanar dashiba tunda nidai nasan ba'amin fyad'eba kuma ina farin ciki zan koma makaranta dan haka na amince zanyi musu aikin☺
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
17-18 Sabreen da munirane suna zaune a d'akinsu bayan sunyi sallan isha suna cin abinci, munira ta kalli sabreen tace dama shine suhail d'in? Sabreen tace eh shine bai ganenibane saboda nik'af ne a fiskata ranan. Munira tace to ai yakamata ki sanar dashi tunda kinga nemanki ne yasa suka sake dawowa nan d'in, sabreen tace a'a munna wannan maganar sirri ce tsakanin nida ke pls, munna tace to ai shikenan kika san koya kyasa ne yasa ya biyoki, gashi da alama masu haline kinga shikenan mun fito fari, dariya sukayi dukkansu sannan sukaci gaba da hiransu.
   B'angaren suhail kuwa, tunda suka dawo kowa da tunanin da yakeyi, hafsat ne tazo ta samesu a palo tace yah suhail ina kukajene inata nemanku, suhail yayi murmushi yace munje gaisuwa ne hafsat akwai wani abu ne, a'a kawai dai dan ban ganku bane. Kamal yace nidai zan tafi gida seda safenku, suhail ya tashi ya rakasa hargun mota sukai sallama sannan ya dawo gun mum sukaita hira har zuwa 9pm kafin suka wuce donyi bacci. Shidai suhail yana ta kallon idanun sabreen a ransa dan yayi mishi kama dana wannan yarinyar, sedai na sabreen sun kumbura kuma sunyi jah, to shine dai yake kokonto akan kila kamace kawai, kuma kaka ya tabbatar musu da cewa babu yarinyar da akayiwa fyad'e a kauyen, ya shiga rud'ani sosai da haka yayi bacci...
Yau wata guda kenan da rasuwan mammin sabreen. Shikuwa Suhail yana can pakistan kusan 3week kenan. Kamal ne a kofar gidansu munira yana jiran fitowar kaka da sabreen, can segasu sun fito suna rungume da juna suna kukan rabuwa, maman munirane taketa basu hakuri tana cewa munna kiyi hakuri aiba rabuwa kukayiba 'yan watannine kawai zatayi seta dawo kinji, da kyar dai suka rabu kamal ya bud'ewa kaka gaba sannan sabreen ta shiga baya suka tafi tanata yiwa munira bye tana kwalla. Tunda suka fara tfy sabreen taketa kuka har suka iso wani gida mai kyau, hon kamal yayi aka bud'e suka shiga, bayan motan ya tsayane kamal yaje ya bud'ewa kaka dan sabreen kam harta fito tana rik'e da yar jakanta, kamal yace bissimillah kaka muje, kofa ya bude sika shiga k'aton palo mai kyan gani, anan suka zauna kamal yace sannunku da zuwa kaka, kaka yace yawwa sannu kamal, ruwa mai sanyi ya kawo musu tare da juice ya zuba musu, ahankali suka karb'a suka sha tare dayi mishi godiya. Kamal yace kaka nan gidan mahaifinane amma Allah yayi musu rasuwa shida mahaifin suhail a k'asar saudiya, iyayenmu aminan junane sosai suna business a wani kamfani dake pakistan, lokaci lokaci suna zuwa duba kasuwancin nasu. bayan rasuwansune mahaifiyata tayi aure a pakistan d'in, inda ni kuma nake zaune a gidan mahaifina, nida suhail mukaci gaba dayin business kamar dai yadda iyayenmu sukeyi, idan naje wannan karon, wani karon kuma suhail ne yake zuwa, mahaifiyar suhail tak'i yin aure sam tana zaune damu anan da kuma 'yar yayan baban suhail wato hafsat, itama marainiyace dan bata da uwa bare uba. Mahaifiyar suhail ta rik'e hafsat kamar 'yarta na cikinta, inda mu kuma muka zame mata yayyu. Matar da take musu girki d'anta ya samu aikin yine shine yace mamansa zata dena girki, shiyasa muke neman wanda zata dinga musu girki ana biyanta duk wata. Kaka yayi ajiyar zuciya yace Allah ya jikansu da rahama suka amsa da ameen dukkansu. Kamal yace na kawoku nanne saboda kace sabreen bata iya girkin zamaniba sena gargajiya, shine nakeso ku zauna anan koda na tsawon wata biyu ne na samo wanda zata dinga koyawa sabreen girke girken zamani idan ta iya sena kaiku gidansu suhail koya kagani kaka? Kaka yace bakomai kamal na fahimceka kuma na amince danna yaba da halaiyarku nasan bazaka cutar damuba zamu zaunan anan d'in harse ta gama koyon. Kamal yayi murmushi yace to alhamdulillah kaka ina tabbatar maka da cewa bazan tab'a cutar dakuba shiyasama nace mu taho tare dakai koda ruwa seka dinga ba flawer kaima ana biyanka. Godiya sosai kaka yayi sannan kamal yace muje in nuna muku masauk'inku, tare suka mik'e sabreen tana binsu a abaya, d'akin mummynsa yaba sabreen, sannan yaba kaka d'akin babansa, manyan d'akunane da komai a ciki, murna sosai sukayi tare da k'arayin godiya.
