Wednesday, 7 March 2018

YAR KWALLIYA Page 1-5



Bismillahirrahmanir Rahim                              
.
Wannan kirki raren labarine nayi shi dan fada karwa da nisha dan tarwa ban yishi dan wani ko wata ba    Written by husba'ah fama                         
.
  Wata yarin yace 'yar shekara 15 kafa fururu komai babu fuska kuma tasha Jan baki da hoda harda gazal ta fallo da   gudu kanta daukeda tulo tadebo ruwa a guje ta fada gida Tana shiga ta saki tulun yafadi ya fashe   Nidai gaskiya bazan yar daba hikenan ni banda kata bus hine fa ya bini har inda zan debo ruwafa inna  yana cemin   *YAR* *KWALLIYA* kafa ba mai fuska tasha ado hine nakamahi da danbe na fasa mihi baki hine dan bahida kunya ya biyoni gida  Yasin bazan yarda ba inna kalli yanda bakina yake zubar jini inna Abu muguwace wlh  Kayi hakuri kaji kaima da naka ina ruwanka da tsokanar ta kuma kasani sarai bazata barkaba   Au abinda zaki ce kenan to shi kenan zan turo me rama min   Kayi hakuri mana kai baka jin hakurine  Ina kotsayawa beyiba yatafi  Inna ki barhi ki barhi nace kaje ka kawo bindiga karhe kenan     Yanzu Abu Wannan rayuwar kika zaba to shikenan zandena tsare miki wlh tinda ke bakida hakuri yanzu Wannan gabjejen kato kika kama da fada  Inna hinefa ya nemi tso kanata fa   Yanzu ruwan da kika debo ma gashi kin fasa tulon kaini inna ina zansa kaina  Inna Wannan fa laifin tulun kine ina ruwanhi dani nan naso na ajiye hi hine ya fadi ya fahe sai hakuri  Kamarya sai hakuri Abu girkifa zan Dora yanzu ya kikiso ayi  To ni kome ma  za ayi ayi tuludai yafahe nikuma na gaji bazan iya komawaba  
.
Kin isa komawa kamar kinyi kin gama ga wani tulun can jeki dauka kidebo wani ruwan   Kai inna kinemo wani ya debo kinga janbaki da hudana ya kare sonake na zagaya baya na siyo  I dan har baki debo ruwan nan ba ba inda zaki Abu kin jini da kyau   hikenan zan debo      Abu ta dauki tulun tatafi   Rake yauwa bari naga   maya finda ke daure a kugunta ta kwance ta Ciro Hamsin ta mika wa me rake  Yabata rake da canji tana tafe tana sha harta karasa rafi         Yauwa wana kama wato jiya kika watsa min kasa kika gudu ko yanzu wana kama cewar Abu  Ke Abu kinga diban ruwa aka turoni ba fada ba matsa na wuce cewar binta  Ke binta me kike nufi ni wasa aka turoni kenan bari kiga wasa cewar Abu      Hannu tasa ta ture tulun dake kan binta yafadi kasa yafashe  Yauwa kinga wasa nan nafasa banza ko kinada abinyi ne   Kaiiii ni kika fasawa tulu wallahi kinyi karya saina rama Abu kome kike takama dashi kin tara kin samu ni binta saina gyara miki zama  Binta na gama fada tasa kafa ta daki tulun Abu yafashe   Nanfa Abu ta daka tsalle ta dire ta kamo wuyan Binta suka kama fada da kyar aka rabasu   Aina fada miki Abu ni Binta nice dai dai ke saina gyara miki zama   Tohi kenan idan baki gyara min zamaba nizan gyara miki kuma saikin biyani tuluna kona  daka ki a gurin nan wlh   Allah ko Abu bazan biya ba kiyi abinda kika gadama koda me kika zo ni Binta na fiki  haka kikace ko to hikenan   Kallon ta Abu take tana gyada kai da buga kafa   Banga wanda ze fi karfinaba ni Abu wai saiwata banza bazara iskar damuna binta wlh kintarowa kanki aradu da ka   Hannun ta Abu ta kama ta sakar mata cizo dagudu tabar wajan   Binta tabi bayanta da gudu haka suka yanka cikin unguwa dagudu harzuwa gidansu Abu   Abu ta boye a bayan inna  Inna ki matsa Wannan fadan ba naki bane kimiko min Abu na nuna mata abinda binta zata iya ni kika ciza dai ko cewar Binta  Yar gidan