  Kamal ne kwance a d'akinsa ya kira suhail a waya yace abokina se nanda 2month su kaka sasu zo, suhail yace toba damuwa Allah ya nuna mana, kamal yace amin sannan sukaci gaba dansu. Bayan sun gama wayanne kamal yace bazan iya sanar dakai suna gunaba abokina, harse sabreen ta k'ware sosai da girkin zamani anan, insha Allah gobe zanje inyi musu cefene sosai zuwa jibi RUKAYYA zatazo ta fara koya miki sabreen, da wannan shawaran kamal yayi bacci tare da jin dad'i a ransa wanda bansan dalilin saba

[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
21-22 Bayan sabreen ta gama karyawane taje tayi wanka tasa d'inkin doguwar riga na atamfa ta d'aura d'ankwalinta sannan tasa farin himar komai bata shafaba ta fito. Kamal ya shirya cikin blue shet da black jeans yana zaune a palo yana jiran fitowanta, can segata ta fito da murmushi a fiskanta tace hamma kamal na shirya, kalonta yayi tare dayin murmushi yace toh muje, atare suka fito lokacin kaka yanaba flower ruwa sunata hira da mai gadi,segasu sabreen sun fito tace kaka zamuje mu dawo, kaka yace toh sabreen sekun dawo. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai acikinsu har suka karasa super market, nanne kamal yace muje sabreen, a hankali ta fito suka shiga se kallo takeyi dan bata tab'a zuwa super market ba. Kayan abinci suka saya sosai, sannan kamal ya kaita gun kayan sawa yace ta d'auki duk abunda taga ya mata kartaji kunya, nan sabreen tayita d'iban atamfofi da material da kuma dogayen riguns, ta kalli kamal taga yana can nesa da ita, gunsa ta nufa tace hamma kamal zan iya d'auka ko wanne 2? Murmushi yayi yace ko 5 5 nema ki dauka kinji, murmushin itama tayi sannan tace nagode ta juya yana binta da kallo yana murmushi, komai 2 take d'auka wai ita da muniranta. Bayan sun gama da kayane yace ta biyosa suje gaba, sun isa wani gun maiyukan shafawa suka nufa da turaruka, NATURAL HONEY shine mai d'inda take shafawa ita da munna, dan haka shima ta d'auki 2 sannan ta d'auki turaren FASIO shima 2 dasu body spray, kamal yace kayan kwalliya fa, sabreen tace sedai in d'aukawa munna danni bana kwalliya, murmushi yayi yace koda gazal da janbaki da hoda nedai ki dauka, dariya tayi tace hamma kamal ai to na d'iba kayan kwalliyan gaba d'aya kenan, yace eh idan kina kwalliya zakifi haka kyau, ba musu ta d'iba suka d'ibi takalmi da jaka, sayayya dai sukai sosai sannan suka wuce gun tela aka bashi d'in kaya kala 24 nata dana munna. Daga nan suka wuce gida, kaka ya tayasu shiga da kayan komai aka shiryashi a store, kayan,tea kuma suna daining drinks a frij, komaidai gun zaman suna nama akai kaisa babban friza. Sabreen ta nunawa kaka irin sayayyan daya mata ita da munna tace kuma munbada d'inkin kaya, kaka yayita masa godiya dasa masa albarka hakan yayiwa kamal dad'i sannan yabaiwa kaka takalma da turare yace kayanka anjuma zankai makasu d'inki, godiya sosai sukayi sannan kamal yace shizai fita zaije ya duba mum d'in suhail da hafsat ze zuwa dare zai dawo sabreen ki dafawa muku koma menene kinji, toh seka dawo.
A gidansu suhail kamal ya yini yayita bacci harseda yayi sallan isha sukaita hira kamar yadda suka saba sannan ya koma gida. Lokacin 8:30pm kaka suna zaune a palo suna kallon sunna TV kamal yayi sallama tare da shigowa, bayan ya zauna ne yace kaka sannunku da gida, yawwa kamal sannu da dawowa yaka barosu, lfyansu lau wlh, sabreen tace sannu da zuwa hamma kamal ga abincinka akan daining, yawwa sabreen ta bari naje nad'an watsa ruwa senazo naci girkin k'anwata. Bayan yayi wanka ya fitone yasa jallabiya tare da fesa turare ya wuce daining, sabreen ta mik'e taje ta zuba mishi tuwon shinkafa da miyar egushi yaji manja da dry fish ga nama, tunda sabreen ta bud'e kulan kamshi ya daki hancinsa take nyawunsa ya tsinke, da bissimillah ya fara cin abincin yana lumshe ido☺, sabeen ya kirata, tace na'am tare da mik'ewa, irin wannan miya mai dad'i aibase a samo mai koya miki girkiba domin ni ban tab'a cin miya mai dad'n wannanba, dad'i sosai taji tana dariya tare da cewa nagode amma ina bukata dai akoyamin wad'anda ban iyasuba na zamani. Kamal yace badamuwa gobe zatazo ta fara nuna miki kinji, tace toh Allah ya kaimu goben yace ameen.
  Washe gari da safe RUKAYYA tazo bayan sun gaggaisa ne se suka wuce kichine da sabreen suka fara had'a breakfast, duk abinda RUKAYYA takeyi idon sabreen nakai har suka gama sukayi breakfast gabad'ayansu kuma sunji dad'in girkin nata. Haka sukayi na rana suka sake yin na dare, kullum kuma RUKAYYA so 3 takeyin abinci wato safe rana da kuma dare, seda tayi girki harna tsawon 1 week sannan tace sabreen ta sake maimaita duk abinda ta dafa na tsawon satin. Tsab kuwa sabreen tayi kamar yadda RUKAYYA takeyi kuma yayi dad'i sosai, Aunty rukayya shine sunan da sabreen take kiranta dashi, cikin k'ank'anin lokaci suka shaku da juna sosai kuma sabreen taci gaba dasa hankali akan koyan girkin. Shikuwa kamal dad'i yakeji sosai yana zuwa dubasu mum kullum dan acanma yafi zama se dare yake dawowa.
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
23-24 Lokaci nata fty har aunty Rukayya ta gama koyawa sabreen girki na tsawo 2month, sannan babu abinda zakace sabreen ta dafa makashi wanda bata iyaba, ta k'ware sosai itama yanzu sedai ta koyar da wasu, harta snacks da drinks na gida wabu wanda sabreen taba iyaba. Yaune kamal ya sallami aunty rukayya da kud'ad'e masu yawa wanda nima bansan adadinsu, sabreen suke tsaue da aunty rukayya suna bankwana, sabreen tace aunty rukayya ki bani number wayanki dukka dai bani da waya amma zanso kiban number'nki kakana yace jibi zai sayo min waya, aunty rukayya tace to badamuwa nan ta ciro card d'inta tabawa sabreen sannan tace gaskya kinada hankali da dad'in sha'ani sabreen Allah ya baki miji na gari, sabreen tayi murmushi tace ameen aunty rukayya bazan tab'a mancekiba nagode sosai Allah ya biyaki, aunty rukayya tace ameeen sannan tayiwa su kaka da kamal sallama ta tafi.
Duk hiran da aunty rukayya sukeyi da sabreen kamal yana jinsu, dan haka ya shirya zai fita se sabreen tabi bayansa tace yah kamal zaka fita ne, eh sabreen akwai wani abune, a'a dama inaso inyi maka godiyane akan girki dakasa aka koyamin nagode sosai, murmushi yayi yace bakomai sabreen nizan fita se dare zan dawo, ok dama inaso inje gurin munira ne tunda muka rabu bamu sake had'uwa ina kewarsu sosai☺, kamal yace to shikenan ki bari zuwa gobe semuje harda kaka koh, dad'i taji sosai tana maiyin murmushi wanda yake k'ara mata kyau tace nagode yah kamal Allah ya kaimu goben, ameen sabreen na tafi. Bayan kamal ya fitane ya kira aunty rukayya yake tambayarta ko sabreen ta tab'a gaya mata irin wayar da takeso, aunty rukayya tace eh toh akwai randa muke hira take cemin akwaia wayan malaminsu na secondary skul wai wayan yana da camera sosai idan ya d'aukesu hoto a ciki, tun daga ranan take son wayan a ranta samsung galacky x5, kamal yace toh shikenan nagode. Shagon waya ya tsaya ya saya mata sabuwar samsung x5 sannan ya wuce gunsu mum.