marasa tsoro mekikeyi a bayana aina fada miki ni nadena bada hakuri kinga Binta gata nan zoki mata abinda kike so cewar inna  Gadan gadan Binta tataho   Kinga Binta tsaya Abu ina ruwan dana aikeki kidebo cewar inna  Inna asara kika aika dankuwa ni Binta nice nan na fasa tulun *'YAR KWALLIYA* tafasa min nawa shine nima na rama wata tsiyarce cewar Binta  Ahh babu bakomai kinyi daidai yanzudai kiyi hakuri Binta kibari idan tafito kuyita takare mutuwama tana tsoron idon ma haifi cewar inna  Inna kenan kince haka ko to ina waje ba inda zanje kekuma Abu zaki fito kisameni hoda bawanka kidinga Wanka idan zakiyi kwalliya   Binta tajuya ta fita  Inna ki matsa kibar ni da ita kina jin metake cemin   Karya tayi Abu gaskiya tafada yau kwananki nawa rabonki da kwanka  Inna batun wankan nan kibarhi aikyan kwalliya kayihi batateda wankaba gawani kamhin turare na musamman   dayake tahi a  jikina gahi turaren babu a kasuwa me yafi raina shine zan tsaya  inta batawa kaina lokaci wajan yin kwanka  Dalla rufemin baki kazamar banza kazamar hufi ina kyau Anan *HODA BA WANKA*   Baki tabude ta gir_giza kai ta dunkule hannu   inna harda ke yasin duk wanda yasake ce min hoda ba wanka na dena raga mihi yasin cewar Abu  Yanzu da kika dunkule hannu damben zakiyi dani nima cewar inna  Jifa tayi da takalmin kafarta ta debo kayan Kwalliya ta zube a gabanta tadauki Wannan tashafa ta ajiye takalli kanta a madubi tayi dariya 
.
Inna jiya da naje dan dali aka dinga tambaya waye yafesa turare nayi shiru tsabar kanhin turaren jikina hanci suka toshe Niko kayan nan ma bacanzasu zanyi ba Wanka kuwa nadena   Kaza kankida motsi afakaice suka zageki baki saniba ba abinda kikeyi sai bugawa kitemaka ki ajiye kayan kwalliya kiyi Wanka kekanki zakiji dadi  Tab tab aaah waii saidai wata Abun badai niba wanka nida hi munyi hannun Riga inna kifara sabon lissafi daga nan harranar sallah nida Wanka  Haka kikace to Allah yashigoda yayanki da malam su insun isa dake Sa saki kiyi tinda ni kin rainani dan Allah ji yanda kika cika mana gida da tsami cewar inna  Kinji ko inna kinji irin kamhin turarena ko hakama wani saurayi yajiyo kamhin yace yana sona nace bana son hi ni fako inna har bana son fita dik inda nabi ansan nice saboda turturarena cewar Abu  Waiyoo waiyoo tasa kafa tayi koli da kayan kwalliya    inna ban fada mikiba yau ake cin kasuwar gangare natafi    Tayi fice warta  Badan Allah yasa akwai sauran ruwa agidan nan ba da Abu ta gama dani cewar Inna  Tafiya take a hankali tana tafiya tana yanga acewarta tafi kowa haduwa ga turaren jikinta yafi na kowa kanshi tana tafe tana cin gyada hannun takuma rikeda sandar rake ga wuwar danmara tasha a kugunta  binda na labe tana kallon ta Abu nakara sowa inda Binta take Binta tariketa   Wana kama yasin saina dagargaza bakinki zan kyaleki yanzu ina inna take balle kibuye a bayanta cewar Binta  Yasin Binta kanki baya aiki kalli yanda kika rike min Riga a gaban mutane gasamari a gefe kalan ki zubarmin da mutunci a idonsu haba kidena abinda kuda zebiki  Karsan kuda nice mangoro kobakijiba cewar Binta   Janyota tayi zata daka bashiri ta saketa tatoshe hanci   Abu dagaskene abinda ake fada kenan Wannan warin daga ina lallai kinci sunan ki huda ba Wanka sammin raken mana   Abu taraba shi2 ta bata  Yauwa nagode gyadar fa   Tadiba tace Gahi  kibarni zaki rakani cewar Abu  Eh ni yanzu kawarkice gaskiya kinada hankali Abu   Dariya tayi tace ko nasani   suna tafe suna shirme harsuka siyo suka dawo  
.