Kamar kullum se yaban isha kamal ya dawo bayan yaci abinci ne yazo palo yasamesu sunata hira, wayan daya sayawa sabreen ya mik'a mata gashi sabreen wayane na sayo miki na miki charging sannan nasa miki sim d'in MTN aciki, karb'a tayi hannun biyu tana farin ciki tare da cewa nagode yah kamal Allah ya biyaka da gidan aljannah, ameeen sabreen Allah ya bamu dukkanmu sannan kakama yayi masa godiya yace kamal kaibaka gajiyane, kud'adenka zasu kare dan Allah ya isa haka ka dena b'arnatar da kud'inka akanmu zaman da mukeyima kad'ai ya ishemu wlh ka mana gata sosai Allah ne kad'ai zai biyaka, kamal yace haba kaka bakomai wlh ni zanje in kwanta saboda da safe nakeso mu tafi dan kud'an yini acan zuwa yamma semu dawo, kaka yace to badamuwa Allah ya kaimu, wayarsace tayi kara ya d'auka tare da sawa a hands free yace hello abokina, suhail yace eyyy yane gwabro kak'i dai kayi aure koh, kamal yayi murmushi yace wannan ai bani kad'ai kake tsokanaba harda kanka, dariya suhail yayi yace toh garin yasu mum, kamal yace yanzu na dawo daga gunsu lfyansu lau ya pakistan, suhail yace lfya lau wlh mummy ce take cemin wai munk'i muyi aure semu tsufa ai mun rasa matan aure, kamal yayi dariya yace aiseka yi kafin nima nayi dan haka kai nake jira, suhail yace zan dawo ran friday insha Allah ya maganan su kakane dan mum tacemin ran wenesday mai girkinsu zata tafi, kamal ya kalli kaka da sabreen yace eh nima d'azu danaje ta gayamin kuma na tabbatar mata da cewa ran talata zan kawo mata mai girki, suhail yace ok to yaushe zakaje garinsu kakan? Kamal yayi murmushi yace gobe insha Allah, suhail yace to nagode abokina ka gaida su kakan inkaje, kamal yace suna jinka, suhail yace me kace? Kamal yace sorry nace zasuji, bayan sunyi sallama ne kaka da sabreen suke ta dariya, kunya kamal yaji seya mik'e tare da cewa seda safenmu, har yanzu dariya sukeyi sannan kaka yace to Allah ya tashemu lfy yace amenn sannan ya shige d'akinsa.
Washegari suka shirya tsab se k'auyensu, murna sosai mutanen k'aunuen sukayi da ganinsu kaka musamman ma nunna, tace sabreen me sirrin ne kin ganki kuwa yadda kika kara kyau se wani shek'i kikeyi, sabreen tayi dariya tace kema kin canjafa me sirrinne k'awas? Nan munira ta bata lbrn saurayin da tayi me suna ABUBAKAR SADDIQ shi doctor ne kuma yana da hankali sosai gashi yana kulawa da ita sosai kingama harya sayamin wayanmu galacky x5 sannan komai ya sayamin sena ajiyei miki naki kinga nan munira tayita nunawa sabreen kayan alkhairin da Abbakar yake mata harda iyayenta. Bayan ta gama ganine tace lallai k'awata kin paso gari Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma nuna mana bikinmunira tace amenn toya birnin bani lbr mana, sabreen ta kwashe lbrn birnin tun daga farkon zuwansu har karshe ta fad'awa  munna sannan ta bata sayayyan kayan da kamal yayi musu harda k'arin jaka da takalmi nasu mama ma dabanne. Munna ta bud'e baki tana ganin abun duniya tare dayin godiya ita dasu mama sukaiwa kamal godiya sosai, munna tace kodai yana sonkine sabreen? Sabreen tace SO kuma, oho nidai bai tab'a gayaminba nima kuma bansa komai a rainaba, SUHAIL shine a raina amma kuma duk randa yah kamal ya furtamin cewa yana sona nad'au alk'awarin amince masa tare da bashi soyayyata danya cancanci hakan daga gareni kuma kowace mace zataso mutum irin yah kamal dan baida wata matsala wlh. Munna tace to Allah ya zab'a miki mafi alkhairi sabreen, ameen Amaryan abbakar mu zamu koma se wani lokaci kuma.
  Bayan sun komane kamal yace to kaka seku shirya jibi talata zaku koma gidansu suhail ran laraba mai girkinsu zata tafi sabreen zata fara girki ran alhamis yayinda suhail zai dawo k'asar ran FRIDAY. Daga kaka har sabreen basuso hakanba, shima kamal d'in babu yadda zaiyine amma sam bayason tfyarsu, kaka yace toba komai Allah ya nuna mana, kamal yace ameen sannan ya wuce d'akinsa suma sukai nasu d'akin da tunani kowannensu yayi bacci
TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
25-26 Kamal ne dasu sabreen akan daining suna breakfast, babu wanda yake cewa komai gabad'aya jikinsu a mace yake tunba kamal ba. Bayan sun gamane sabreen ta koma d'akinta tana kwance akan gadonta suna waya da munira tana dariya, bayan sun gamane ta kira aunty rukayyama sukasha hira sosai dayake kamal yasa mata credit aciki.
   Wani number ta gani yana kiranta, ta d'auka tare da cewa hello, muryan yah kamal taji yace sabreen kamal ne na kirakine in sanar dake wannan number nane kiyi saving kinji, ok toh nagode ya kamal ka fita ne? A'a yanzu dai zan fita akwai wani abune, emmm dama inaso inje shago ne akwai abinda nakeso in saya, toh menene gayamin se in sayo miki koh, shuru tayi batace komaiba, yace "sabreen" tace emmm nafiso inje da kainane yah kamal, murmushi yayi yace toh shikenan fito muje kisaya, toh nagode sannan ta katse wayan ta dauki himar d'inta tasa tayiwa kaka sallama sannan ta sami ya kamal agun motansa, gaba ta bud'e ta shiga sannan yaja suka isa wani d'an babban shago, sabreen tayi saurin cewa yah kamal ka zauna kawai ni zanje yanzu zan fito, toh yace mata sannan ta fita ta wuce shagon, bayan shigantane kamal ya fito yana biye da ita a baya batare data saniba ya shiga. Part kawai sabreen ta dauka guda 2 sannan tazo gun biyan kud'in, mai karaban kud'in yace ki barshi kawai, tace yah za'ayi kace in barshi ungo karb'i kud'inka, mai shagon yace wani ya riga daya biya miki, tace wani kuma waye shi? Mai shagon ya nuna mata motan kamal, kunya sosai taji tace yanzu yasan abinda na saya kenan, k'in fita tayi tana tsaye a cikin shagon segashi ya shigo fiskansa a d'an d'aure yace baki gama bane sabreen, shuru tayi ta wuceshi ta nufin gun motan kunya kamar ta shiga k'atsa.
    Tunda suka fara tfy batace komaiba kanta na gefe, kamal yace sabreen ya kikayi shuru, tace bakomai, murmushi yayi yace aida kin gayamin in sayo miki me aciki muna sayowa hafsat ai nida suhail, kunya taji sosai tasa himar d'inta ta rufe fiskanta tana dariya batare dayajiba, shima dariyan yayi yace kidena kunyata sabreen domin ni bana kunyanki kinji koh? Batace dashi komai shima bai sake cewa komaiba har suka iso gida, bayan ya tsayane ta bud'e kofan tare da cewa nagode batare data kalleshiba, dariya yayimata wanda ya kara masa kyau yace bakomai na tafi gun mum se dare zan dawo, toh zallah ya tsare, ya ameeen sannan ta rufe motan ya tafi. 9:00pm kamal ya dawo gida, bayan yayi wanka yaci abincine seya kira sabreen a waya yace inason magana dake ina palo, doguwar rigan atamfane a jikinta da d'ankwalinsa da tayi lullub'i dashi yana hango gashin kanta harta k'araso gunsa sannan ta zauna akan kujera tace gani yah kamal, kamal ya gyara zama yace sabreen kin tab'a yin soyayya? Wani iri taji dan bata tsanmaci wannan tambayar daga garesaba, daurewa tayi tace a'a yah kamal, ya sake cewa amma dai nasan kina da masoya ko, tace eh akwai amma gaskya ban tab'a kula ko wani d'a na mijiba, kamal yace shin ko akwai wanda kikeso aranki? Ananne sabreen tayi shuru dan bata san me zata ce mishiba, sake maimaita tambayan yayi tareda cewa ina sauraronki sabreen, kanta a sunkuye tace a'a babu. Kamal ya sauke ajiyan zuciya yace ko zan iya sanin dalilin k'inyi soyayyar? Sabree tace babu wani dalili yah kamal, yace toh shikenan tashi kije, kallonsa takeyi har cikin ido shima haka sannan ta wuce d'aki. Murmushn jin dad'i kamal yayi tare da tashi ya shige d'akinsa da farinciki sosai aransa. Ita kuwa sabreen mamakin tambayoyin da yah kamal yayita mata takeyi har bacci ya d'auketa
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
          (Sad-Nas)
27-28 Ayaune sabreen zasu koma gidansu suhail, bayan ta gyara ko ina ta kimtsane tayiwa ya kaml girki ta ajiye a daining, da yamma yazo ya tarar dasu a palo suna zaune. Bayan yaci abincine yace to bari ind'an watsa riwa semu tafi koh, sabreen tace to sannan taje ta d'auki plate d'in ta wanke ta dawo ta zauna, daidai lokacin kamal ya fito daga d'akinsa se kamshin turare yakeyi yace toh kaka muje ko sannan ya d'auki kayan kaka ita kuwa sabreen ta d'auki nata suka tafi. Maigadi baiso rabuwansu da kakaba harma da sabreen domin mutanen kirkine suna da dad'in zama sosai. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai se wayan kamal ya fara ringing, ya d'auka tare da cewa hello abokina ya akayine, suhail yace ka d'aukosu kakan kuwa, eh na d'aukosu yanzu hakama muna dab da shiga gidane, suhail yace"thankyou dud" pls ka gaishemin da kaka, kamal yace kaka yana jinka, se kaka yace ina amsawa Allah ya dawo dakai lfy, suhail yace ameen kaka nagode, kamal yace to abokina zan kiraka anjuma, ok sena jika sannan ya katse wayar, dai dai lokacin kamal yayi hon aka bud'e gate suka shiga, tun daga wajen gidanma kasan gidan manyane bare kuma inka shiga ciki, bayan sun fitone kamal ya d'auki kayan kaka yana musu jagora har suka k'arasa da sallamarsu, mum ce da hafsat zaune suna kallon "THE GARDINERS DAUGHTER" wani series film ne mai dad'in gaske. Tun shigowarsu suka sawa sabreen ido suna ganin irin