Atare suka shiga gidan   Inna na ganinsu ta fara salati   Abu mekika kuma yiwa Binta cewar inna   Inna ai yanzu Binta tazama kawata cewar Abu  Ina baze yiyuba ban yardaba wlh dama ya kike bare ankaraki da binta waye besan bintaba cewar inna  Kinga Binta jeki gida zanzo na same ki cewar Abu  To inna sai anjima cewar Binta  Sallama Alaikum inna ina wuni  Lpy kalau Nura sannu dazuwa kaga Abu tayi sabuwar kawa mara aji irinta   Ke Abu yatoshe hanci inna meya yake bugawa haka cewar Nura  Wacce inbanda *'YAR KWALLIYA*    Fari Abu tayi da ido tareda juyawa            New writer's  Taku husba'ahfama
.
Yaya Nura a hekaima kaji kanhin tiraren nawa  Dalla kanshi ko wari kazama kawai dubi yanda gidan nan yadauki warin jikin ki  Wari karyama kenan Yasin kanhi kaji cewar Abu  Yau sai kinyi Wanka bazan iya zama dake kina wariba wlh inna bani ruwan nan na kusa dake cewar Nura  Banga abinda zesa nayi wanka ba Yasin kalan kanhin turarena ya tafi   Nura ya dauki ruwan yasa a bandaki yakai mata soso da sabulo ya karyo bulala yarike   Shiga kiyi wanka   Yaya Nura ina ganin gir manka fa cewar Abu  Yadaga bulala bashiri ta fada bandaki tayi zamanta   Kayi ka gaji yaya ba wankan da zanyi cewar Abu  Tana tawasa da ruwan kamar tana wanka tawanke fuska da kafa da hannu   Kate makeni ina fitowa zan cika fukata da KWALLIYA na raka Binta tallar gurjiya hahhh  Tabude ta fito ta harareshi tashige daki tayi KWALLIYA ta tafi  gidansu Binta taje tasamu Binta ta fito tallar gurjiya  A hanyarsu na tafiya Abu tayi ido4 dawata taci ado da KWALLIYA tayi kyau sosai harta bace Abu na kallon ta  Ke mekike kallo cewar Binta  Kinga yanda tayi kyau tafi yanta kayanta komai yayi   Nanfa Abu tashiga yin irin tafiyar  Kibar Wannan abin Abu kinsan daga ina take cewar Binta  A'a cewar Abu  Daga birni take haka suke tasu KWALLIYAR dasa kaya ba irin nakiba HODA BA WANKA
.
  Yasin yanzun nan bakinki zeyi jini Binta nizaki cewa haka nifazanyi fada da duk wanda ya kirani da Wannan sunan kowaye hi cewar Abu  Maida wukar nataba zuwa birni sau1 yanada kyau ginin su ba irin namuba kinga baze yu nabaki lbr ba saikin gani da idon ki cewar Binta  Kai nima inaso naje zaki kaini dan Allah cewar Abu  Inna inna ce matsala Abu damunje yasin cewar Binta  Kinga bawata matsala ki kaini kawai inzaki kaini ya kika ganni zanyi kyau a birni ko cewar Abu  Ehhh to ban saniba saikinje tukunna saboda gaskiya tsoro zaki basu kalle kifa tab cewar Binta  Waike hikenan bakida magana sai kice na kalli kaina me zan gani kodai ciki baki kike min ne cewar Abu  Ko daya KWALLIYAR takice abin tsoro ga kafarki Fari fat gaskiya bazan kaikiba saikin waye cewar Binta  Abinda Binta tafada yabatawa Abu rai yasa tayi gaba ta barta a baya     
.