kyawunta ai atake kirjin hafsat ya buga da karfi, bayan sun zauna ne suka gaggaisa hafsat tace bro kamal kardai ince sune bak'in namu? Kamal yayi murmushi yace kwarai kuwa sis sune, wannan itace sabreen wannan kuma kakanta, shi zaici gaba daba flawer ruwa ita kuma zata dinga yin girki, mum tace Allah sarki sannu sabreen ya hakurin mahaifiyarki kuma, sabreen tace hakuri ya zama dole, mum tace to Allah ya jikanta ya jikan dukkan 'yan'uwa musulmai, gabad'aya suka amsa da ameeen. Se mummy tace toh hafsat tashi ki nunawa sabreen d'akinta ko, hafsat tayi murmushi tace taso muje, mikewa sabreen tayi tare da d'aukan akwatinta tabi bayan hafsat, shi kuwa kaka masaikin bak'i dake tsakar gidan ta gefe aka kaisa, d'akin harda AC da komai dakomai dai gwanin sha'awa. Bayan hafsat takaita d'akinne ta bud'e wall drop sannan ta karb'i akwatin sabrren ta ajiye mata a ciki ta juyo tace nan shine d'akinki, sannan ga toilet naki nan, idan akwai wani abu da kike buk'ata toki sanar dani kinji, sabreen taji dad'i sosai tace nagode hafsat. Bayan hafsat ta fitane sabreen ta k'arewa d'akin kallo tas d'an daidai ne bayi da girma sosai amma an zuba kayan duniya, kwanciya tayi tana ta tunanin yah kamal, tace oh yah kamal yau shi kad'ai a gidan bazaiji dad'iba hakama mai gadi. Bayan isha hafsat tazo ta kira sabreen wai kizo kici abinci, a baya take biye da hafsat har suka k'arasa daining, kamal na zaunne kusa da mum suna cin abinci, hafsat ta zubawa sabreen ta ajiye tare da cewa bisimillah zauna muci, sabreen tace zanje inci a d'aki, mum tace meyasa zakije d'aki bayan gamunan anan kodai kunyan d'an nawa kikeyine kamal, kamal yace kunyana kuma mum meyasa zataji kunyata kawai dai k'ila kunyanki tajeji, mum tace toh shikenan hafsat mik'a mata ta tafi d'akin tunda hakan tafiso, sabreen ta karb'a tare da cewa nagode emm kaka fa? Kamal yace kaka yana d'akinsa yanzu na kai mishi nashi abincin jekici abincin seki dawo muyi hira kinji, toh tace sannan ta wuce d'akinta taje ta zauna tana cin abincin, abincin yayi dad'i sosai dan haka taci sosai sedai bata cinyeba. Wani murya taji kamar daga sama an SABREEN, d'ago da kanta tayi tana kallon bakin kofan shigowa wannan MACEN tagani a tsaye tana kallonta tana mata murmushi, itadai sabreen sam bataji an bud'e kofaba kawai ganin mutum tayi a tsaye, ahankali MACEN take takowa inda sabreen take, ihu mai karfi sabreen ta sake tare da wurgi da plate d'in abincin hannunta tasss kakejin fad'uwan shi a k'asan tiles take ya tarwatse. Ganin yadda sabreen ta tsoratane yasa MACEN tayi saurin b'acewa segasu mum da kamal sun shigo da saurinsu, kamal dake waya da suhail yace  abokina bani 2minit zan kiraka, da gudu sabreen taje ta rungume mum tanata kuka tare da waige waigen bayanta樂
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
29-30 Mum ta d'ago da sabreen tace lfy sabreen, menene, sabreen ya rasa me zatace se tace musu mammina na gani anan mammina tana nan d'akin naganta, kamal ya matso kusa da mum yace ki kwantar da hankalinki sabreen mamminki ta rasu ai ba yadda za'ayi ki ganta anan wanda ya rasu baya dawowa kinji "may be dai kin razana ne kawai" har yanzu dai sabreen waigawa takeyi tanata k'arewa d'akin kallo. Mum tace shikenan hafsat kwashe plate da abincin can, sabreen muje daining kici abinci.