Wani yarone yazo siyan gurjiya gun binta   Binta zuba min gurjiya   Karki zuba mai cewar Abu  Tinda na ganka nadawo mekace min jiyama   Meka ce mata Eh cewar Binta  Shiru yayi yakasa cewa komai saida ya gano yayanshi   yace ' *YAR KWALLIYA* nace  Ohh  me dadtin dankwali itace *'YAR KWALLIYA* cewar Binta  Barshi dani yanzu nanuna masa kalata Yasin harni zaka tsokana ka gudu anhi kudin nahi Binta cewar Abu  Binta ta ansa tace kuma bazan siyar maka da gurjiyan ba na karfine   Gaya mihi binta waihi Wannan dame yake dakama ne naga saiwani jijjidakai yakeyi cewar Abu  Kasa ta diba ta watsamai a ido Binta tasamai kafa ya fadi suka rufeshida duka abin mamaki kato a kasa mata na duka abinda mutane ke cewa kenan  Yayan shina kara sowa ya daka musu tsawa   Suka bar dukanshi suna Harar shi   Lpy kaikuma meya kawo ka kasan muko suwaye cewar Abu  Suwaye Ku inbanda kucakai marasa hankali dalla dubeki kafa furu furu komai be ganiba dubi kayan jikinki fuska saikace Aljana waike kinyi KWALLIYA  Ap abanza yafi na tsohuwa kaga ka gaggauta barin gurin nan inba hakaba kuma hmmm cewar Binta  Karkusake suce zaku yimin haukan da kuka saba danni bazan daukaba wlh   Ko Binta mu gwadamai aiki dan nakula saimun koya mishi hankali cewar Abu  Waige Binta tafara can ta gano dutsa tace haryanzu bakinka be mutuba ko tsaya ka gani   Dutsen ta dauko da buga mishi a kai   Banza a banza cewar Abu   Jini ya fara zuba a kanshi   Abu da Binta suka zuba a guje suka wuce gidansu Binta  Umma ga gurjiyar ki yau an hana talla inji me gari cewar Binta  Ke Binta waya fada miki cewar umma  Umma Nifa ganauce ba jiyauba Gashi can ya baza yan *DOKA* A gari cewar Abu  Kunga bana son shegan taka waca tsiyar kuma kukayi na sanku da kyau cewar umma  Wani ne ya nemi tso kanar mu hine muka fasa mai kai cewar Binta  Eh banjiba naji kamar kince fasa kai Allah na gode maka daka bani Binta nidai shikenan bakina baze zauna shiru ba saboda inada Binta cewar umma  Kofar gidan su Binta aka siga duka da karfi   Kufito mana dasu ko mushigo yara sun gagari kowa wlh yau zamu sharewa kowa hawaye kufito dasu cewar mutanan da suka zo  Kuna jiko yara kunzama dan kuka mejawa uwarsa jifa   Umma kinga jeki kiji dame suka zo idan da sulhune kusulhunta idan kuma akasin hakane kikira womu katkenan cewar Abu  Kushiga ciki bari naji dasu  
.