  Da sauri tabi mum suka isa daining ta zauna mum ta zuba mata abincin, kad'an sabreen taci tace ya isheta, ruwa mum ta mik'a mata yasha sannan tace nagode mum, hafsat ce ta k'araso tace mum ko zamu kwana da ita a d'akina idan ta dena tsoron seta koma d'akinta, mum tace toh hakanma yafi sabreen ku kwana tare kinji, kai sabreen ta d'ago batare datace komaiba hankalinta yana gun wannan MACEN. Wayan kamal ne ya sake yin kara ya d'auka hello abokina, suhail yace meke faruwa ne a gidan? Kamal ya gayawa suhail komai, sannan suhail yace ina sabreen d'in bata wayan, sabreen da tayi nisa cikin tunani kamal yana ta mata magana tare da mik'a mata wayan amma sam bata jinsa, hafsat dake zaune a gefentane ta tab'a kafad'arta tace sabreen tunanin me kikeyi haka akanata miki magana bakyaji, se a lokacin ta dawo hayyacinta a zabure ta kalli hafsat sannan ta karbi wayan tasa a kunne tare da cewa hello, suhail yace sabreen naji abinda ya faru amma inaso kisani shi mamaci baya dawowa k'ila dai kinsa tunaninta arankine har kike ganinta a naki tunanin yakama ki d'auki kaddara kisa a ranki cewa ta rasu ba kuma zata dawo garemuba har abada kinji? Shuru tayi tana had'iyan kukanta batace dashi komaiba, suhail yaji tayi shuru batace komaiba seya kira sunanta "sabreen are you there"? Se alokacinne tace "yeah naji kuma na gode" sannan ta mik'awa yah kamal wayan, lokacin suhail nacewa sabreen muryaeki yamin kama dana wata yarinya, karaf a kunne kamal amma seyayi kamar baiji yace hello abokina yane, suhail yayi ajiyar zuciya yace bakomai nan dai sukaci gaba da hiransu har kamal yayi musu sallama ya tafi suma suka wuce d'akunansu donyi bacci. Kamal dai tunda ya koma gida tunanine cike a zuciyarsa game da sabreen da kuma abinda yaji a bakin suhail, da kyar bacci ya d'aukesa. Shima suhail acan pakistan kasa bacci yayi yanata tunanin wannan yarinyar mai nik'af, tabbas yanzu da yayi magana da sabreen seyaji irin wannan muryance datace mishi "Thankyou so much SUHAIL" yace toh kodai kawai dan nasata a rainane shiyasa naji muryanta irin na sabreen, da wannan tunanin shima yayi bacci. Itama sabreen kasa bacci tayi dukda kashen wutan d'akin da hafsat tayi amma sam ta kasa bacci, fiskan MACENNAN dai shiyake mata yawo a kwakwalwarta, tace dama na sani dabanyi ihuba tunda dama na dad'e inaso in sake ganinta domin inyi mata godiya, insha Allah duk randa na ganta bazan sake tsorataba zanso inji metakeson gayamin sannan nima kuma inyi mata tambayoyi, ta wani gefe kuwa dad'in kalaman suhail takeji har cikin ranta tana ta murmushi tare da mamakin suhail tana zamcen zuci, yanzu shi suhail kota muryata bazai ganeniba, murmushi tayi tana tuna lokacin da suke shak'ar numfashin junansu yayinda suke kallon idanun junansu, kyakkyawar fiskarsa take gani a idanunta tare da murmushin yayi mata dad'i sosai take ji har cikin ranta tace koda wasa bazan sanar dashiba, kuma bazan tab'a bari ya ganeniba da wannan tunanin itama bacci yayi gaba da ita.
   Bayan sunyi breakfast ne taje gun kakanta sunata hira har azahar kafin ta shigo dama bata sallah. A palo suke zaune sunata hira da mum da yah kamal da kuma hafsat sabreen dai dariya kawai takeyi tana sauraron tsokanar da yah kamal yakeyiwa hafsat, har la'asar bayan sunyi sallah ne kamal yace zai fita se dare zai dawo, mai girkinsu tana gama abincin dare d'anta yazo ya d'auketa, alkhairi sosai mum ta mata harma da hafsat sannan suka tafi. Bayan isha yah kamal yayi cefene sosai ya kawo gida saboda gobene alhamis sabreen zata fara girki. Washegari ta shiga kichine ta fara girki, dama kunsani base na k'ara maimaitawaba. Kowa yaji dad'in girkin nata harma da masu gadin gidan sunata cewa ai tafi nadama iya kirki wlh, dad'i kaka yaji har cikin ransa don yadda aketa yaba girkin jirarsa. Haka tayi na rana dana dare mum farin cikine a fiskarta sosai danko gaskya girkin sabreen bakarya, sun yaba sosai harda hafsat tana cewa gaskya zaki koyamin girki sabreen, yah kamal yace da lalacinkinne zaki koyi girki? Hafsat ta b'ata rai mum kinji abinda bro kamal yake cewa ko, mum tace rabu dashi zaki bashi mamaki kuwa, sabreem tace zan koya miki hafsat karki damu. Haka sukaita ta hira har suka gama cin abinci se yah kamal ya mik'e tare da cewa mum nizan tafi seda safenmu, mum tace yau da wuri haka babu hira kenan, kamal yace mum kinsanfa gobene abokina zai dawo, dan haka bazan samu zuwa da safe bama sedai zuwa yamma. Mum tace to shikena Allah ya bamu alkhairi, kamal yace ameen sannan ya wuce gun kaka sukai sallama seya tafi, su mum kuwa sun d'an tab'a hira sannan suka wuce donyin bacci, Hafsat se murna takeyi gobe bro suhail d'inta zai dawo, ita kuwa sabreen binta kawai takeyi da kallo tana mamakin hafsat, dan sam basa wani hiran kirki da hafsat d'in, amma gashi yanzu tanata murna tana cewa sabreen zakiga d'ayan bro na gobe kinji, sabreen tayi murmushi tace to Allah ya kaimu goben Allah kuma ya dawo dashi lfy, hafsat tace ameen sannan ta kashe wuta suka kwanta kowacce da tunaninda takeyi a ranta da haka har bacci ya d'aukesu...