Wai baza a fito dasu bane Eh mumafa yan zama nine kofar suka bude suna kokarin shiga  Haba dan samari gidan matan aure ne fa   Nasani ina 'ya'yan Allah banin nan suke Binta da Abu   Basa nan sun fita   Karyama kenan ina ganin su suka shiga gidan nan dan haka ki fito dasu kawai mu baza mu hakuraba dan uwanmu suka fasawa kai gashinan sai zubar jini yakeyi yanzu haka yana Asibiti  Allah yabaku hakuri kuje idan sun dawo nida kaina zan kawo muku su cewar umma  Eh to na yarda dake saidai be kamata mu tafi haka ba bari mu bar miki sheda idan sunzo ki nuna musu      Yadaga gora ze sauke mata dagudu tabar gurin ta shige gida tarufo kofa   Yauni umma naga ikon Allah ina kuke   Umma sun bar miki sheda banzaye sokaye sun yarda ba ma nan gamunan muna jinsu kuma cewar Binta da Abu  Au kujin dadin kune a bar min sheda saboda kun amsa sunan Ku Binta da Abu ko Allah yate makeku suna nan suna jiranku kuna fita sai abinda hali ya yiwu cewar mama  Basu isaba yanzuma ba barinsu zamuyiba narike muryar su zan ne mesu 1 bayan 1 cewar Abu  Umma kawo mu kai miki dan dali cewar Binta  Gashi nan kutafi amma dan Allah karku nemi tso kanar kowa kuma Ku canza hanya karsu ganku cewar umma  To sai mun dawo suka fada gaba dayansu suka fita     
.
Suna fita umma taji wani hadeden wari  Umma taja dogon  nun fashi Wannan wani sabon yayi ne kuma Abu irin Wannan bugawa haka nida Allah yasa kar Binta tadau Wannan halin na rashin Wanka   Suna tafiya suna waka suna ciye ciye suna neman tso kana   Abu ta gano bishiya   tace Binta ajiye gorjiyar nan muhau bishiya kinga yanzu basu fara zuwaba zuwa anjima sai muje dan dali  To muje suka tarar da yara a jikin bishiya suna wasa   Kubar gurin nan Abu da Binta sunzo ko sokuke jiki yayi tsami cewar Binta  Tinkan Binta ta karasa magana yaran suka bar gurin dan sunsan halin Abu da Binta  Suka cire takalmi suka haye bishiya suna wasa kamar yara    Wasu yan mata suka zo wucewa suka gano Binta da Abu suka kwashe da dariya   Abu na ganin su ta sauko Binta ma sauko wa tayi   Wakuke wa dariya Eh daku nake magana Abu ta fada tana dungure musu kai  Karki sake dun guremin kai kinsan kowaye babana kuwa A garin nan   
.
koma waye hi beda meniba abinda yasa kika kallemu shine yanzu ze Ja miki dukan tsiyama kuwa cewar Binta  Jiki ko kayama baki iya sawaba ji hodar fukarki janbakin ma tsohon yayi ne amatse ciki asai sabo cewar Abu  Kaji wai harkurace zata ce da kare maye jiki kalli kafarki kalli fuskarki ji wani wari mara dadi da kikeyi gaskiya kinci sunan ki HODA BA WANKA   Nanfa Abu tayi kukan kura ta rufesu da duka Binta nadukan daya Abu ma na dukan 1               
.
Duka sukai musu bana wasa ba harda yaga riga     Cikin muryar kuka yarinyar tace saina nuna miki bakida wayo Saikin ga gatana   Abu tace Jeki turo duk wanda kika gadama ni Abu ina jiran hi banza qazama   Eh nice qazama idan ni kazamace ke kuma fa fada min cewar yarin yar  Bakinki be mutuba ko Abu saimun zubar mata da hakwara tukun na cewar Binta  Kuyi duk abinda kuke so lokacin kune yanzu nima lokacina nanan zuwa cewar yarin yar       
.
Tana gama fada ta mike ta debi takal manta a hannu ta kalli kawarta da suke tafe tare   Tace 'YAR  KWALLIYA suka zuba da gudu   Matsoratan banza kawai harni zakibawa tsoro da baban ki Wannan kalmarta zakiga me rama min yazama tamkar tatsoniya a gurina ni Abu naci dubu sai ceto  Sukayi dariya   Kinga dauki tallar mu karasa dandali yanzu kowa yazo zamusha kallo kai ni harnaji ma bana son zuwa cewar Abu  Binta tace meyasa   Tiraren jikina Akoda yaushe shine matsala ta dana je dandali daga kallo sai tohe hanci a gurin sama ri cewar Abu  Binta tace dagaske kike Abu warin najan hankalin samari  Abu tace bana son wula kanci binta wayace miki warine kanhidai nibama nason irin kallon da sama rin suke min nasani nafi matan dandali kyau da kanhin tirare sosai ma nice kadai nasan sirrin   Nanfa Binta ta tafi tuna ni  Ke tina ninme kikeyi  Abu gaskiya nima zan fara fashin Wanka konima turaren jikina zefito kwana nawa zanyi banyi wankaba  Abu tace yauwa yar gari kinga bake ba Wanka indai kinaso tiraren yazauna tareda ke duk inda kika higa ansan kin higo  Binta tace To hi kenan nagode kawata   Tadauko farantin gurjiya tace debi kici iya San ranki aikin bani sirri babba  Abu tace Bakomai yiwa Kaine Binta amma ya zakiyi da umman ki  idan tagane kin dena kwanka  Kibari kawai nikaina bansan abinyi ba mutafiko kinga yamma tayi kar a fara  bugawasa bama nan  Abu tace ga aiki zan saki indan mun higa dan dali ki ki zuba ido kiga abin mama ki gurin sama rida yan mata  To hikenan muje Abu               Suka je dandali hakan kuwa akayi Abu nazuwa masu toshe hanci nayi masu dariya nayi Abu harda sake tafiya      Kawata Abu gaskiya nima na rike sirrin nan hannu 2      Sukayi dariya suka tafa    Suka sha kallo sukayi tsokana iya son ransu suka koma gida  Daga ina kike   Waye Wannan Abu tace tana daga kai taga Nura   Daga dandali nake   Yariko hannunta yawuce da ita ciki ya watsar da ita kamar kayan wanki   Nura ya fara shin shine shin shine   Yace Inna bana tunaninda Abu ta shigawanka tayi   Inna tace Ko hmm zata aikata nasani Wannan nan gaba kadan nizan fara yimata Wanka da kaina 
.
Abu tace Waaa niii tab bawanda ya isa dan bakin ciki turaren nawama rabani dahi za a yi  Nura ya Wanka mata mari tafashe da kuka  Inna abinda ya dace kenan kifara yi mata da kanki tinda ita bata yi  Nifa bawanda zemin wanka Nifa yaya anyi walkiya na ganka bakin ciki kawai ka keyi dani dakaji kanhin tirarena saika dinga yamutse fuska saboda bakin ciki  Tirare ko wari kinga kidena shiga cikin mutane kina kiran waikin fesa tirare dariya zasu  miki Wannan warine warinma mara dadi qazama cewar Nura  hi kenan Inna kina jinhi ko ni ya kira qazama tafara timami akasa   Nura yace Inna kice mata ta tashi kokuma yanzu jikinta ya fada mata   Bashiri ta mike tana gunguni harya fito fili tace nagaba yayi gaba kanshi kuma nayi bawanda ya isa yakwace Ehhhe  Waye ze kwace inbanda Wanka Inna duk sanda kika tashi wankar *'YAR KWALLIYA* kitanaji kwalin sabulu saboda tsoro Inna saida safe   Yana fada yayi fice warsa   Allah yakaimu   Inna kinji shi ko Yasin yaya kajawa budur warka Allah ya hadani da ita  Kinga Abu bana son neman tsokana karki sake kitaba musu  'ya kisamu wanda yamiki badai itaba ki kwanta saida safe  To Inna Allah ya kaimu         WASHE GARI DA SAFE   Abu ta fito tana hamma      
.
Inna Allah dai yasa kin gama abinci dan yau yunwa nakwaso abaccin   Bagai suwa ba komai sai Neman abinci baza kiciba saikin goge baki kinyi sallah tukunna cewar Nura  Tamatso kusa dashi tace yaya a gidan nan kaine kwai matsalata yanda sauran suka tafi suka barini kaima zaka tafi ko ince kagaji kabarni  Yatoshe hanci tinda tafara magana harta gama   Nura yace Wai Wannan bakin naki Abu ai sai ya kashe me rai yaushe rabonki da goge baki  AF anzo wajan nikaina na manta gawayin da gihirin na ban wuya Yasin hiyasa na dena wankewa yawan goge baki na kahe hakori  Nura Yana nesa da ita yanda bazeji warin bakin ba  Injiwa Yau saikin goge baki yaushe rabonki da sallah dan Inna tace rabonda taga kin kalli gabas harta manta cewar Nura  Eh hakane yaya hadasu nakeyi hiyasa bata ganina   Hadasu kamarya Abu  Nasati1 nakeyi a rana1 sauran ranakun kuma ina hutu tafada tana dariya  Nura yace Abin ma dariya yabaki ko Abu amma kin dena zuwa isilamiya ko   Tab tsohon zance tin yauhe nadena zuwa bari kaji laifi nayi yace ze dakeni nikuma nace be isaba shine yasa yara suyimin   waka waini *HODA BA WANKA* hine na sace mai tayar keke hine fa yake ne mana ruwa a jallo
.