 
    Sad-Nas
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
31-32 Washe gari da safe safreen da hafsat suka kintsa gida tas ko ina se kamshi yakeyi, hafsat ce taje d'akin bro suhail ta wanke masa ta gyara ko ina tsab. Sabreen ta had'a musu breakfast bayan sunci ne taje gun kakanta suka d'an tab'a hira dayake bata da wani aiki se girkin kawai. Sabreen ne da mum a palo tana tambayanta Hajiya me za'a dafa, mum tace karki damu sabreen d'ana suhail babu abinda baya ci se gwaten doya da kuma duk wani juice na gargajiya da ake had'awa to baya sha, shidai a drinks coke yafi so. Sabreen tace toshikenan Hajiya yau zan koma d'akina da zama, mum tace meyasa, sabreen tace bakomai ai yanzu na dena tsoron, murmushi mum tayi tace to shikenan kiyi yadda kike so kinji, nagode Hajiya sannan ta tashi ta wuce d'akin hafsat ta kwashe kayanta tas ta mayar d'akinta sannan ta kwanta a gadonta tana jiran wannan MACEN ta sake zuwa, ganin ba wani abinda zatayine seta kira munira sunata hira abinsu, daga nan ta kira yah kamal tace kar yace ni bana kiransa. Ringing d'aya ya katse sannan ya kirata, murmushi tayi ta d'auka tare da cewa hello yah kamal ina kwana, lfy lau sabreen ya kike, lfyta lau yau bakazo kayi karin kumallo ba, eh wlh nasha tea nd bread karki damu zanzo da suhail bayan la'asar muci daddad'ar girkinki kinji, murmushi tayi tace toba damuwa se kun zo dama na kirane mu gaisa se anjuma, ok sabreen nagode sosai ki gaishemin da kaka, to zaiji insha Allah sannan ta katse wayar tayi baccinta.
  20:00pm daidai sabreen ta farka tare da duba wayanta taga time,  wuce kichine tayi da saurinta domin had'a  domin had'a abinci, peppe soup d'in kaza tayi da rice nd stew sannan ta hada cor-slow mai dad'i kuma yasha had'i, sannan ga friut salad. Da misalin 3:50pm ta gama komai seta zubawa kaka da maigadi kowa da nasa takai musu sannan ta wuce d'akinta tayi wanka tare da shafa mai tasa doguwan riga after dress batayi kwalliyaba sam se d'an turare data fesa ajikinta "WISAL" wanda yah kamal ya saya mata. Kichine taje ta d'ibi abincinta ta koma d'aki taci sannan ta mayar da plate d'in kichine ta dawo d'aki tana ta game a wayanta dan ya kaml yasa mata games masu yawa.
4:15pm motar kamal tayi hon a gate, da sairi mai gadi ya bud'e gate yana yiwa suhail maraba da dawowa sannan suka gaisa dukkansu seya k'arasa ciki. Hafsat ne ta fito d'auke da ado sosai a fiskarta tayi matukar kyau ta k'arasa gunsu da mirnarta tana cewa oyoyo bro suhail "yoir wlcum" murmushi suhail yayi yace wannan kwalliyar dukni akwai wa? Murmushi tayi tace sosai ma kuwa, kit d'insa ta karb'a a hannun ya kamal tace sannu da kokari yah kamal, yawwa hafsat, suhail yace gaskya naga wannan wankan naki yar'uwata kuma zan biya, dad'i taji sosai sannan suka wuce suna dauke da kaya a hannunsu. Mum tana mirmushi tace maraba da dawowa ya hanya, suhail yace Alhamdulillah mum kuna lfy, lfy lau sannunka da hanya, yawwa mum sannan ya wuce tare da cewa bari nad'an watsa ruwa, ok kamal yace sannan hafsat ta shiga da kayan d'akinsa.
   Bayan suhail ya fito ne ya wuce daining inda suke zaman jiransa, ya k'arasa ya zauna tare da gaishar da mum d'insa, sannan suka gaisa da hafsat yace ta zuba mishi aminci. Suna cin abinci dukkansu suna hira sega sabreen ta fito ta iso hargun daining tace ya kamal sannu da zuwa, ya suhail sannu da dawowa ya hanya? Kamal ne ya fara magana yace yawwa sannu sabreen yana mata murmushi, suhaila yace yawwa hanya Alhamdulillah ya karin hakuri kuma, sabreen tace hakuri alhamdulillah kanta na kallon hafsat, yace to allah ya jikanta, tace ameen seta kalli mum tace hajiya bari naje gun kaka, mum tace toh sabreen sekin shigo, murmushi tayi sannan ta wuce kamal da suhail sunata binta da kallo harta fita. Mum da hafsat duk sun lura da kallon da sukeyiwa sabreen ita kuwa sabreen batama san sunayiba, bayan fitantane suka maiya

0 comments:

Post a Comment