    Tana fada tana Sosa kai da jikin ta  Inna haka lamarin Abu ya kara lala cewa cewar Nura  Inna tace kaji da kunnan ka kakuma gani da idonka yazu kuma abin zekara finnada tinda ta hadu da Binta  Ido yazare yace Binta gagare   Ita dai yanzu kawartace sosai duk inda Abu take zakaga binta Cewar inna  Dole nakara samiki ido Abu jeki kwanke baki kiyi Alwala kizo kiyi sallah a gabana kuma ma inbanda rashin hankali irin na   Abu a i na akace miki hada sallah a keyi kowacce ana yinta akan lokacin ta kina jiko cewar nura  Abu tace Yashiga tanan ya fita tanan bayan kai ba malami bane me zaka fada min nayarda bayan sanin ma nafika  Na yarda jekiyi alwalar kizo    Taje tayi ta zo gabanshi tace yaya na hutar dakai dama yau nake hadesu guri guda barima nayi ka gani  Nura yace Ke bana son hauka fa sallar Asuba raka'a nawane  Lallaima yayan nan nawane inbanda 2  Sallama Alaikum Nura yajiyo sallama daga kofar gida girgiza kai kwai yayi yatashi yatafi  Nura ya Inna taku   Lpy kalau cewar nura  To Alhamdulillah megarine yace kuzo dakai da inna dakuma Abu  Allah daiyasa lpy cewar nura  Ehhhhhto lpy ba lpy ba saidai koma meye idan kazo fada kaji  To gamu nan zuwa yace yakoma ciki  Inna yarinyadai tasake ballo ruwa megarine yake Neman mu  To Bakomai bari ta idar da sallah saimu tafi cewar Inna  Abu tace Inna Nifa ba inda zani idan banci abinci ba Ehhhhe  Waiba sallah kike yiba Abu cewar Inna  Abu tace Inna kwantarda hankalinki na idar bani na bawa cikina tukunna    Inna ta bata ta ansa tana hannu baka hannu kwarya harta gama Tasha ruwa   Tace Inna saura kwalliya idan banyiba bazan iya sa kafata wajeba   Nura yace kin isa waye ze zauna jiranki  Inna tace kai kanka kasan hakan baze yiyuba kabarta tayi mutafi   Abuta baje kayan KWALLIYA tayi kamar yanda ta saba fukarnan kamar Aljana  Inna mutafi naga ma  Warin bakinta yadoki hancin Nura  Kaiiiiiii Abu baki wanke bakiba ko  Eh ban wankeba bakina ko naka     
.
Tayi gaba abinta sukuma suna binta a baya harsuka karasa fada kowa na gaida megari amma banda Abu  Megari yace Ke Abu me yarin yata tai miki kika daketa jiya tareda bakuwar gidana  Tawatsawa yarin yar harara tace kuma na dake ta nadaki banza ba uwar dayasa tace min HODA ba Wanka  Ke Abu baban nawa kike fadawa haka cewar yar megari  Anfada mihi ubanki ubanane cewar Abu  Kaji yarinya mara kunya me garin kike fadawa haka  Ayi hakuri yarin yace cewar Inna  Abu tace Inna saboda ni karki fara karya niba yarinya bace hekarata goma shabiyar   Inna nayimata alama tarufe baki amma ina zance kwai Abu take saki            

0 comments:

Post a Comment